← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 145

Sashe 31

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin Salman ya gama tantance abunda Mami ke faÉ—a masa, ya ji saukar muryarta cikin tashin hankali tana faÉ—in.
"You are my son, not Abra. Abra karuwa ce ta Haifawa Ubanka, ya zo ya ke ci mana amana, Salman, believe me ya fifita son da ya ke maka akan Abra, yarinyar da babu wanda yasan asalin wacce Shegiyar karuwar ce uwarta, Khamal ya raina min hankali Your father hurt us, deceived us"

Ta ƙare maganar tana sakin kuka da ƙarfi, ita kanta bata san lokacin da maganganun suke fitowa da ga cikin bakinta ba, wani irin zafi Zuciyarta ke yi mata, wanda ya sanya ta kasa controlling kanta, har ta kai ta dayin Revealing secrets tonan asirin shekara da shekaru.

Salman zama ya yi kamar wani gunki, ya kasa tantance abunda Mami ke faÉ—a masa, his thoughts stopped.
Komai nasa ya tsaya, ya kasa yadda ko fahimtar abunda ta ke faÉ—a akan Abra, shi tsoran Mahaifiyar tasu ne ma ya fara kamashi, ta ya ya zaka haifi É—a a cikin ka kace wai karuwa ce ta haifa? This is impossible.

Juyawa ya yi a hankali zai fice da ga cikin ɗakin, Mami tayi saurin Miƙewa tsaye, jikinta na rawa ta fisgo Salman baya tare da sanyawa ƙofar key. Salman ya ɗaga idanun shi wanda su kayi jajur, a hankali kuma ya ce.

"You are too tired Mami, za ki samu headache fa, ki kwanta ki huta"
Girgiza masa kai ta yi ta ce  "listen to me Salman, at least listening to your mother Salman, Wlh Allah Abra ba ƴa ta bace, I have nothing to do with her, ban taɓa shayar da ita nono na ba, Everything that happens is your Father's plan, I'm just pretending, na gaji da yadda ya ke fifita ta akanmu da mu ke dolensa"

Tuni jikin Salman ya fara rawa, tunaninsa ya rabu kashi-kashi kowanne da abunda yake faɗa masa, "Salman Mahaifiyarka ce, ba zata yi maka ƙarya ba" wata zuciyar ta gaya masa.
"Salman kada ka yarda daman can Mami ba son Abra take ba, tana nuna masa rashin so irin na É—an fari ne kawai"

A raunane yace "Mami ke fa Uwa ce? Ta ya ya zaki dinga sheganta Æ´ar da ki ka haifa? Me Yaya tayi maki Maki? You don't love her, that's all, but stop harassing her ki dai na sheganta ta don Allah"

Da Mamaki Mami tace.
"Salman kana tunanin zan maka ƙarya? Mene yasa kai ban ce bani na haifeka ba? Mene yasa bance ban shayar da kai nono na ba? Mene yasa ban sheganta ka ba? Because you are my son, my blood, biological son. Kai na ɗauki cikin ka, naji zafin haihuwar ka, na raineka. kasan akan Abra nayi haihuwar da ban shirya ba? Na haifeka saboda bala'i a kitchen, Gaba ɗaya Abra ta ɗauke min wani jin daɗin rayuwa da farin ciki? Tun kana cikin cikina na fara samun matsala da mahaifinka, shiyasa na ke ta ƙoƙarin nesanta ka da ita, kai ɗan sunna ne ka daina haɗa kanka da ƴar karuwa.....,"

"Mami!!!!!!"
Salman ya faɗa jikinsa ko'ina rawa yake, ya kasa ɗaukan maganganun ta wanda suke neman haukata masa ƙwaƙwalwa, saboda muninsu. Cikin rawar Murya ya ce.
"Ba zan yarda ba, Yaya Æ´ar kice kamar yadda nake É—an ki, that's all"
Mami ta kalli Salman sosai ta ce "Kana nufin zan maka ƙarya Salman?" Shiru ya yi mata kansa a ƙasa amma idanunsa sunyi jaa sosai sai numfashi yake fitarwa, ji yake kamar mafarki ya ke.

