← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 145

Sashe 44

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace "Nima ban sani ba, abunda zanje inji kenan, ya akai suka ci gubar suka mutu, ba tare da an samu wani cikakken bayani a bakinsu ba".

"Kai amma ban so ba, daga dawowarka jiya ko gama ganinka ba muyi ba zaka juya?".

Ya ɗago ya kalleta yace "Am sorry, nima ba hakan na so ba, amma kuyi haƙuri ya zama dole in tafi, lamarin akwai alamar tambaya".

Tace "Shikenan, Allah ya tsare bari in ƙarasa haɗa maka kayan".

Ta cigaba da haÉ—a masa kayan, shi kuma ya shiga wanka.

Successfully, GY BULAMA ya cirewa 'yan matan nan ciki, bayan tafe masa uwar kuÉ—insa da suka yi, ya rubuta musu magunguna tare da kafa musu dokokin da za su bi, dan gudun kar Matsala ta biyo baya.
Suna tafe a mota, Baby na driving tana cigaba da shirya musu yadda zasu damfari Alhazan dake mu'amala da su kuÉ—i, Mussaman wanda yai mu'amala da Ihsan, wanda ya kasance babba ne sosai.
Tace zasu koma gidan da suke su huta, idan suka warware zasu tafi Abuja, aje ayi wadda za'ayi dan su zasu biya kuÉ—in cire cikin da aka yi.

Yauma a gajiye Abra suka koma gida, duk ta gaji jikinta har wani ciwo yake, Wanka kawai tayi, tai sallar la'asar,ta hau gadonta dan ta É—an huta, ta lumshe idanunta sai dai gabanta ya faÉ—i, a lokacin da tuno da mutumin da ya tsinci ID card É—inta, Mutumin da ko sunansa ba ta sani ba.
Guntun tsaki ta ja, tare da ƙoƙarin gyara kwanciyarta, amma wayarta tai wata 'yar ƙara, alamar saƙo ya shigo.
Ta miƙa hannu ta ɗau wayar, ta fara duba saƙon.

*Sky is beautiful, especially when the millions of Stars appears in the dark, but is not that beautiful if the Moon doesn't appear. You are always that Moon that make the Sky beautiful, Stay bless my Angel.

Murmushi Abra tayi tare da furta "Allah ya shiryeka Faris"

Ta gama hutawarta, ta tashi ta shiga kitchen, a Wannan karon akai sa'a Mami tayi girki, ta shiga kitchen ta zuba ta fito falo, dan taci.

Hakan yayi daidai da fitowar Salman falon shima, yana ganin Abra yace "Alhamdilillah, thank God dama nima banci Abincin ba, let's eat together".

Ya ƙarasa kitchen, ya ɗakko spoon ya dawo ya zauna a inda Abra take, yasa cokali suka fara cin Abinci.

Abra tace "Wai nikam ina Abbi? Naga motarsa a gida, kuma banga alamar yana nan ba".

Salman yace "Mami tace mini aikin gaggawa ne ya kama shi, ya koma É—azu muna school".

Abra tace "Amma be bari mun dawo ba, ban gama ganinsa ba fa".

"To ga hanya nan, maza bi shi" Salman yayi Maganar yana saka lomar Abinci a bakinsa.

Mami ce ta fito daga sashinsa, cikin faÉ—a tace "Salman meye haka? Wai ba hanaka wannan abun ba, ka zauna kuna cin abinci tare, kai kaga dacewar hakan? Ko da duk ka nunamin ban isa bane?".

Salman yace "Mami, Yaya ce fa ba wata ba, banga aibun haka ba".

"Ai dama ba zaka gani ba, tashi ka bar gurin nan kafin in ɓata maka rai".

Kan Salman ya yunƙura, Abra ta miƙe, ta bar masa Abincin, ta koma ɗakinta rai a ɓace.

Wayarta na hannunta, taji tayi vibrating.

