← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 145

Sashe 139

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Angel, lokuta da dama zukatanmu suka mato a so da ƙaunar wani abu, har mu dinga jin tamkar rasa wannan abu na nufin tawaya ko samun naƙasu ga rayuwar mu, sai dai kash, tun gabanin mu zo duniya Alƙalamin ƙaddara ya kammala zana mana ƙaddarorinmu. Sai dai muyi ta lalube a duhu da sanyawa zukatanmu burika daban daban, wasu su cika wasu kuma saɓanin haka, wanda wannan hikima ce ta ubangiji da ba a masa dole.
Tabbas soyayya ba ƙarya bace ba, na rayu da soyayyar ki a lokacin da nake zaton, tsananin ƙauna ce ta 'yan uwantaka, sai bayan bayyanar wani sirri da ya zama makamin ruguza wancan tunani da nake a baya, ya sauya akalar wannan soyayyar da nake miki.
Abra ba kiyi Mamaki ba, yadda abubuwa suka dinga faruwa cikin hukuncin ubangiji ba, sama ta ka Adnan ya kutso ratuwarki, cikin ƙiftawa da bisimillah soyayya ta sanya kika rusa burin Abbi a kanki yayi miki aure. Sai dai duk da Auren da ki kai da zimmar Soyayya yayi silar rabuwar duniyarki zuwa abu biyu, idan ki ka tsaya da tunaniki kika duba hukuncin ubangiji da yadda abubuwa suka dinga wakana tamkar shirin film, sai ki gano ashe Adnan shi ne ƙaddarar ki. Duk da ya cuzguna miki a baya, sai ki duba a silarsa kuma kin haɗu da farincikin da kuɗi ba zai saya miki ba, ga iyayenki kin gano, ga kuma a silarsa 'yar uwakki ta bayyana, a silarsa Allah ya yi miki kyautar ɗan mutum sukutum guda.
Yayata, ke mace ce me yafiya, wadda muka rayu ta gini a kan raunin zuciya, haƙuri da kuma kawaici, Adnan be gaya mini meke tsakaninku ba, amma yanayinsa ya nuna yana cikin damuwa, kuma kin san bashi da cikakkiyar lafiya, kika iya yafewa Mami balle uban 'yar ki? Kiyi tunanin my Angel"
Tuni hawaye ya wanke fuskar Abra, saboda tasirin kalaman Salman a a zuciyarta, cikin kuka ta ce "Faris, Adnan ya cutar da ni san.....

"Shhh, a sanadiyar yafiyar da zaki masa, sai Allah ya yi miki abin da baki zata ba, ko kin manta shine masoyinki na farko? Am sorry to say Abra, mahaifinki ya cutar da zuciyar Adnan, duk da hakan ba hujja bane na ya huce a kanki, amma ke a kan kanki, ya faru a Asibitinsa, cikin duhun dare ba tare da ya san ke 'yar sa ba ce, idan aka ce uwa Yaya an gama magana, mahaifinki ya cancanci ya nemi yafiyar waɗanda ya cutar, ba wannan maganar muke ba, duk da shima ina son ki yafewa mahaifinki daga ke har Afra, dan kan mu wuce Dubai nake son, muje mu ganshi, dan Allah komai ya wuce yayata, musa a ranmu dukkaninmu Allah yayi mana zaɓi ne daidai da ƙaddarorinmu, da kuma abin da ya dace da mu"

Tuni hawaye suka wanke fuskar Abra, Salman ya dinga share mata ya cigaba da rarrashinta, har ta É—an samu nutsuwa ta cigaba da aikinta, har yana tayata.
Bayan ta kammala girkin, har suka yi bidirn cin abincin su, Adnan na É—aki bai fito ba, bata son Salman ya kuma magana, dan haka ta bi Adnan É—aki, ta tarar da shi a kwance a kan gado, yayi shiri ya zubawa wuri É—aya ido.
Shigowarta ce ta sanya ya mayar da idonsa kanta, ta ƙaraso ta tsaya tana kallonsa "Ba zaka ci Abinci bane?".
"Angel bana jin yunwa sam, kewarki ce ke damuna" taɓe baki tayi ta ce "Dama zan gaya maka ne, gobe in Allah ya kaimu ƙarfe huɗu, Dubai zamu tafi, zan bi su Salman, zamuje wurin Ummi muyi mata sati ɗaya sannan mu dawo"

Cikin mamaki Adnan ya kalli Abra "Amma baki gaya mini ba sai yanzu?".

