Sashe 42
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da yamma Abra na zaune ita kaɗai a main Parlor tana duba lecture note ɗin da aka yi musu yau. Salman ya fito daga ɗakinsa cikin shigar kayan Ball. A hankali ta ɗago ta kalle shi jin ƙamshinsa, ɓata fuska ta yi tare da ɗauke kanta. Ƙarasowa ya yi ya zauna a gefenta ya ce. "Angel Sarkin karatu, ba ga bokon ba, ba ga islamiyya ba."
"Ina zaka je?" Ta tambaye shi a shagwaɓe.
Idanunsa a cikin nata ya ce. "Ball, amma bazan jima ba zan dawo."
"Ball kuma Faris? Maimakon ka zauna ka yi karatun abun da aka yi muku yau? Ko dan ka ga Abbi ba ya nan ne?"
"Idan na dawo zan yi, kar ki damu Babyn Faris da Abbi."
Turo baki ta yi ta ce. "Ni dai kar ka fita ka bar ni, ni kaÉ—ai Please."
"Ki yi haƙuri Yaya, ba zan jima ba fa." Ya ƙarashe zancen tare da kamo hannunta. Kamar za ta yi kuka ta ce. "To zan bika."
Shafa sumar kansa ya yi ya ce. "Angel rigima, gurin ball ɗin zan tafi dake? ai ta kalle ki ana tanka ki raina yana ɓaci a banza, ban yarda ba gaskiya."
"To mene abun ɓacin ran?"
"Ke ba za ki gane ba ai." Ya faɗi haka tare da miƙewa tsaye ganin lokacin fara ball ɗin har ya wuce. Kallon shi kawai take ba ta ce komai ba, ganin yanayinta ya san yana fita za ta iya yin kuka, shi kuma ba ya son hakan. Cikin rarrashi ya ce. "Mene wai? Yanzu fa zan dawo, ki yi kallo ko chat ko game kafin na dawo, zan taho miki da favourite thing ɗinki, choculates and sweets, I promised."
"Ba na so, tunda kai always sai dai ka fice ka bar ni."
Da ƙyar ya samu ya lallab'a ta, ta bar shi zai tafi, amma sai da sharaɗin ba zai wuce one hour ba, ya ce ya amince. Har bakin gare ta raka shi, sai da ta ga fitar shi sannan ta koma cikin gida.
Kasa cigaba da karatun da take ta yi, tunanika kala-kala ne suka shiga yi mata yawo a cikin kai, tunanin rayuwarta da ƙalubalen da take fuskanta daga gurin mahaifiyarta, da kuma yanda yanzu take ƙoƙarin shiga tsakaninta da Abbinta.
Knocking ɗin ƙofar parlour'n da aka yi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi. Numfashi ta sauke tare da miƙewa cikin sanyin jiki ta je ta buɗe ƙofar bayan ta tambayi waye. Gabanta ne ya yanke faɗi ganin Uncle Faisal, ba ta ƙaunar abun da zai na haɗa ta hanya da mutumin nan ko kaɗan a rayuwarta. Baya ta yi da sauri ganin irin kallon da yake bin ta da shi, cikin rawar murya ta ce. "I...ina ...kwana?"
"Lafiya ƙalau, Aunty Nai'ma fa?"
"Tana sama tana bacci, bari na kira ta."
Wani ɗan murmushi ya yi yana bin parlour'n da kallo kamar mai neman wani abu, cikin ransa kuwa faɗi yake. 'Wannan wata dama ce da ka samu Faisal, ka yi amfani da ita wajen cimma burinka na shekara da shekaru ba tare da kowa ya san kai ka aikata ba." Ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idonsa, ya tuno lokacin da ya shigo gidan yanzu bai gamu da kowa ba, dan yana ta horn mai gadi bai zo ya buɗe masa gate ba, hakan yasa ya yi parking Motar a waje ya shigo babu ita, ya yi sa'a kuma ƙaramar ƙofar gidan a buɗe take. Ya san Salman ba ya gidan yanzu, dan da yana nan dole tare zai gan su da Abra a parlour, tunda ba sa iya rabuwa idan ba lokacin bacci ba, tamkar HANTA DA JINI haka suke.
