Sashe 111
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bulama ya ce "Bulaguro zuwa ina kenan?".
"Wani aiki aka tura shi ƙauye, ka san jami'in tsaro ne".
"Amm, ko zaka iya gaya mini cikakken sunansa?".
"Wallahi ban sani ba, kawai dai Adnan na sani, amma ban san cikakken sunansa ba, da yake ban daÉ—e da fara yi masa gadi ba. Tun da dai matar nan ta sa ta rasu, gaba É—aya ya zama sai a hankali".
Bulama ya yi ajiyar zuciya, ya ce "Wane ƙauye aka tura shi aiki?"
"Yo ni ina zan sani?".
"Dan Allah idan ba damuwa, ka bani lambar wayarsa".
Mai gadi ya ce "Babu damuwa, bari in baka" ya bawa Bulama lambar Adnan, ya yi masa sallama ya tafi.
Ko da Adnan ya ƙarasa gidan maigari, aka yi masa iso, ya shiga suka gaisa, ya ce musu "Ni baƙo ne daga cikin garin Kano, ga takarda da aka bani na taho da ita zan yi wasu 'yan kwanaki a nan, kan in wuce".
Mai gari ya nuna farin cikinsa da jin batun Adnan, suka karɓe shi hannu bibbiyu aka ba shi masauki, a wani gida, wanda galibi a nan suke saukar baƙin su, sai dai hankalin Adnan, sam ba ya kan aikin da aka turo shi, yana kan a ina zai sake ganin yarinyar nan? Ko kuma dai kamar yadda yayi tsammani, tsabar sanya Abra a ransa ne ya sanya ya ke ganin fuskarta na yi masa gizo a fuskar mutane?.
Yayi alwala ya yi sallolin da suke kansa, bai nemi Abinci ba ya zauna ya cigaba da aikin na sa na tunani.
Wayarsa ce ta fara ringing, ya duba wayar amma ya ga baƙuwar lamba, kawai sai ya share, ya cigaba da tunaninsa.
Jin an cigaba da kiran ba ƙaƙƙautawa ne ya sanya, ya ɗau wayar zai sanya a silent, amma ya fasa ya ɗaga ya kai kunnensa tare da yin sallama.
"Wa'alaikum salam, barka da yamma".
"Yauwa wake magana?" Adnan ya faɗa cike da ƙosawa.
"Doctor G.Y Bulama ne"
Wani uban tsaki Adnan ya ja, "Me zan yi maka? Me ka kirani ka gaya mini?".
Bulama ya kwantar da muryarsa ya ce "Dan Allah ka yi ka haƙuri ka tsaya mu fahimci juna".
"Babu wata fahimta tsakani na da kai, ka jiraye ni zuwa lokacin da zan kai ka kotu, a kan kisan mata ta".
"Kana da right É—in da zaka yi haka, amma dan Allah ina son ka mini bayani yadda zan fahimta, ya aka yi yarinyar nan ta zama 'ya ta?".
"Au mamaki ma ka ke yi? Bayan har gidanka na kai maka envelope da hotunan ta a ciki da wasiƙa watannin baya? Meyasa tun a lokacin ba ka yi ƙoƙarin neman 'yar ta ka ba, sai yanzu da ka kasheta?".
"Adnan ka daina faÉ—an haka, ban kasheta ba, amma dan Allah ina son mu haÉ—u".
"Mu haɗu ka yi mini me? Da fari ka kashe mahaifiyata shekaru Ashirin da uku da suka gabata, cike da zalunci ka sayar da jinin da za a sa mata, ka yi mata gurɓatacciyar allura, wadda ta yi ajalinta, katsam Allah ya haɗani da 'yar ka wadda ita kanta ba ta sanka ba, da yake Allah ba Azzalimin sarki ba ne, sai gashi irin halin da ka ke wa mutane na wasa da rayuwarsu, ka yiwa 'yar ka har ta rasa ranta. Haƙƙin rayukan mutane ba zai barka ba, kuma daga kan matata ba zaka ƙara wasa da lafiyar wani ba" Bulama zai yi magana, Adnan ya katse wayar, ya cillar da ita gefe, ya dafe kansa yana wani irin huci tare da haɗa gumi.