"Kana tunanin zan maka ƙarya, kaf dangina da na mahaifinka da wa ka ga ta na kama? Akwai me irin siffarta?" Salman dai ya yi shiru, kansa na ƙasa bawai bai yarda bane, gaba ɗaya bashi da nutsuwar fahimtar Maganar tata.
A zafafe Hajiya Na'ima tace "Answer my questions Salman Khamal Khamis?"  Salman ya ɗaga kansa tare da kallon Mami a hankali ya ce. "Ban ƙaryata ki ba Mami, na kasa yadda ne kawai...,"

Ɗauke shi tayi da ƙyakƙyawan mari tace "Ni nayi kuskure tun farko, to kaje duk uban wanda zaka tambaya kaje ka tambaya Abra Shegiya ce, Abra TSINTACCIYA ce, Abra ƴar karuwa ce...!!"
Tana faɗin haka ta koma saman gado ta zauna, Da sauri Salman ya nufi ƙofa zai fita.

"Salman"
Mami ta kira sunansa da ƙarfi, kiran da ya sanya ya yi saurin juyawa tare da kallon direction ɗin da take zaune, da hannu tai masa nuni da ya zo.
Bai mata musu ba ya Ƙarasa wajanta kansa a ƙasa, hannunsa ta kama muryarta na rawa tace.

"This is an secret between us, ba wai dan ba ni da gaskiya ba, saboda ina son in kasance da kai da kuma Mijina, idan ka faÉ—awa wani ko wata cewa ni na faÉ—a maka, Mahaifinka zai datse igiyar auren dake tsakaninmu, I don't like that Salman, I love my husband, i so much love your father shi ya sa nake ta zaune har yanzu, sannan ina fatan za ka nesanta kan ka da ga wannan yarinyar"

Kallonta kawai Salman ke yi, bai taɓa ganin Mami na kuka ba sai yanzu, mene gaskiyar Al'amarin? Ta shi ya yi jiki a sanyaye sai da ya je bakin ƙofa Mami ta ce.
"Ka saka a ranka, ba zan taɓa so da ƙaunar Abra ba, ina kishinta sosai kishin kuma akan ka ne, duk wani plan da muka shirya da Khamal akanka ta wargatsa, She take away my happiness, she destroyed my house, to the extent ta fini kima a idon mahaifinka"
Tana faÉ—in haka ta saki kuka sosai, gaba É—aya matar data kirata a waya ta gama wargatsa mata lissafi.

Da sauri Salman ya bar cikin ɗakin jikinsa na ɓari, ko Kallon gabansa ba ya yi tashin hankali ya bayyana akan fuskarsa, yana zuwa ɗakinsa ya faɗa kan gado tare da jan duvet ya lulluɓe jikinsa, wani irin zazzaɓi mai zafi ya rufe shi, he can't believe cewa Abra ba ƴar Mami bace, har yanzu ya kasa yarda ko kuma fahimtar hakan.
Shiru ya yi haƙoransa na haɗuwa waje guda, ya zama kamar wani zautacce, ya kasa yadda, bacci ya ƙauracewa idanunsa how could he believes that Abra ba sister ɗinsa ba ce, yadda ya ke jin ta a ranshi, ya sa maganganun Mamin su ka kasa tasiri a zuciyar sa, sai dai kuma ko me za'ayi ba zai taɓa yadda Abra karuwa ce ta haifawa Abbi ita ba, bacci ɓarawo shine ya sace Salman cikin dare.

Gefen Hajiya Na'ima kuma, daren black night ya zame mata, Babu wanda ya yi baccin kirki sai Abra. Wacce ake ta Masifa a kanta, she slept peacefully, ba ta san me yake faruwa ba.