Abra ganin yanda ya yi shiru ta san ba Alkhairi yake kitsawa a cikin ransa ba, hakan yasa ta juya da sauri don guduwa ɗakinta. Ko taku biyu ba ta yi ba ya damƙi hannunta, ƙara ta saki tare da faɗin. "Please Uncle leave me, me na yi maka kake bibiya ta da wannan mummunar manufar, na roƙe ka da girman Allah ka bar ni, kai fa ƙanin mahaifiyata ne, ni tamkar ɗiyar ka ta cikinka nake."
"Na bi ki ta lallami kin ƙi yarda, dama na faɗa miki idan ba ki yarda ta daɗin rai ba, za ki yarda ko ta halin ƙaƙa. Babu abun da zai hana ni cika burin raina a yau, ko dan na rama tijarar da Babanki ya mini akan na nemi wata alfarma a gurinsa."
Fashewa ta yi da kuka tare da ƙoƙarin ƙwace hannunta tana kiran sunan Abbi da Faris, saurin toshe mata baki Faisai ya yi da hannunsa ɗaya, ta ƙarfin tsiya ya ja ta suka fice ta ƙofar kitchen wadda za ta kai ka ga ƙofar bayan gidan, Abra tana ji tana gani ya fice da ita daga gidan ta ƙofar baya ba tare da an gan su ba. Wani irin kuka take yi tamkar za ta shiɗe, don ta gama saddaƙarwa Faisal ya ci galaba, zai tafi da ita ya ɓata mata rayuwa kamar yadda ya sha furtawa.
[10/1, 2:40 PM] Abk: Ihu Abra take yi, tana turjewa amma ya dinga janta, idanunsa gaba ɗaya sun rufe, ya manta da irin abunda ka iya biyo bayan ɗanyan aikin da yake ƙoƙarin aikatawa, ba abunda makauniyar zuciyarsa ke raya masa, illa cikar muradin sa akan Abra.
Har waje ya janyota, tana tirjewa tana kuka, amma ya cigaba da janta har waje, layin shiru babu kowa. Ba zato ba tsammani sai ga wani daga cikin masu gadin gidansu Abra, wanda ya kasance soja ne ya nufosu akan babur, take Faisal ya tsaya cak yana wuri-wuri da ido.
Cikin mamaki sojan, mai suna james yace "Hey Oga lafiya kuwa?".
Faisal yace "eh lafiya ƙalau".
James yace "to ya naga kana janta, kuma tana kuka, ga jikinta ba ko mayafi".
Faisal ya haÉ—e rai yace "Eh laifi tayi mini, zan je in hukunta ta".
ÆŠan waro idanu Abra tayi, tana kallon Faisal.
James yace "koma me tayi maka, ai be kamata ka dinga janta haka ba, da Oga na gari kaima ka san ko me tayi maka, ba ka isa ka fitar da ita daga gidan nan ta ƙarfi haka ba, koma me tayi maka kayi haƙuri"
Wani irin baƙin ciki ne ya cunkushe zuciyar Faisal, na tarnaƙin da ya samu gurin cinmma mummunan burinsa akan Abra. Abra kuwa tana ganin Allah ya ƙwace ta, ta koma gida da sauri tana cigaba da kuka.
James bai kawo komai ba, saboda ganin Faisal ƙanin matar gidan ne, bai kawo wani abu na cutarwa yayi niyyar yi mata ba.
Ɗakinta ta koma ta cigaba da kuka, ta rasa wannan wace irin rayuwa ce, yanzu wa zata gayawa abunda Uncle Faisal yake yunƙurin yi mata, ai wannan ba abunda ma za ta iya faɗawa wani bane, ta yaya ma zata faɗi wannan mummunar magana haka.
