← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 145

Sashe 15

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Yan uwa da abokan arzkin wanda aka sacewa 'yan uwa hankalinsu yaƙi kwanciya, gani suke babu wani yunƙuri da gwamnati take yi, dan karɓo musu yaransu, musamman masu 'ya'ya mata a ciki.
Suka dinga kira ga gwamnati, akan Lallai a biya su wannan kuɗi, a karɓo musu yaransu.
Yayin da gefe guda, gwamanti na ta ƙoƙarin ganin yadda za'a karɓo yaran, ba tare da an illata wani ba, kuma ba tare da an biya wannan kuɗi ba, idan aka kwashi wannan zunzurutun kuɗi aka bawa 'yan ta'adda hakan ƙarara ze ƙara nuna gazawar gwamnati, wanda babu gwamnatin da zata so ace ta gaza.

Taro aka gabatar cikin dare, in da aka siyo manyan makaman yaƙi, da za'a rabawa Sojoji, cikin sirri aka kawo makaman aka saye su, a in da tsirarun da aka yadda da su a harkar tsaro ne kawai suka sani.

General Ibrahim ne tare da ƙaramin ministan tsaro, suka ɗai a wani ɗaki suna tattaunawa cikin harshen turanci.

Ƙaramin minista ya kalli General Ibrahim yace "ai mu wannan abu gaba ta kaimu, ka saka amintattun yaranka su fita da wasu daga cikin kayan da na gaya maka, aka kaisu wannan mararrabar, masu shi za su zi su karɓa, kuma akwai ƙishin ƙishin tun da gwamnatin tarayya ba zata karɓo su ba, Gwamnan jihar ze rage wani abu ya basu ya karɓosu, wanda muna da kaso me tsoka a ciki".

General Ibrahim yace "an gama ranka ya daÉ—e, duk yadda kace haka za'ai, sannan akwai wasu sojoji, da aka kora suke ta ragaita a gari, cikin sirri zan janyo su cikin harkar nan, zasu bada gudunmawa sosai da sosai".

Minista yace "ni dai fatana kar a samu matsala, dan idan aka samu matsala na san yadda zan zame kaina in barka".

General yace "ba za'a samu wata matsala ba, za'a fitar da makaman a siyar musu da wasu"

"Good" suka cigaba da tattaunawa akan yadda za su yiwa harkar tsaro zagon ƙasa dan gina kawaunan su.

Yau kuwa gidan Captain Khamal, bayan Sallar isha'i suna zaune a kan carpet suna yin dinner da Pride rice with chicken ɗin da Na'ima ta yi musu, Abra dai ta ƙi ci dan har yanzu ta kasa sabawa da irin abinciccikan nan, sai fruits Captain ya bayar aka siyo mata masu yawa take shan abun ta, hakan ba ƙaramin ƙara ƙonawa Na'ima rai ya yi ba. Suna cin abincin amma hankalin Captain gaba-d'aya yana kan Abra, da ta yi motsi zai ce. "What happen Daughter? Ko, What do you want?" Ko Abincin ya ƙi maida hankali ya ci, ya lalace akan Abra. Imagining take da babu wannan shegiyar yarinyar, da tuni yanzu tana jikin Mijinta tana zuba masa shagwab'a yana tattalinta, yana ririta ta kamar ƙwai. Gashi ƙarin abun takaicin yarinyar ta ƙi yarda da ita ko kaɗan, duk irin wayon da ta yi mata amma yarinyar ta ƙi zuwa gurinta.

Bayan sun gama cin abincin da kansa ya yiwa Abra wanka ya kwantar da ita ya tofe ta da addu'a, sai da ya ga ta yi bacci sannan ya baro É—akin da take.

Sai a wannan lokacin Na'ima ta samu ya ba ta full time ɗinsa a kanta, ya nuna mata soyayya kamar yadda ya saba, tamkar babu wani abu na ɓacin rai da ya faru a tsakaninsu.