I want you in my life for today, tomorrow and forever, have a cool evening my Moon.

Ɗan shiru Abra tayi, Salman dai gashi can a Falo Mami na yi masa faɗa, to waye ya turo mata wannan saƙon? Sai yanzu ta duba labar taga baƙuwar lamba ce.

Ɗan taɓe baki tayi, tana tunanin kawai mistake ake gurin turo mata saƙon.

Kafin lokacin da zata kwanta bacci, aƙalla an tura mata messages kusan biyar.

Haushine ya fara kamar Abra, ta replying da wrong number.

  Daga haka ba  a kuma turo mata message ɗin ba, kan ta kwanta bacci sai da ta kira Abbi, sukayi hira, ta yi masa Adduoi da fatan Alkhairi.

Haka nan ta samu kanta da jujjuya messages ɗin da aka dinga turo mata yau, sai ta samu kanta da tunanin ko yaya masu soyayya suke ji oho, ita dai Allah be sa ta taɓa yin saurayi ba, balle taji me ake ji.
'to ke meye naki na soyayya, ke da kike karatu, ki maida hankali akan karatun ki, ko dan ganin Farincikin iyayenki' wata zuciyar ta gargaÉ—eta.

Ta ture tunanin komai, ta cigaba da karatun ta, ƙarfe ɗaya ta tashi, tayi alwala tayi sallar nafila, sannan ta nemi guri ta kwanta bacci.

Da Asuba ƙarar shigowar saƙo ne, ya farkar da ita, ta ɗau wayar ta sake dubawa.

"I pray Allah Khair for you now and always, include me in your prayers dear, you will always be in mine, have a wonderful Morning, i will be in your department to".

"Ikon Allah" shine abunda ta faÉ—a, ta ajiye wayar.

Abu kamar wasa kusan kwanaki uku, Ana turowa Abra ire-iren wannan saƙonnin, ba tare da ta san waye ake turo mata ba, da fari abun haushi yake bata, daga bisani kuma har Alla-Alla take, me turo saƙon ya turo, sai dai be taɓa kiranta ba.

Tayi saving É—in lambar a wayarta da Mr. Unknown.
Ko da ta duba what's app É—inta, labar ta bayyana a contact É—inta, amma dp É—in lambar babu hoto.
Ji tayi tana son yiwa lambar magana amma kasa, kuma gashi tunda ake turo mata saƙon, tunda tayi reply da wrong number, ba ta sake replying ba.

A wannan karon sai taji tana son yun replying, a message É—in da aka turo mata, wanda yake cike da Adduoi da kuma koÉ—a ta.

Tayi Replying da "Ameen, Nagode sosai, amma da Allah ko zan iya sanin waye?".

Tun safe da tura message É—in be mata reply ba, haka ana lectures amma hankalinta na kan wayarta, tana jiran ayi mata reply.

Sai bayan da ta koma gida, sannan akayi reply "Is someone, who want a chance to be with you for ever".

"May i know you please?" Ta kuma tanbayarsa.

"Sai kin sanni sanni sannan zaki so ni? Bana iya komai a rana idan har ban ganki ba".

Sai da ta É—an ware idonta, sannan tace "A ina kake gani na, bayan bana zuwa ko ina sai Makaranta".

"Zan ajiye miki saƙo a what's app, wanda zai tabattar miki da hakan, aini bana ƙarya sai bisa kuskure".

Cikin hanzari ta shiga what's app ɗinta, aikuwa saiga saƙo a what's app ɗin, hotonta ya turo mata, tana tsaye a ƙofar ajinsu, saye da doguwar rigar abaya, wanda sam ba ta san an ɗau hoton ba".

Mamakine ya sake kamata tace "A makarantar mu kake kenan?".

"Neither No, Nor Yes"

Kamar tana gabansa ta tura baki ta tura masa "Please tell me".

"Me kike so in gaya miki?"