Tana cikin kukan ta jiyo muryar Salman, yana ƙwala mata kira, nan da nan tai sauri ta ja bargo ta rufe idonta, dan ba ta son ya zo ya sakata gaba da tambayoyi.
Yana buɗe ƙofar ɗakin nata, ya hangota kwance ta juyawa ƙofa baya, dan haka sai yayi tunanin bacci take, dan haka ya rufe mata ƙofar ya koma ɗakinsa.
Littafin nan na kuɗi ne ₦300 NE
Via 0116886423Â Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne É—ari uku kacal.
Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750
A duk wani motsi da zai yi, tunanin Abra yake yi, lokaci-lokaci ya kan tsinci kansa da É—aukar ID card É—in ta yana kallo.
Yanzu hakama zaune yake akan gado, hannunsa riƙe da ID card ɗin nata, ya zuba masa idanu, ya tattara dukkan wata nutsuwarsa a kallon ɗan ƙaramin hoton passport ɗin ta da yake jikin ID card ɗin.
 Wata irin ajiyar zuciya yayi, ya ɗan lumshe idanunsa tare da damƙe katin sosai a hannunsa a hankali ya furta "Abra Khamal Khams" sai kuma ya ajiye shi akan gadon, ya tashi yana tafiya a hankali, zuwa banɗakin da yake cikin ɗakin.
A department É—insu, sukayi parking É—in motar, Abra ta kalli Salman tace "Faris"
"Yaya" ya amsa.
"ID card É—ina, ban ganshi ba"
"Kiyi haƙuri, za'a ganshi insha Allah, saura kije kiyi ta kuka dan bakiga ID card ba, rainaki za'ayi"
"Mhmm, to ka bani naka"
Ware ido Salman yayi yace "Namiji kika koma?"
"To kowa yana da nasa, amma ni bani da shi".
Salman yace "to waye yace ki ɓatar da naki?" Tura baki tayi tana ƙoƙarin fita daga motar.
Salman yace "ayi lectures lafiya My Angel ki kula da kanki Please,ba ruwanki da kowa kinji?"
Murmushi kawai tayi masa, ta nufi hall É—insu, duk da hijjabi ne a jikinta, da facemask a fuskarta ba'a rasa msu binta da kallo ba, saboda hatta tafiyarta cikin nutsuwa takeyi gwanin ban sha'awa.
GY BULAMA HOSPITAL AND MATERNITY.
GY Bulama ne ya haɗa gumi, yana yiwa wani matashi ɗinki, a ƙafarsa sakamakon faɗan daba, an ƙi karɓarsa a Asibitin gwamnati ance sai da 'yan sanda, shine suka taho Asibitin Bulama.
Gaba ɗaya Emergency room ɗin sai ƙarnin jini yake, dan har a lokacin jinin be fasa zuba ba , haka Bulama yayi ɗinkin nan, da taimakon Nurses.
Bayan ya kammala, ya cire safar hannunsa yace a kai mara lafiyan male ward, a biyo shi Office a karɓi takardar gwaje-gwaje da za'ayi masa.
Haka akayi, Nurse Jamila ta bishi Office, ya rubuta gwajin ya bayar yace a kai lap, suje su É—ibi jininsa ayi wannan gwajin akawo masa.
Bayan ya Sallami Nurse Jamila, wasu 'yan mata suka shigo su uku, suka samu guri ta zauna suka gaisa da Bulama.
Ya kallesu yace "'yan Makaranta ya school É—in?".
Ɗaya daga cikin su tace "Lafiya ƙalau doctor, ya aiki?".
Ya amsa da "Alhamdilillah"
Tace"Yawwa doctor, kaga Wannan ƙawayena ne, to an samu matsala ne, nace bari in rakosu Asibitinka, ɗaya 4months, ɗaya 5Months".
Bulama ya É—an kallesu yace "to ku ya akai kuka bari haka ta faru?"
ÆŠayar tace "wallahi doctor tsautsayi, bamu san kan abun bane"