Washegari da safe Captain yana bacci Abra ta yi kashi a ƙasa a cikin toilet ɗinsa, duk da zaman da ta yi a gidan Madam Halima, amma har yanzu ba ta saba da hawa kan toilet seat ba idan za ta yi kashi. Na'ima tana ɗakinta a lokacin suna waya da mahaifiyarta tana ba ta labarin abin da ya faru, ba ta san me Abra ta aikata ba.

LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.
[9/30, 8:55 PM] Abk: *DARE DA DUHU*

_Brigh pens✍️_
Nimcyluv
Ayushercool
Zee Kumurya

P7

Domin samun complete litattafanmu, ku yi following É—in wannan accounts É—in a Arewabooks

https://arewabooks.com/book?id=6220842688e1ec3a0410329f

https://arewabooks.com/chapter?id=6316f4af434cfeb9e7fe2949

https://arewabooks.com/u/nimcyluv

Elegant online writers

LITTAFIN DARE DA DUHU, ₦300 NE KACAL, ZA KU TURA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN
0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank.
KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR DAN TURA KATIN WAYA NA NAIRA 500 TA WANNAN 09047871750
DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI, KU TUNTUƁE MU AKAN WANNAN LAMBAR 07063065780\09047871750
MUNGODE.

Cikin wani irin ɓacin rai, Na'ima ke bin Abra da kallo! Wacce ke tsugune a toilet ɗin Captain, tayi kashi a ƙasa gaba ɗaya ta ɓata toilet ɗin da jikinta.
Bata taɓa jin, akwai wani data taɓa tsana a duniya kamar ABRA KHAMAL ba, ta tsani Yarinyar tsana mai yawan gaske. Gani take shigowarta rayuwarsu gaba ɗaya matsala ce.
Wannan dalilin ke sa wa Na'ima ta ƙara jin ranta ya ɓaci akan Abra. Kishin Abra ya kama Na'ima, irin kishin nan na tsakanin Kishiya da kishiya (crazy jealousy) mussaman yadda ta ga Khamal ɗin ya na bawa Abra kulawa.

Rai ɓace, Na'ima ta ja hannun Abra zuwa Part ɗin ta, Abra na tirjewa tana ƙoƙarin ƙwala kiran sunan “Abbi” Na'ima ta hankaɗa ta zuwa cikin toilet ɗin dake nata part ɗin. Wannan shi ne dama ta Farko, Da Za tai amfani da ita wajan cin Uban Abra, ta san idan tace a part ɗin Captain Khamal Khamis zatai Punishing ɗin ta, Tabbas zata ɓata rawar ta da tsalle, wanda zai sanya Captain Khamal Khamis ya din ga yi mata kallon Munafuka mai Fuska biyu, ita kuma bata son duk wani abu da zai shafi mu'amalar ta da Khamal.

"Zaki ci Ubanki, ƴar banza mai siffa irin ta sadaka yalla!" Na'ima ta faɗa tana murɗe kunnen Abra cike da mugunta, zafin da Abra taji ya sa ta saki wata siririyar ƙara mara sauti, saboda rufe mata baki da Na'ima tayi.
A fusace kuma ta shiga zarewa Abra, kayan jikinta tare dayi mata tsirara.

Ficewa Na'ima tayi, daga cikin toilet ɗin ta nufi ƙofar part ɗin nata, cikin sauri ko lura da cikinta ba tayi, taja ƙofar ta rufe, ta sa mata key, saboda kada Khamal ya jiyo sautin kukan Abra.
Tana komawa toilet ta nemi wayar chaji, Abra na durƙushe in da ta ajiyeta, babu zato ta ji saukar bulala akan fatar gadon bayanta.

Ihu ta saki da dukkan ƙarfinta tana kiran sunan Abbi, bata taɓa tunanin akwai azaba irin wannan ba, saukar bulalar ya gigita Abra Khamal Khamis ƙwarai, har wani irin shiɗewa take na rashin sabo!.

