Sashe 98
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Hmm, wai ashe Salman ya je gidanta bamu sani ba?".
ÆŠan juyowa Abbi yayi ya kalli Mami ya tsuke fuska ya ce "A kan me zai je mata gida, ko bai san matar Aure ba ce yanzu, salon yaje ya janyo mata matsala a gidan Aurenta?"
"Ai shiyasa na ke son a yiwa tufkar hanci, har ya iya zuwa Nigeria yaje gidanta amma mu bamu ganshi ba, Akwai matsala, akwai buƙatar kaje can ƙasar da kanka".
"Ban gaya miki kar ki sake yi mini zancen inje nemo miki É—anki ba? Ba in da zani".
"Dan Allah kayi haƙuri ba dan halina ba, kar in rasa ɗana kuskure ne na riga na yi shi, dan girman Allah Major ka yi haƙuri".
Miƙewa yayi ya ce "Sai kuma ki yi". Da sauri ta zube a kan ƙafafuwanta ta riƙe ƙafarsa tana kuka "Don Allah Maajor kar ka yi mini haka, dan Allah ka yi mini afuwa". Kuka take sosai kamar ƙaramar yarinya wanda hakan ya sanya tausayinta ya kama shi.
Hannunsa ya sanya ya É—agota tsaye ya ce "ki daina mini kuka, zan ga abin da zan yi a kai"
Rungume shi ta yi tana kuka ta ce "Thank you very much dear".
Abin duniya ya sanya Abra a gaba, dan yanzu idan jikinta yayi ƙaiƙayi ta sosa sai wani irin dabbare dabbare ya fito a kan fatarta ga wasu irin ƙananan ƙuraje da ke fito mata har cikin kanta, ta yanke shawarar idan lokacin komawarta awo yayi, za tayi musu bayani su bata magani.
Haka nan tana kwance ta ji ba abinda take buƙata sai kasancewa a jikin Adnan.
Miƙewa tayi ta fito falo, ta tarar da Adnan yana zaune yana aiki a kan system ɗin sa, takawa tayi a hankali ta ƙarasa in da yake ta zauna, ba tace masa komai ba, shima bece mata ba, a hankali ta zame ta kwanta a jikinsa tana sauke numfashi, tana cigaba da jin tamkar ana kakkarya ƙasusuwan jikinta.
Ture system ɗin yayi ya janyota jikinsa, sai da a wannan karon yayi mamakin samun haɗin kanta, sainda ya bari tayi reaching highest peak, Sannan ya tureta da ga jikinsa, tare da faɗin "Jarababbiya kawai" bin sa ta yi da ido galala tana kallon ikon Allah. Ya miƙe ya bar mata falon baki ɗaya.
Haushin kanta ne ya kamata, da ba ta zo in da yake ba da duk haka bata faru ba, amma ya za tayi ita kaɗai ta san mai take ji a jikinta, kasancewarta a jikinsa skin to skin yana sanyawa ta ji sauƙin zafin da take ji a cikin jikinta.
Haka ta lallaɓa ta koma ɗakinta, sai dai ba kunya Adnan ya dawo cikin dare yayi abin da Allah ya nufe shi da yi.
Lokacin da yake ƙoƙarin tashi, ta rirriƙe shi tana kuka ta ce "Dan Allah Sp ka tsaya tare da ni, ko bacci in samu in yi, ɗumin jikinka kawai nake buƙata, dan Allah".
"Kin daɗe ba ki ji ɗumin jikin nawa ba? Dalla cikani in je in kwanta, gobe in Allah ya kaimu ƙarfe huɗu zan in tafi Enugu".
"Sp a haka zaka tafi ka bar ni? Dan Allah kar ka tafi ka barni a wannan halin".
"Hmm kalleki da Allah, ƙil da da ɗigon imani a zuciyar mahaifinki, da kin bani tausayi, amma da na tuno mahaifinki sam sai in kasa jin taisayinki, cikani dalla in kin ha dama ki tashi ki gyara jikinki, ko ki ta zama da najasa ƙazama" haka Abra ta bi shi da ido, tana zubar da hawaye.
