← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 145

Sashe 115

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sorry Allah ya baki haƙuri, kije ki kwanta sai da safe we will meet in the morning, ki shafa min kan Aishatul-humaira bye"

Daga haka ya miƙe ya nufi ɗakin Salima ba tare da ya sake cewa komai ba, ɗan juyowa ya yi yaga har lokacin tana tsaye ta ƙura masa idanu tana kallonsa ɗan murmushi Abbi yayi cikin tsokana yace.

"Ko zaki rakani É—akin amarya?"

Kukan da take dannewa ne ya ƙwace mata kawai ta fashe da kuka tare da rugawa da gudu ta shige ɗakinta ta rufo ƙofar tana ci-gaba da kukanta.
Murmushi kawai yayi kafin ya kakkashe komai ya wuce É—akin amarya Salima.

Washegari ma dai Na'ima ƙin tashi tayi bare tayi musu breakfast kamar yadda yawanci uwargida ce ke yi, sai ma Salimar ce tayi girkin, da tazo kiranta ma ko kallo bata ishe ta ba, cikin jin haushi Salima ta juya ta bar ɗakin tana faɗin

"Mtsww cikin ki ko cikina kar ma ki ci mana" ita kaÉ—ai tayi breakfast É—inta kasancewar da ma Abbi baya fitowa da wuri, tana cikin karyawar Abbi ya fito kujera ya ja ya zauna yana murmushi tare da faÉ—in
" Amarya bakya laifi" sunnar da kai tayi tana murmushi itama kafin ta miƙe tana tambayarsa mai zaici tayi serving ɗinsa, ganin Na'ima bata wajen ya sashi faɗin

"Ina antyn taki kuma kike cin abinci ke kaÉ—ai?"

Cikin kissa da kisisina ta shiga faÉ—in

"Wallahi nayi nayi ta zo muci abincin amma ko kallo ban isheta ba,kuma dama da naga ba tayi girkin ba na shiga kitchen nayi da kaina, shi ne naje part É—in nata atleast tazo muci amma ban san ko mane yake damunta ba ko zaka kirata?"

Miƙewa kawai Abbi yayi ba tare da ya karɓi plate ɗin soyayyen dankalin da take miƙa masa ba ya wuce ɗakin Na'ima

A kwance ya sameta ta bawa ƙofan baya, jingina yayi da ƙofan kafin yace

"Morning wifey"

Bata juyo ba bare ya sa ran zata kula shi,

"Me yasa kika ƙi fitowa muci abinci?"

"Bana ra'ayi a ƙoshe nake"Ta faɗa ba tare da ta juyo ba.

"Okay to, shikenan" ya faɗa tare da ƙarasawa ya ɗauki Aishatul-humaira dake ta wasan ta abin ta, zama yayi a gefen gadon yana mata wasa yana ɗan satan kallon Na'ima har dai ya gaji ya miƙe ya fice a ɗakin nata.
Shima kaɗan yaci abincin kafin ya miƙe ya fice a gidan ma gaba ɗaya.

Gidansu Ammi ya wuce ya gaishe su tare da sanar dasu dama yanaso ya koma bakin aikinsa cikin satinnan, babu wanda yace masa komai sai fatan alkhairi da suka masa tare da tambayar lafiyar su Na'imar.

A kishingiÉ—e yake akan kujerun da ke gaban beach É—in yana kallon yanda ruwa ke gudu akan surface É—in, yana sanye cikin kayan shan iska guntun wando ne da ya wuce gwuiwarsa da kaÉ—an sai riga short sleeve, idanunsa da sunglasses sai cup na soft drink dake hannunsa.
Faris kenan, wanda zuwa yanzu ya ƙara wani irin kyau da girma na ban mamaki, duk da har zuwa yanzu tunanin Abra ya kasa barin zuciya da gangar jikinsa, ya riga ya san ya rasa yayarsa har abada amma bai san me yasa ya kasa daina tunaninta ba.
A hankali ya ajiye cup É—in a gefensa yana É—aukar wayarsa ta ke ta ruri tun É—azun, ganin Mami ce mai kiran ya sashi saurin É—agawa tare da yin sallama.

