← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 145

Sashe 57

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Numfashi ta sauke ta ce. "Lafiya ƙalau Mami." Taɓa baki Mami ta yi ta ce. "Idan ma akan maganar Aurenki ne ki kwantar da hankalinki tamkar an yi an gama, abun da nake so dake kawai idan Abbinku ya tambaye ki kina son Auren ki ce masa eh, shi ne kawai solution. Gyaɗa mata kai Abra ta yi cikin kunya, mamakin abun take, wai ita ce yau ake maganar za a yi Auranta, abun da ba ta taɓa tunanin yin shi nan kusa ba.

"Yawwa Æ´ar Albarka, fatanmu kawai Allah ya kai mu lokacin mu sha biki." Na'ima ta faÉ—a cikin murmurshi tare da dafa kafaÉ—arta.

Rufe fuskarta ta yi da hannunta tana murmurshin ita ma. Yau kam ta gasgata maganar Salman da yake ce mata Mami tana son ta, for the first time in her life ta goyi bayan abun da take so, kuma har ta zauna tana yi mata magana cikin kulawa da fara'a, hakan ba ƙaramin farinciki da jin daɗi ya haifar mata ba. Kwantar da kanta ta yi akan kafaɗar Mami, wata muguwar harara Na'ima ta gallawa kan Abra, a ranta tana jin tamkar ta shaƙe ta har lahira, amma a fili sai ta shiga shafa kanta.

"Mami yau Salman ya fito kuwa?"

"Wai mene damuwarki ne akan hakan? Tun da kika tashi sai tambaya ta Salman kike, yaro ne shi ko jariri da za a saka masa ido irin haka?"

"Mami may be fa ba shi da lafiya ne." Ta yi maganar kamar za ta yi kuka.

"Lafiyar kenan, don lafiya ita take sa a ji shiru, da wani abu yana damun shi ai da tuni mun sani." Na'ima ta faɗi haka tare da zame kan Abra daga jikinta ta miƙe ta fice.

Bin ta da kallo Abra ta yi, zuciyarta cike da mamakin Mami, yanda Mami take nuna over caring akan Salman da damuwar shi amma yau ta ga kamar ko a jikinta da rashin fitowar tasa, don ɗazu ma a da za su yi breakfast ta ce za ta kira Salman ganin bai fito ba hana ta Mamin ta yi ta ce ta ƙyale shi, cikinsa ne ai ba na wani ba.

Tashi ta yi da sauri ta gyara hular kanta ta fice zuwa É—akin Salman.

Yana zaune akan bedside drawer hannayensa duka a cikin sumar kansa yana yamutsawa Abra ta yi knocking Kofar ɗakinsa. Ko ba a faɗa masa ba ya san ita ce, kamar ya share ta kamar yadda ya yi mata ɗazu amma sai ya kasa, numfashi ya sauke tare miƙewa ya je ya buɗe ƙofar.

"Bloody what happened to you?" Abra ta faÉ—a kamar za ta yi kuka.

Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi tare da lumshe idonsa, kaso mafi yawa na damuwa da ɓacin ran da yake ciki ya fara gushewa, sakamakon tozali da kyakkyawar fuskar Angel ɗinsa gami da shaƙar sassanyan daddaɗan ƙamshinta. Juyawa ya yi ya koma ya zauna a bakin gado ba tare da ya ba ta amsa ba.

Ƙara tashi hankalin Abra ya yi ganin yanayinsa kamar yana cikin damuwa, bin bayansa ta yi da sauri ta dafa kafaɗunsa idanunta cike da ƙwalla ta ce. "Faris please talk to me, me ya sa jiya ba ka fito ba? Ko dinner ba ka yi ba, yau ma ba ka yi breakfast ba."

Ganin tana shirin fashewa da kuka ya kama hannunta ya zaunar da ita a gefensa, idanunsa cikin nata ya ce. "Ke ce Angel, kin hana zuciyata sukuni, jiya ko bacci ban iya yi ba." Ya yi maganar cikin tsantsar damuwa.

"Innalillahi! Ni kuma Faris? Me na yi maka?"

Shiru ya yi bai ce komai ba sai hannunta da yake murzawa a hankali tare da sauke ƙananun ajiyar zuciya, bai san ya yi missing ɗinta over ba sai da ya gan ta yanzu a kusa da shi, ba ƙaramin daure zuciyarsa ya yi ba na hana kansa ganin ta ba a jiya, ya kwana cikin ɓacin rai da takaicinta ita da Mami.

"My Faris ka faɗa mini abun da na yi maka mana, tun kafin ka faɗa mun na yi maka alƙawarin ba zan kuma ba, I'm sorry please, ka san bana son ganin ka a irin wannan yanayin na damuna ko?"

"Abra! ashe zaki iya yin Saurayi har ya zo gidan nan ba tare da na sani ba? Ashe akwai abun da zaki iya ɓoye mini a rayuwarki?"

Ƙasa ta yi da kanta cikin rashin ganin kyautawarta, amma ita ta yi hakan ne saboda gudun ɓacin ransa, ashe ta yi gudun gara ne ta tadda zago, kuma ba ta yi tunanin zai sani ba, yanzun ma ta san Mami ce ta faɗa masa.

"I'm sorry Bloody." Ta faÉ—a cikin raunin murya.

"Hmm, kin san ba zan iya dogon fushi dake ba ne shi ya sa kike mini abun da kika so, babu komai."

"Haba Salman, don Allah kar ka ce haka, kai ma ka san ba haka ba ne."

"Ya ya ne?"

"Bana son ɓacin ranka ne, kai ma ka sani."