Gajiyar da Abra ta yi, bai hana ta tashi tun 7 na safe ba ta fara gyara gidan, ba tai Mamakin yadda ta ji gidan shiru ba, Faris ne kawai ya tsaya mata a rai, domin tasan da wuri yake fitowa ta yata aiki.
Tana tsaye a kicthen, sanye da pech ɗin pyjamas ta ɗora hijab akai, wuƙa ce a hannunta tana yanka Onion  With red pepper wanda Zatai using da shi, wajan yiwa Abbi ƙosan da yake so. Few minutes ta gama haɗa ƙullin ƙosan da ya sha kayan ƙamshi da Egg.
Tana gama soya ƙosan, ta ɗakko malkaɗɗan ƙullinta na kunun gyaɗa, wanda ya sha haɗin, Danyar gyaɗa, Dafaffiyar
shinkafa, sugar, madara, Leman tsami, Filawa. 15 minutes to 20 ta kammala kunun gyaÉ—ar, tana gamawa ta haÉ—awa Salman Smoothies. HaÉ—a komai ta yi akan dining table, zuciyarta fal tunanin abinda ya hana Salman fitowa.

Cikin sanyin jikin nan nata, ta yi wanka ta shirya cikin wata blue ɗin Abaya mai stones, ta yi rolling kanta da Vail ɗin, Oval shape face ɗin ta, ya sake fitowa kyanta na ƴan matanci, ya bayyana a fili da Wahala mace ta kalli Abra bata sake Kallonta ba, balle kuma namiji. Ƙyakƙyawan idanunta ta ja ta rufe tana jin yadda hearing aid ɗin nan sometimes yake damunta.

Flat shoe ta saka ta nufi Main Parlour, amma ga Mamakin ta har zuwa lokacin babu kowa a parlourn, da fararen idanunta take bin cikin wajan dining table da kallo, a nutse ta nufi bedroom É—in Salman domin tabbatar da lafiyarsa.
A hankali ta tura ƙofar ɗakin, Salman na kwance har lokacin idanunsa biyu, bawai barci ya ke ba, Ƙamshin turarenta kawai ya shaƙa wanda ya tabbatar masa Yayarsa ce, da sauri ya rufe idanunsa yana ƙara narkewa jikin bargon daya rufe jikinsa da shi.

Abra ta kalli Salman, cikin sanyin murya ta ce."You haven't woken up yet?" Ƙara rufe idanunsa Salman ya yi.

"Faris"
Abra ta ƙara kiran sunansa tana yaye bargon daya lulluɓe jikinsa da shi, Shiru ya sake yi ma ta baya son ko haɗa idanu ya yi da ita. Kamar Abra za ta yi kuka ta ce.
"Please Faris wake up, It's already morning"
Ta faɗa a sanyaye kamar mai raɗa. Tana ƙoƙarin zare bargon da ga jikinsa baki ɗaya, Salman ya yi saurin riƙewa tare da juyowa baki ɗaya zuwa inda Abra take zaune.

Kallon juna su kayi, shi dai bai Magana ba, sai bin ta da ido da yake. Abra ta ce.
"Barcin me kake haka?"
Idanunsa ya mayar kan hannunta data riƙe bargon, sai kuma ya ware idanun shi ya ce.
"Yaya.."
Abra ta kwaɓe fuska ta ce "Ba wani yaya, kawai ka je kayi wanka sai muyi breakfast, ka ga yau har Smoothies na yi maka"

Salman ya Girgiza kai idanun shi a ƙasa yana kallon hannunta ya ce.
"Ba wannan ba yaya" "to mene?" Abra ta faɗa da ɗan sauri ganin gaba ɗaya Salman baya cikin mood ɗin sa, langwaɓar ma ta da kai gefe ya yi cikin ƙasa da murya ya ce.
"Have you forgotten?"
Ta ware idanunta, sai kuma ta ce "Na manta"
Murmushi kawai ya yi ma ta yana Girgiza kansa da ke masa ciwo.
Ganin ya yi shiru kuma ba shi da alamun mgn Abra ta ce "Kayi shiru?"
"A'a ba komai yayata"
Ta ce "to tashi ka yi wanka" ya dafe kansa ya ce
"Ke yaya wannan wankan kamar ibada, kai na kemin ciwo sosai, sanyi-sanyi na ke ji"
Chapter 31 · 0% Book details