Bulama ma ajiye wayar ya yi, ya dafe kansa yana tunanin, wace envelope aka kai masa? Shi ba wanda ya kai masa wata envelope.
Ta da motarsa ya yi, ya ja ta a guje, ya nufi gida, yana parking ya fito, ya nufi wurin maigadi a sukwane.
Ganin da mai gadi yayi Bulama ya nufo shi, ya sanya ya taso da sauri ya taho, tare da risinawa a gaban Bulama.
Bulama ya kalleshi ya ce "Kwanakin baya, ko ma in ce watannin baya, an kawo wata envelope an ce a ajiye mini?".
Mai gadi ya yi shiru, can ya ce "Tabbas Yallaɓai an yi haka, an kawo saƙo an ce a ajiye maka watannin baya".
"Ina takaddar?".
"Yallaɓai ban duba ba, ban san ko takadda ce a ciki ba, na kaiwa Hajiya ta karɓa ta ce zata ajiye maka".
Jinjina kai ya yi ya tafi da sauri, Hajiya Saudat na É—akinta, tana kwalliya a gaban mudubi, Bulama ya faÉ—a É—akin ba bu ko sallama.
"Doctor lafiya kuwa?".
"Watannin baya an kawo saƙo a envelope, an bawa maigadi, shi kuma ya ce mini ya baki ki ajiye mini, ina saƙon?".
"Wane saƙo kuma? Ni ba wani saƙo da ya bani".
"Kar ki mini wasa da hankali, envelope aka kawo mini, da takadda a ciki da hotuna suna ina?".
Gabanta ya yi mummunar faÉ—uwa, amma ta dake ta ce "Ni babu wata envelope da aka kawo mini, ka dai tambaye shi wanda ya bawa".
"Shut up Saudat, Mutumin nan ba zai miki ƙarya ba, ki bani saƙon nan".
"An ya ba ciwon damuwa ne ya kama ka ba, ya ke neman ya taɓa maka ƙwaƙwalwa ba?".
"Ni ki ke gayawa ƙwaƙwalwata ta taɓu? Kin kyauta amma na fara tunanin wani abu, akwai abin da nake tunani, idan har ya tabbata zaki ga abin da ba ki tsammani ba".
Ya juya fuuuu, ya tarar da Meenal a ƙofa a tsaye, jin hayaniya ya sanya ta fito, bai ko kalleta ba ya wuce yana huci.
Meenal ta ƙarasa shiga ɗakin ta kalli Mummy ta ce "Mummy me ke faruwa ne? Wace takadda da hotuna Daddy ya ke magana a kai?".
"Ke kar ki dameni dan Allah, koma É—akinki"
Ƙurawa Mummy Ido ta yi, ta ga gaba ɗaya gumi ya rufeta, alamun tsoro da rashin gaskiya suka bayyana ƙarara a fuskarta.
"Mummy dan Allah ki gaya mini".
"Get out from my sight, ki koma É—akin ki na ce" ba shiri Meenal ta bar wurin, tana tunanin meke faruwa haka?
Sintiri Hajiya Sauda ta shiga yi a ɗakin, tana jinjina kai tamkar ƙadangaruwa. "Kafin ka binciko komai, zan sake bunneka doctor, ba bu abin da zaka iya ganowa!' ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya.
Hajiya Mama ta kira Adnan a waya, ta ji ko ya sauka lafiya, suka taɓa hira, har ta tura masa hotunan Aishatul Humaira ta waya, kamar yadda Mami kan tura mata.
Adnan ya ƙura mata izanu, ji yayi zuciyarsa na son ganin Aishatul Humaira, rabon da ya ganta tun tana kwalba, tun da aka tafi da ita bai sake zuwa ya ganta ba, wata irin soyayyar yarinyar ta mamaye zuciyarsa, musamman yadda kammaninta suka juue zuwa na Abra sak, wanda kyakykyawan hanci Bulama irinsa ne ɗoɗar a fuskar Aishatul Humaira.