"Amma dai na gaya maka ko? Ba É—aukar jaka nayi na tafi baka sani ba" tai maganar tana harrasa up and down.

Adnan ya jinjina kai ya ce "Haka ne, Allah Ya kiyaye hanya" ta amsa da Ameen ta fice ta bar masa É—akin, yana cigaba da mamakin yadda gaba É—aya Abra ta sauya, tamkar an canzo masa ita da wata.

A gidan su Salman suka kwana, sai dai basu fuskanci cewar ba É—aki É—aya su Abra suke ba.

Washegari tun azahar Abra ta gama kintsawa, saboda zasu je prison wurin mahaifinsu.

A É—aki ta tarar da Adnan yana kwance, da alama jikinsa ya tashi.
"Zamu tafi, kuma na ga tun safe baka sake fitowa ba"
"Angel bana jin daÉ—in jikina ne, dan Allah kar ki tafi ki barni".
Idanunta ne suka cika da hawaye ta ce "Au kar in tafi in barka kace? Ai gara ni wurin iyayena zani, ka manta ni ranar da ka sa ƙafa ka tafi ka barni, kana ƙyanƙyamin jikina, saboda ƙazantar da ta fito a jikina?" Shiru Adnan yayi ya rintse idanuwa a hankali ya furta "Is ok Angel, Allah ya kiyaye hanya, ki gaishe mini da Ummina, ba zan iya driving ba da na raka ku, bari driver ya kai ku" Ya dafe ƙirjinsa a hankali ya miƙe, wani abu ne mai kama da tausayi ya fara fizgarta, amma ta maze.
Adnan ya fito falo, yana murmushi ya kalli Salman ya ce "Malam shine kawai zaka É—auke mini mata, bayan kai kana tare da matarka"
Salman yayi murmushi ya ce "Ko zaka bimu ne? Kar mu gudu da ita?"

Adnan ya ce "Ai ina ganin likita ne, muje driver ya kai ku"
Suka ƙarasa har gaban mota, Abra na ƙoƙarin shiga motar, Adnan ya riƙo hannunta ta baya, ya saka bakinsa a daidai kunnenta ya ce "My Angel, ina sonki da yawa, Allah ya tsare mini ke ya dawo da ku lafiya, dan Allah Abrana ki yafe mini,. Ban sani ba ko kan ku dawo rai yayi halinsa, bana son in je wurin Ubangiji da hakkinki, dan Allah ki yafe mini" ya ƙarasa maganar hawayensa na zirarowa yana gangarowa daga wuyanta zuwa cikin rigarta. Da haka ya cikata, ya juya ya koma cikin gida.
Jikin Abra yayi sanyi ƙalau, amma ba ta ji zata fasa tafiyarta ba.
Prison suka fara zuwa, aka fito musu da Bulama, gaba ɗaya ya fita hayyacinsa, duk wannan gayun babu, jar fatar nan tasa duk tayi baƙi.
Abra na ganin halin da yake ciki ta fashe da kuka, ta rungume Bulama tana ta shesheƙar kuka, Bulama ma rungumeta ya yi shima yana kuka har da majina.
" 'ya ta dan Allah ki yafe mini, ke da 'yar uwakki dan Allah ku yafe mini" Afra ma dai kuka take yi, sai dai ta kasa zuwa in da yake.
Abra ta shiga share masa hawayen fuskarsa ta ce "Daddy ya ake ciki da zaman kotun naka? Insha Allah zan fara halarta kuma Insha Allah zan shawo kan Ummi ta yafe maka"
Kalmar Daddy da ta kira shi da shi, yafi komai faranta masa rai.
"Daughter, dan Allah ki yiwa mijinki godiya, duk da munin laifin da na aikata masa, tun ranar da aka fara zaman kotu, kullum shikaɗai ne wani nawa da yake zuwa, sai abokaina, kuma ya ɗaukar mini ƙwararrun lauyoyi har guda uku da zasu kareni, kuma koda Yaushe cikin yi mini aike yake na kayan Abinci, mahaifinsa ma ya zo, iyayenki ma Major da mai ɗakinsa sun zo. dan Allah ki nema mini gafarar mijinki akan abin da na aikata masa" Shiru Abra tayi, sam Adnan bai taɓa gaya mata wannan maganar ba.
Suna tsaka da magana ne, gandiroba ya ce lokaci ya yi, zasu mayar da Bulama, suka dinga kuka ƙarshe sai Salman ne yayi ta aikin rarrashi da basu haƙuri.