Washegari da safe da ƙyar ta iya tashi, ji take tamkar iska zata ɗagata ta watsar, salla kawai ta iya yi ta koma ta kwanta ko Abinci ba ta ci ba.
Tana nan kwance salla kawai ke tashinta, Adnan ya shigo É—akinta, ya tarar da ita a cikin bargo.
Haushi ne ya kama shi, gani yake har da langwai Abra ta ke yi.
"Wai ke malama meye haka? Sai kace a kan ki aka fara ciki? Dalla tashi". Shiru ta yi masa, ita da da wannan masifar da yake mata, dama rungumeta zai yi taji É—umin jikinsa.
Yaye bargon yayi, ya janyota "Ke kullum cikin kwanciya kamar ruwa, ki dinga ƙwarara jikinki malama".
"Ba zan iya ba ne, ni kaÉ—ai na san me nake ji, dan Allah ka yi mini Alfarma, ko mintuna uku ne in yi a jikinka".
Gefen fuskar Abra ya kalla, ya ga wasu ƙananan ƙuraje sun mata dabbare-dabbare a gefen fuskarta ba kyan gani, ya kalli hannunta in da ya riƙe, ya ga har hannunta duk sun feso. Da hanzari ya cikata ya ja da baya, saboda yadda tsigar jikinsa ta tashi.
"Meye wannan a jikinki haka?"
Ta kalli jikinta ta ce 'Nima ban sani ba".
"A haka kike cewa in rungume ki? Allah ya sa ba da wannan abun a jikinki na haɗa shimfiɗa da ke ba jiya, wannan ai ƙurajen ƙazanta ne, wannan ai ƙarzuwa ce. Kinga ni ga jakata can a Falo na shirya, sai jibi zan dawo an turani aiki"
"Dan Allah kar ka tafi ka bar ni a haka, dan Allah Adnan".
"Saboda me na zan tafi ba, in zauna in cigaba da kallon wannan ƙazantar".
"Adnan ka yaudareni da daɗaɗan kalamanka na amince na aureka, Ruhin Adnan Alyu Matawalle, Zan rayu da ke in kula da ke, zan kasance mai tausayi a gareki, da duk irin wannan alƙawarurrukan, amma ka kasa cika ko guda. Shikenan ka je Allah ya yafe maka, Ya kai ka in da zaka lafiya" ta juya tana ƙoƙarin kwanciya ya ga yadda tsakiyar kanta duk babu, ya zube. Ga wannan ƙurajen duk sun yi tambari a gadon bayanta.
Ya sa kai ya fice ya bar gidan, yana cigaba da jin yadda tsigar jikinsa ke tashi.
Kwana biyu ya zaman banɗaki ma da ƙyar take iya zuwa, dama Abinci ba'a magana ba iya ci take ba, ta yanke shawarar zuwa Asibiti, dan ba zata iya jure cigaba da zama a haka har ranar awonta ta zagayo ba, dan da wani irin ciwon baya da ƙafafuwa ta tashi.
Da ƙyar tana haki ta fito harabar gidan, da yake tun lokacin da ta gudu gidan su Adnan, ya kawo maigadi ya ajiye a gate.
Mai gadin na ganin Abra na bin bango, ya taso da gudu yana faÉ—in "hajiya lafiya?"
Kan tayi Magana, taga gari yayi mata duhu, yana jujjuya mata, ta yanke jiki ta faɗi a ƙasa.
Mai gadin ya fita da gudu, ya ƙwanƙwasawa maƙwabtansu ƙofa, da gudu suka dawo tare da maigidan, suka tarar da Abra a kwance a ƙasa, maƙwabcin ya kira matarsa suka sanya Abra a mota zuwa Asibiti.
GY BULAMA HOSPITAL AND MATERNITY
Ba free bane na kuɗi ne ₦300 kacal ku tuntuɓe mu a kan lambar wayoyin mu
08081012143
09047871750
[10/28, 5:00 PM] Abk: Cikin gaggawa suka shiga da Abra Asibitin.