Abra ta tura masa da "Ka gaya mini idan a makarantar mu kake, sannan ka turomin hotonka"

"Idan na turo miki hotona na san ba zaki yadda ki soni ba"

"Meyasa?"

"Saboda ni mummuna ne, muni me ban tsoro, ke kuma kyakykyawa ce Masha Allah, kyawu mai É—aukar hankali".

Abunka da farin shiga, Abra ta ture litattafanta gefe, ta gyara zama tana cigaba da hira da wanda ba ta san kowanene ba.

"Ni koma a ya kake, dan Allah ka turomini hotonka in gani".

"Gaskiya ina tsoron bayyana miki kaina, kar Major ya sa sojoji su zane ni, bani da ƙwari zasu iya yi mini illa".

Tayi reply da "Eyya, ai ba haka Abbi na yake ba, ba abunda zai sa ayi maka, ko hotonka ka nuna mini".

"Ba zan turo miki hotona ba, amma zaki ganni very soon insha Allah, ina Faris?"

Saida t buÉ—e baki da mamaki tace "Ya akayi ka san Faris, ko a Makaranta ba kowa ya san ina gaya masa wannan sunan ba".

"Yanzu idan nace miki da Faris kike magana me zaki ce?"

"Kaiiii Faris kuma, i dont think Faris will prank me with this".

"Are you sure my Angel?"

Gaba É—aya Abra ta rikice, banda Abbi da Salman, ba wanda yake kiranta da Angel.

Da sauri ta ajiye wayar, ta fita falo, aikuwa ta tarar da Salman a kwance a ka kujera, yana danna wayarsa.

Da sauri ta ƙarasa, ba tare da tayi masa magana ba, ta miƙ hannu zata ƙwace wayarsa, caraf ya riƙe hannun, ya kalleta yace "Ya dai?"

"I want see your phone" ta faÉ—a tana tsare shi da ido.

"For what?"

Abra tace "I just want to see it".

Salman yace "aikuwa ba zaki gani ba".

"Please Faris, ka bani in gani".

"Me zaki yi da ita?".

"Kai dai kawai ka bani".

Miƙewa Salman yayi yace "tun da ba zaki faɗa mini me zaki da ita ba, na hanaki".

Diddira ƙafarta ta shiga yi, cikin shagwaɓa tana cewa "dan Allah Faris ka bani in gani"

Dariya yake yi yace "sai kin gaya mini me zaki da ita".

Shagwaɓa take sosai, wanda hakan ba ƙaramin burge Salman yake ba, ganin za ta yi masa kuka, ya sanya ya miƙa mata wayar ta sa.

Sai dai duk wani bincike da tayi, ba ta ga wani abu makamancin saƙonnin da ake tura mata ba a wayar ta Salman.

Littafin nan na kuɗi ne ₦300 NE
Via 0116886423  Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne ɗari uku kacal.

Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750.
[10/1, 2:40 PM] Abk: Ƙara rikicewa Abra tayi, ganin yadda ya tayara da motarsa ya bar gurin. Gaba ɗaya ta rasa abunda yakamata tayi a gurin nan, ihu za tayi ko kuka za tayi? Bata koma gurin cin Abincin nan ba, ta nufi department ɗin su, tana zuwa ta tarar da Salman da waya a hannunsa yana lelleƙawa  yaga ta in da zai hango Abra.
Yana waiwayowa ya sukai ido huÉ—u da Abra da take ta tsuma.

Da sauri ya ƙaraso in da take yana faɗin "Wai ina kika shiga ne? Over 15 missed calls, amma baki ɗaga ko ɗaya ba.
Shiru tayi tana rarrraba ido, ta kasa ce masa uffan.

A É—an hasale yace "ki yi mini magana ma, kin tsaya kina kallona".

"Wani lecturer ne ya ƙwace mini waya"

"Me ki kayi masa da ze ƙwace miki waya?".
Chapter 44 · 0% Book details