Har suka isa Dubai, Abra na Mamakin a yadda Adnan ya tsani mahaifinta, amma ya iya taimaka masa, take taji kaso mafi rinjaye na haushinsa da take ji ya ragu a zuciyarta, dama can ƙasan zuciyarta tana jin tausayinsa dannewa kawai take yi.

Ummi ta rasa in da zata saka kanta dan daɗi, ganin yaranta a tare da ita, ta dinga farinciki tana nan nan da su, shi kansa Salman tana matuƙar son yaron nan, saboda kulawarsa ga yaran nata, kamar yadda yayi mata alƙawari ya cika, ya kawo mata yaranta wurinta.
Sai dai tayi ta mita, saboda rashin kawo mata Little.
"Abra ina wannan mijin naki masifaffe, naji babanki wai shi suka kuma aurawa, koda yake mahaifinki ne ya janyo miki koma menene"

"Ummi ni mijina ba masifaffe bane, wato ba kya son mijina sai wannan É—an naki ko?" Tayi maganar tana tura baki.
Ummi ta ce "Abra raina ya ɓaci da jin abinda ya yi miki ne, ban san me su Major suka gani suka kuma bashi ke ba, ni so nayi su bani ke in aura miki balarabe"
Abra ta ce "Ni bana son farin namiji, Caramel nake so kamar baban little" Hira me cike da soyayya da ƙaunar juna ce ta shiga tsakaninsu, a haka Abra ta shigo da batun Ummi ta yafe wa Daddyn su, nan da nan Rumaisa ta haɗe rai ta ce "Ko dukiyarta zata ƙare, sai ta tabbatar an kai shi prison, kuma sai an nemo Matarsa an musu Shari'a a kan abin da ta aikata mata" Babarsu Abra na da sanyin hali, amma a wannan karon ta ɗau zafi da yawa, duk irin kukan da Abra tayi mata, fafur ta ƙi amincewa da yafewa Bulama.

Duk da tattali da kulawar da Ummi ke basu, hankalin Abra na Nigeria wurin mijinta, saboda yadda yake haki lokacin da zasu rabu, ta san yana jin jiki matuƙa, ga kuma wannan abun alkhairi da ya yiwa mahaifinsu.

Salman ya cigaba da yiwa Abra nasiha, a kan ta yafewa Adnan, mussaman duba da irin abin alkhairi da ya yiwa mahaifinta. Ita kanta ta san Adnan ya yi laushi na gaske.
Sai da Abra ta kwan goma a daddafe, gashi ta nemi lambar Adnan da ya dinga kiranta kwanakin baya, amma ba ta gano lambar a wayarta ba balle ta kira shi a waya, ta ji ya yake?.

Ranar kwana na goma sha É—aya, suka rako Abra airport, Abra da Afra sun sha kukan rabuwa, haka Abra ta hawo jirgi zuwa Nigeria.
Chapter 139 · 0% Book details