Na'ima da har ta sadaƙar Faris bazai ɗauki wayar ba jin ya ɗauka ya sata fashewa da kuka.

"Faris ina son ganinka urgently please ka dawo gida, akwai matsala ka dawo ina buƙatarka a kusa dani"

Da sauri ya miƙe zaune hankali a tashe yake faɗin
"Mami, lafiya?me ya faru?me aka yi miki sanar dani"

Bata sake cewa komai ba sai ji yayi ta kashe wayar.

Cikin sauri ya lalubo number Abbi, bugu É—aya ana biyun ya É—auka yana faÉ—in

"Faris ya akayi? "

"Me ya sami Mami?"

"Da akayi me ?"

"Yanzu ta kirani tace in dawo tana buƙatata kuma naji tana kuka me ya faru Abbi"

"Kana jina Faris, kar ka damu da Maminka ta kasa daina tunanin Abra ne, maybe ta tuna ta ne shiyasa take kuka, ka kwantar da hankalinka, ka dage da karatunka duk da nasan bazaka iya dainawa ga baki É—aya ba but please ka rage tunani more especially akan Abra kaji?"

"Na ji Abbi but please you should be there for Mami, kaga yanzu bata da kowa bana nan yaya bata nan"
"I will, karka damu"

Daga haka suka yi sallama, ajiye wayar Faris yayi yana sauƙe numfashi, ya zai yi ya kasa hana kansa tunanin Abra, be couldnt stop himself but zai yi ƙoƙari yaga bai shafi studies ɗinsa ba insha Allah.

Ƴar Baba na kwance a daɗi tai shiru idanunta rufe amma ta lula duniyar tunani, waye wannan ɗan gayon da yake ta damunta ne? Wace kuma Babur take kowa. Ko dai Aljani ne?.
Da sauri ta girgiza kanta kafin a fili ta ce "Allah ya sauwaƙe na zama matarsa, ɗan Iska ne" da sauri ta ja iska tana shaƙar Ƙamshi ta ce "Kuma turarensa mai daɗi ne, amma baƙiƙƙirin dashi".
"Wai Meke damunki ne ƴar baba? Ki yi ta kwanciya a ɗaki kamar ruwa, maza tashi kafin na dokeki" turo baki tayi cikin taɓara wacce ta zama ɗibi'arta ta ce.
"Ni kam Inna idan kin tsaneni ne kawai ki faÉ—a mini na sani, bani da lafiya fa? Ba kiga na rame nai zuru-zuru ba, sai ki tayin mita da faÉ—a"

Inna ta shiga tafa hannu sosai tana faɗin "Na shiga uku, yau naga abin da yafi ƙarfina,wai wacce irin yarinya ce ke ƴar baba? Ace ba zaki hankali ba kisan Annabi ya faku kalli sa'aninki fa duk suna ɗakin mazajansu amma ke jiya iyau" "Inna kina nufin nafi ƙarfi kenan? Gudana nawa nake gaba ɗaya da zanfi ƙarfin fisabilillahi" sai ta fashe da kuka tana kifa kanta a cinya.
Zama Inna tayi tare da yin ƙasa da murya ta ce "Haba ƴar baba shallen Inna, ƴar gatan yayanta Musa, daina kukan kinji share hawayen ki saurare ni"

"Ba dole nayi kuka ba Inna, tunda Baba ya rasu mitar yau daban ta gobe daban, daman shike so na" Inna ta kamata ta ce "Ba haka bane, ai ni uwa ce ba zan so ki lalace ko kuma ki sangarce a aikin banza ba, shi ya sa nake tsawatar dake amma babu abin da nake so sama dake" Ƴar Baba na dry sosai ta ce "Inna kinfi so na fiye da Yaya Musa ko?" Inna ta ɗaga kai ta ce "Sosai ma, ina ruwana da wani Musa, yanzu dai tashi ki shirya ki amso mini gyaɗa tun safe ake sallama a nema" turo baki tayi tace "Ke Inna wai babu wata sana'a sai gyaɗa ni banga wata riba a ciki ba" Inna ta riƙe haɓa ta ce "Oh! To aini na gani maza tashi tunda mun shirya idan ba mitar kike so ba, saura kije ki yi ta tsokana kina ja mana bada hqr ana zama lafiya"