Bulama baya nan, doctor Aminu ne a bakin aiki, cikin gaggawa suka biya kuɗin ganin likitan, kasancewar maƙocin su Abran yana da file a Asibitin.
Doctor Aminu ne yaje kan Abra, ya tambayi ina document É—in ta na awo?
Maƙwabcin ya ce "Wallahi ban sani ba, matar maƙwabcina ce".
Doctor Aminu ya ce "Babu halin in taɓa ta ban san history ɗin ta ba, dan haka a nemo mijinta".
Aka kira lambar Adnan ta ƙi shiga, gashi ba wanda ya ke da lambar wani na Abra.
Maƙwabcin ya ce "A taimaka a duba ta, a bata taimakon gaggawa mana".
Doctor ya ce "Bani da ikon taɓa ta banga documents ɗinta na awo ba, kuma kaga tases na ANC a Asibitin nan dubu hamsin ne, abu ɗaya zan iya yi muku, kuju ku yi scaning yanzu a kawo, kan in tashi idan na tashi sai dai ku jira likitan yamma.
Haka suka kwashi Abra suka tafi sacaning, sai dan kan su dawo liktan ya tafi, sai dai su jira Bulma, wanda sai biyar zai shigo.
Gaba daya kuma an rasa lambobin Adnan, maƙwabciyar ta koma gidan Shi ta duba ko zata ga wayar Abra, amma ba ta gani ba.
A haka Abra ta farfaÉ—o, tana kiran sunan Allah sai juyi take Saboda azabar ciwon da take ji. Ba yadda ba suyi da Abra tayi magana ba, amm ta kasa salati kawai take yi, tana ambaton Allah.
Sai biyar da kwata sannan Bulama ya shigo, ko da ya shigo Nurse É—in da take duty taje ta yi masa bayani, bai je kan Abra ba sai cewa ya yi sai sun biya wannan dubu hamsin É—in ta awo, sannan zai dubata kuma wannan scaning ya nuna akwai matsala dole ayi aiki, a cire cikin da gaggawa kar a rasa jaririyar, saboda ruwan da take ciki yayi kaÉ—an, dan haka sai an biya wannan dubu hamsin na awo da ba ta yi a Asibitin ba, sanan a biya dubu É—ari biyu da hamsin wanda za a yi mata aiki.
Maƙwbcin ya ce Gaskiya ba zai iya biyan wannan kuɗin haka bai sai dai aita jarraba lambar mijinta har a samu.
Matar maƙocin ta je ta samu Nurses ta ce "dan Allah ko wata allurar ce ku yi mata kan mijinta ya zo, Wallahi ko nawa ne zai biya"
ÆŠayar ta ce "Wallahi bamu da ikon yin hakan, tun da baku biya kuÉ—i ba, amma bari inje in tambayi likitan.
Nurse É—in ta koma gurin Bulama a fusace ya ce "Ke kar ki isheni, ba a biya kuÉ— ba ya zan yi? Kuje ku yi mata wata analgesic É—in ta samu releif.
Nurse É—in ta fito tana tunain wace allura ce analgesic, tun da ita food hygiene ta karanta ba Nurse ba ce.
Gashi ita ganinta abun kunya ne ta tambayi abokan aikinta, da haka ta jeta ɗauko wata allura da take kyautata zaton ita ce Analgesic.
Ta huda Abra ya kai sau bakwai sannan ta samu jijiyarta, ashe ba a allurar a jijiya, bayan ta gama yin allurar ta tafi mintuna talatin jini ya ɓallewa Abra.
Innalillahi wa Innalillahi raji'un, a guje matar da suka kawo Abra ta je ta samu Nurses É—in ta gaya musu, suka zo suka duba suka tafi suka gayawa Bulama, amma ya ce 'ba Abin da zai iya a kai sai an biya kuÉ—in aiki.