Na'ima tace "Yadda ki ka rabani da farin ciki na, ki kai sanadiyyar shiga tsakani na da mijina, haka zaki dauwama cikin gidan nan ina gana maki azaba kala kala, wacce zata saka da ƙafarki ki fice ki bar min gida na,
Gidana nawa ne, da ga ni, sai Mijina sai kuma yaran da zan haifa masa, bana buƙatar kowa cikin rayuwarmu, zuwanki ya ruguza min dukkan wani  burina, ba zaki taɓa jin daɗi ba in dai a gidan nan ne, mufuka, Algungumin".
Tai Maganar Kamar ta na yi da sa'arta.

Yadda Na'ima ke kumfar baki zaka ɗauka da wata ƙatuwar mace, sa'arta take wannan ihun, ba da little Abra da ba ta wuce a goyata. A. Abra kasa kuka tayi sai sakin ajjiyar zuciya kawai take, bayanta yayi kwance da zanan bulala, ta kasa ko ɗaga kai ta kalli Na'ima.

Tana bala'i da kumfar baki ta wanke wa Abra kashin, tare dayi mata wanka. Na'ima ta kalli Abra kafin da ɗan ƙarfi tace "Tsinanniyyar yarinya, Allah ya isa tsakani na dake, wlh da ƙafarki zaki bar gidan nan" Abra bata san me Na'ima take faɗa ba, hakan yasa bata ma fahimta ba, wani irin tsoron Na'ima ya kama Abra, tsoran dake neman sanyata cikin mugun hali, da son raunata mata ƙaramar ƙwaƙwalwarta.

Kama gashin kanta tayi da ƙarfi, cikin tsanar Yarinyar tace "Keee!!"
Abra ko motsi ba tayi ba, sai jikinta kawai take tsuma da karkarwa na azaba.
"Kika sake, naji kin faÉ—awa Abbi wannan maganar sai na yanka ki" Na'ima ta faÉ—i maganar cikin kunnen Abra, tana nuna mata wuyanta da hannu.
“A...Abbi jani" cewar Abra wanda ilahirin jikinta rawa yake, Na'ima ta figi hannunta zuwa bedroom tana faɗin "Abbin uwarki, ko na Ubanki? Baki da Uba a gidan nan Wallahi zan tabbatar dana gurɓata wannan muguwar fuskar taki. Kura da fatar Akuya!" Abra bata fahimta, da alamar yarinyar ta gama gigita da Na'ima, a haka Na'ima ta shirya Abra cikin Pria shirt short dress. Red colour, ta ɗaure mata tulin sumar kanta da ribbon.

Yadda Na'ima taji ana knocking ƙofar ta, yasa tayi saurin Miƙewa tare da gogewa Abra Fuskarta tas, ta nemi perfume ta fesa mata, hannunta ta saka ta ɗauki Abra tana gasa mata mintsini a haka ta nufi ƙofa da ita.
Tana buɗe ƙofar taga Captain Khamal tsaye sanye cikin ƙana nan kaya masu kyau, sai ɗaukan idanu yake.

Na'ima tai murmushi, tace "Man, ina son yarinyar wallahi ta shiga raina daka jiya zuwa yau" tai maganar dan kar ya fahimci wani ab7

Ganin Khamal yasa hankalin Abra tashi, ta shiga miƙawa Abbinta hannu tana son zuwa gareshi.

"Haba Daughter, nifa Mami ce mene yasa kike gudana" Na'ima ta faɗa tana rungome Abra. Kafin ta ɗaga idanunta zuwa ga Khamal tace. "Ina jin babu daɗi, yadda Abra bata son na ɗauke ta, ba na jin daɗin ƙyuyar nan ta ta." kwantaccen Murmushi Khamal ya saki tare da saka hannunsa ya amshi Abra dake hannun Na'ima, Abra ta ƙanƙame Khamal kamar zata shige jikinsa sai ajjiyar zuciya take saki.

A nutse Captain Khamal ya kalli Na'ima yana kashe mata idanunsa yace "Bata da yarda, kin san Uba yafi gaban wasa, shiya sa tafi yarda dani akan kowa"
Chapter 15 · 0% Book details