Nan ya barwa zuciyarsa cewar zai je Kano ya ga Little Abra.
Kwanansa biyu a garin, ya je ofishin 'yan sanda na yankin, ya ga DPO, domin fara gabatar da aikin da ya kawo shi, daga nan kuma ya tafi Kano.
Ba ƙaramin mamaki Mami ta yi ba da ganin Adnan, sam bai sanar da zuwansa ba, ita abin har mamaki yake bata, yadda ko ta waya baya neman ya 'yar ta sa take ciki, sai dai ta yi masa uzuri, kasancewar tun da Abra ta rasu, yake kwance ba lafiya, dan a yanzu ma ya rame da yawa, ya ƙara duhu sai idanu.
Mami ta yi masa kyakywar tarba, tare da yi masa ya jiki.
"Jiki da sauƙi Mami, ya Mamana?".
Mami ta ce "Ai na É—auka ka bar mini ita gaba É—aya ne, baka sonta?"
Adnan ya sunkuyar da kai ya ce "Mami ya za ayi in ce bana sonta, ina gujewa abin da zai sa in dinga tuna Abra ne kawai, yanzu haka ina cikin wani ƙauye a katsina, na tafi aiki, Mama ce ta turo mini hoton ta,naji lallai ina son in zo in ganta".
Mami ta ce "Allah sarki, ai sai haƙuri mu cigaba da yi mata addu'a,bari in ɗauko maka ita".
Ta shiga ɗaki ta ɗauko masa Little Abra, wadda ta ke ta bacci, ya ƙura mata idanu kamar zai cinyeta, tayi girma yanzu kamar ba wadda aka ciro a kwalba ba.
Ya ɗagata yana cigaba da kallonta, amma sai lanƙwashe wuyanta ta ke tana tura baki, alamar bacci bai isheta ba.
"Like Mother like daughter" ya furta yana tuna Abra, tuni idanunsa suka cika da hawaye.
Mami ta ce "Ayi haƙuri dai, Ai mata Addu'a".
Adnan ya jinjina kai sannan ya ce "Abbi ba ya gari ne?".
Mami ta ɗan kwaɓe baki ta ce "Eh".
"To, ga siyayya can na mata, kuma ina ganin tun da ta ƙara girma, ai mata hakika".
Mami ta ce "Tun yaushe aka yi mata hakika, ai kana wannan rashin lafiyar aka mata komai, taron suna ne da bai yiwu ba, tunda ga abin da Allah ya saukar"
Adnan ya ce "Haka ne, Allah Ya rayata ya jiƙan mamanta".
Mami ta amsa da Ameen.
Adnan ya kwaso uban kayan da ya sayowa Aishatul Humaira.
Mami ta ce "Da ka yi shawara da ni ba zaka sayo wannan kayan ba, ta na da kaya da duk wani abun buƙata, da ga can ɓangaren ku sun kawo, nan ma duk an mata komai, madara kawai tana da gwangwani kusan Ashirin, diapers da komai duk akwai".
"Lallai wannan 'ya 'yar gata ce, bakoma Mami ai alhakina ne nima na yi mata".
Sai bayan azahar sannan Adnan ya yi haramar tafiya, kamar kar ya tafi, ji yake kamar ya ce a bashi 'yar sa ya tafi da ita.
Ba yadda ya iya haka ya yi sallama, ya tafi, sai dai ko da ya wuce ta ƙofar sitting room ɗin da yake zama su yi hira da Abra, sai da gabansa ya faɗi, ya tuna yadda ta dinga nuna masa soyayya a wannan lokacin.
Jiki a sanyaye haka ya baro gidan su Abra.
Bai isa katsina ba sai dare, tun a hanya ya sai 'yan kayan da zai buƙata, da abin da zai ci ya kwana a wani Hotel, dan ba zai iya shiga wannan ƙauyen da daddare ba.