Kama haɓarta ya yi ya saka idanunsa a cikin nata dake cike da hawaye, cikin raunin murya ya fara magana. "Angel dama za ki iya tafiya ki bar ni? Dama akwai ranar da za ki bi wani alhalin gani? Please My Baby ki tausayawa ɗan ƙaninki, kar ki bar ni Pleaseee!" Ya ƙarashe maganar da jan harafin ƙarshe cikin wata irin siga.

Lumshe idonta ta yi ba tare da ta shirya hakan ba, ko kaɗan ba ta ɗauki kalaman Salman da wata manufar ba, ta ɗauke su matsayin tsananin shaƙuwar dake tsakinsu ce ta saka ba ya son su rabu. Ba tare da ta buɗe idonta ba ta ce. "Ni ma bana son na yi nesa da kai My Faris, amma ka san ai aure dole ne, watarana dole na y......"

"Na sani Angel, za ki yi aure, amma ba da wani ba." Ya katse ta da faÉ—in hakan cikin kaushin murya.

BuÉ—e idonta ta yi tare da waro su waje ta ce. "To da wa zan yi?"

"Da mijinki, wanda yake ƙaunarki fiye da kowa a duniyar nan, wanda ya yi shekaru yana dakon son ki a cikin zuciyarsa."

Murmushi ta yi tare da cire hannunsa daga kan fuskarta ta ce. "To ai shi ne wanda...."

"Ba shi ba ne."

Ɓata fuska ta yi ta ce. "Ta yaya ka sani? Ni ma fa ina son shi." Runtse idonsa ya yi da sauri yana jin tamkar ta soka masa mashi a cikin zuciyarsa, cikin wata irin murya ya ce. "Please Angel kar ki ƙara faɗar haka a gabana."

"Why?"

"Kawai."

"Shikenan, ni mu bar wannan zancen, ka taso mu je ka ci abinci, jiya da ƙyar na iya bacci saboda rashin sanin halin da kake ciki."

"I'm Okay." Ya faÉ—a a tak'aice.

"Kana son ka gan ni a cikin damuwa ne Faris? Ba ka san yanda nake ji ba idan na gan ka haka, Please ka taso mu je ka ci abinci." Ta yi maganar kamar za ta yi kuka.

Ganin yanda ta nuna damuwarta a kansa sai ya ji wani sanyi a ransa, cikin shagwaɓa ya ce. "Sai dai in zaki ba ni a baki." Da sauri ta ce. "To zan baka, ni dai burina ka ci abincin." Bai ce komai ba sai hannunta da ya kama ya ɗora akan ƙirjinsa, saitin zuciyarsa, yana bin ta da wani irin kallo mai kashe jiki ya ce. "Ji yanda zuciyata take bugawa saboda ke Angel." Murmushi ta yi cikin wautar rashin sanin abun da yake nufi ta yi sama da hannunta ta shafi kuncinsa ta ce. "Ka daina damuwa bloody, ba abun da zai raba ni da kai."

"Sure?"

Gyaɗa masa kai ta yi tare da jan karan hancinsa da ɗan ƙarfi. Ɓata fuska ya yi ya ce. "Kin takura wa hancina Angel, ko dan kin ga ya fi naki kyau ne?"

"No, daɗin ja ne da shi kawai." Ta yi maganar tare da ƙara jan hancin nasa. Murmushi suka yi a tare cikin tsananin shauƙin junansu da suke ji a cikin ransu, daidai lokacin Mami ta turo ƙofar ɗakin da ƙarfi.

Cikin ɓacin rai take duban su ɗaya baya ɗaya, tsayar da idanunta ta yi akan Abra cikin haɗe rai ta ce. "Me kike anan? Wai ku ba za ku taɓa girma ba ne? Goɗai-goɗai dake kin wani taho ɗakin ƙaninki, wanne irin shashanci ne wannan?" Sunkuyar da kai Abra ta yi tare da faɗin. "Ki yi haƙuri Mami."

"Dalla ni ta so ki wuce, tun É—azu Abbi na neman ki, na je É—akinki ba kya nan, na jira ko kina toilet amma shiru, dama na san babu inda za ki yi sai nan."

Jiki a saɓule ta miƙe ta fice cikin mamakin yanda Mami ta koma mata sak ta da, kamar ba ita ce ta gama yi mata magana cikin kulawa da ƙauna ba ɗazu.

"Wato ko gaishe ni ban isa ka yi ba ko Salman?"

"Zan gaishe ki mana Mami, na ga kina magana ne shi ya sa, ina kwana?"

"Ban sani ba, ka riƙe gaisuwarka bana so, mara kunya kawai, har ka yi girman da za ka dinga irin wannan abubuwan ko? Yaushe na haife ka? Yaushe na gama goya ka a bayana?"

"I'm sorry."

"Sorry for your self." Ta ƙarashe zancen tare da jan tsaki sannan ta juya ta fita.

Bin bayanta da kallo Salman ya yi, cikin ransa yana faÉ—in, duk rintsi ba zai rabu da Abra ba, ba gudu ba ja da baya a soyayyar ta."

A parlour Mami ta tarar da Abra a zaune.

"Mami ina Abbin ban gan shi ba?"

"Ya fita zai amso saƙo, tun ɗazu yana ta jiran ki har aka kira shi ya fita." Na'ima ta faɗa ba yabo ba fallasa.

GyaÉ—a kai kawai ta yi zuciyarta cike da fargaba, tsoron gamuwa da Abbi take tunda ta Na'ima ta ce ta faÉ—a masa maganar Adnan, addu'ar ta É—aya Allah ya sa ya amince. Fahimtar hakan ya sa Na'ima ta fara kwantar mata da hankali, tare da jadda mata ta kafe akan ra'ayinta ko me Khamal zai ce mata.
Chapter 57 · 0% Book details