"Ni dai Inna ba zan kulaki ba, ki barni kawai da tunanin da nake shi kaɗai ya isheni" Inna ta ce "Meke damunki ƴar baba?" Shiru Ƴar baba tai tana mirginawa tare da juyawa Inna baya. Inna ta taɓe baki tai waje tana faɗin "Allah ya kyauta,ya shirya mini ke".

Inna na fita ƴar Baba ta miƙe ta cire kaya tare da nufar banɗaki wanka tai, ta shirya cikin wata atamfa mai kyau, duk da cewa a ƙauye take amma bata zama cikin mummunar kama, Baba kafin ya rasu yana iya ƙoƙarinsa ganin ya kyautata mata, komai ya gani ƴar Baba haka Yaya Musa. Hakan yasa take da komai na buƙatun rayuwa kaf ƙawayenta ta fisu suttura mai kyau.

Ƴar Baba na gyara zaman mayafin jikinta, ba wata kwalliyya a fuskarta dai kwalli da man leɓe hakan yasa fuskar tai sharr gwanin sha'awa, ga ɗan jikin nan nata ba auki wanda yake ƙara ɓoye shekarunta. "Allah ya a tsare, ki kula banda shirme banda....," Kafin Inna ta Ƙarasa Ƴar Baba ta ce "Banda tsona da kula samari, haka zaki ce ko? Ni fa duk na hadda ce wannan sai dai wani abun" girgiza kai kawai Inna tai. Ƴar Baba ta fita zuwa karɓar gyaɗa.

A hankali take tafiya duk wanda ta gani sai ta murguɗa masa baki "Ƴar Baba an fito ne?" Cewar wani saurayi riƙe ƙugunta ta yi tana murguɗa baki ta ce "Wai kai sani mene matsalar ka dani ne? Ko baƙin ciki naka baban baya son ka?" Sani ya ware ido ya ce "Wai ni na isa na haɗa kai na dake ne? Ai ke ce sarauniyar ƙauyen nan kawai ki bani dama na nuna bajinta ta" tsaki tai ta ce "Allah ya sauwaƙe me zan dake, jibi ƙaton baki da ido ƴan mitsi mitsi ka fita a harkata wallahi" tana faɗin haka tai gaba Sani ya bita da idanu. A haka ta Ƙarasa gidan amsar gyaɗar mai maimakon ta amsa kamar yadda Inna taso sai ta nemi waje ta zauna suka kafa hira.

Adnan na jingine a jikin wata bishiya ya harɗe hannayensa a ƙirji, yana sanye da wasu manyan kaya masu kyau, wanda suka haskaka baƙar fatarsa, fitowar sa kenan daga gidan da yake zaune sbd ya gaji da zama, honestly ma ba zai iya zama ba tare daya ƙara tozali da Yarinyar nan ma wacce yake jinta tamkar matarsa Abra. Lokacin guda so da ƙaunar Ƴar Baba ya gama ratsa zuciyarsa har yana jin babu abin da zai hana ya mayeta da gurbin murgayiya Abra Khamal Khamis. Ita ce zata goge masa tabon dake maƙale a zuciyarsa. Numfashi ya sauke yana duba agogon hannunsa ganin rana na shirin faɗuwa.

Yana ƙoƙarin juyawa idanunsa ya sauka akan ta tana tafe farantin gyaɗa na kanta sai fari dake da idanun. Wani sanyayyan murmushi ya yi yana dubanta frm head to toe. Buwayi gagara misali. Al-hakkamu mai tsara komai a lokacin da ya so. Yana ganin identical twins masu tsananin kama da juna, amma bai taɓa ganin mutane masu kama da juna irin ƴar Baba da Abra ba. "Something fishy" ya faɗa cikin ransa.
Chapter 115 · 0% Book details