Sashe 22
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari Bayan an idar da Sallar Asuba Abra ta yi lazimi da karatun Alƙur'ani kamar yadda, ta saba kullum ta nufi kitchen dan haɗa breakfast. Sai da ta fara tsaftace kitchen ɗin duk da ba ya tare da wani datti sannan ta fara aikin.
Around 6:40 Salman ya shigo kitchen É—in fuskarsa na nuna alamun tashin sa kenan daga bacci.
"Sleeping sickness, an tashi kenan?" Abra ta faÉ—a tana kallon sa.
Yamutsa fuska ya yi ya ce. "Baccin ma ko isa ta bai yi ba, na tashi ne kawai saboda school."
"Ba dole ba, tunda jiya ka raba dare kana ta aikin kallon Ball."
"Baza ki gane daɗin kallon Ball ba ne Yaya, na ce ki zauna muna yi tare amma ƙin ki."
"Wannan sai ku, ni ina zan iya."
Irish É—in da take soyawa ya É—auki yanka É—aya ya ci ya ce. "Sannu da aiki, ke kullum ba kya gajiya da yi mana daÉ—aÉ—an abinci masu motsa kunnen mutum, kuma gashi ke ba ci kike yi sosai ba."
Murmurshi ta yi ta ce. "Yanda kake da cin nan Salman idan ban zage na yi girki ba a gidan nan ai sai a samu matsala."
Murmurshin ya yi shi ma ya ce. "To Allah ya biya ki, bari na taya ki mu samu ladan tare."
Da sauri ta ce. "A'a ban ce ba, ka je ka shirya school kar mu yi late, nima na kusa gamawa." Ƙi ya yi ya ce shi dai sai ya taya ta, ita kuma ba ƙi take ba, tsoron kar Mami ta zo ta gan shi ne, duk da Abbi yana nan baza ta ce komai ba a yanzu, amma yana tafiya duk sai ta fanshe mata masifarta.
Tare suka kammala aikin suka kai komai dinning, suna aikin suna hira cikin nishaɗi da ƙaunar junansu. Bayan sun gama kowa ya nufi ɗakinsa dan yin wanka tare da shiryawa.
Salman ya riga ta fitowa, dan dama ita yanda take da sanyi haka take yin komai a sanyaye. 5 minutes da zaman shi ita ma ta fito sanye cikin uniform ɗinta mai kyau riga da skirt gami da ɗan ƙaramin hijab iya ƙirji. Salman ya bi ta da kallo. Tana duban sa ta ce. "What are you waiting for? ka zauna kana kallo na baza ka zuba abinci ka ci ba."
"Ke nake jira mana Yayata, kin san ai ba zan iya cin abinci ni kaɗai ba kya nan ba." Ya yi ƙarashe zancen tare da jan kujerar kusa da ita ya zauna. Dai-dai nan su Khamal suka yi sallama a parlour'n, Hajiya Na'ima ta ci kwalliya sai ƙamshi take zubawa, kamar babu wani abu na ɓacin rai dake damun ta, Salman ya bi ta da kallo yanayin da ya gan ta jiya ya faɗo masa a cikin rai.
"Good Morning Abbi and Mami" Abra ta faÉ—a fuskarta É—auke da murmurshi.
"Morning Daughter, da fatan kin tashi lafiya?"
"Lafiya ƙalau Abbina."
Cikin murmushin munafurci Na'ima ta ce, "Uhm, Æ´ar gidan Abbi, wato shi kaÉ—ai kika gani ko?"
Sunkuyar da kai kawai Abra ta yi, mamakin halin mahaifiyarsu na yanda take nuna mata a gaban Abbi yana cika mata zuciya. Khamal ne ya bawa Na'ima amsa da faÉ—in.
"Me kuma ya faru? Yau ma zaki ce ta nuna bambancin ne? Na ga dai a tare ta gaishe mu."
"Amma ai sunanka ta fara kira kafin ni."
Murmurshi ya yi ya ce. "Mr Jealousy, ga naki ɗan nan ai kema, yanda yake kallon ki na san ke zai fara gaisarwa. Salman ya murmusa sannan ya gaishe su a tare. Bayan sun zauna Abra ta yi serving ɗinsu, Khamal sai saka mata albarka yake yi tare da yaba mata. Hakan ba ƙaramin ƙona ran Na'ima yake yi ba, ji take kamar ta ɗauki ruwan tea ɗin dake tururi ta sheƙa mata a fuska, ƙarin abun takaicin Salman sai taya shi yabon Abra yake yi. Babu yadda ta iya ita ma haka ta dinga yaƙe tana taya su.
Bayan sun gama suka ɗauko school bags ɗinsu suka yiwa iyayen nasu sallama suka fice. Kafin su ƙarasa parking space Salman ya ɓata fuska ya ce, "Uniform ɗin nan kamar ya matse ki sosai Yaya."
"Ba bu abun da ya mun, me ka gani?"
"Kawai ni dai haka nake gani, haushi ma nake ji kina yawo a school a haka."
Cikin mamaki Abra ta ce, "Me yasa? Duk sauran students É—in dake yawo a haka fa?"
"Ni ke kaÉ—ai na sani, gaskiya zan cewa Abbi duk ya sauya miki uniform É—inki, ba na son ganin ki da waÉ—annan."
Tace "Sannu Yaya."
"Ai dama ni ne Yayan ko ba ki faɗa ba." Dai-dai nan suka ƙarasa parking space inda direban sojan da zai kai su yake jiran su, hakan yasa Abra ba ta kuma magana ba.
Masha Allah, an samu sauyin gwamnati, bayan shafe dogon lokaci waccan jami'iyya ta na mulki, duk ta yi iyakar bakin ƙoƙarin ta, gurin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro, amma abun ya ci tura, a wannan karon sabuwar gwamnatin ta zo da sabbin tsare tsare, ciki har da yiwa harkar tsaro garan bawul, aka kawo sauye sauye da dama.
Sauyin gwamnati da aka samu ya sa da yawa daga cikin iyayen gidan General Ibrahim da suke harƙallar su tare ba su koma ba, sedai a hakan gwamnatin ta sake ɗibar kara da kiyashi a tafiyar, dan an kuma kitso da kwarkwata gurin zaɓen muƙarraban gwamnati, dan akwai sauran ire iren wanda su ka yiwa waccan gwamnati aiki, suka hanata cigaba suka hana ƙasa cigaba.
Amma duk da haka a wannan karon, jami'an tsaro ma su cike da son ganin zaman lafiya ya wanzu a ƙasa, suna cike da farincikin sauye sauyen da aka samu a harkar tsaro, kuma suka sa ran cewar alamu sun nuna ƙarshen harkar ta'addanci a ƙasa yana kusantowa.
Sabon shugaban ƙasar ta bakin me magana da yawunsa, ya fitar da sanarwar cewar babu yafiya ga duk wani wanda aka kama da laifin ta'addanci ko yi wa harkar tsaro zagon ƙasa.
Sannan duk wanda aka kama da laifin mallakar makami ba bisa ƙa'ida ba musanman bindiga, to hukuncinsa ki sa ne, ba tare da wata Shari'a ba.
Haka zalika duk wanda aka samu da fitar da sirrin rundunar tsaro, shi ma ze zama a cikin 'yan ta'adda kuma hukunci ɗaya za su karɓa da 'yan ta'addan.
Se dai an kai ruwa rana akan wannan ƙuduri na gwamnati kan majalissa su amince, kasancewar shugaban ƙasa a tsaye yake, ya sanya shi tsayawa kai da fata akan dokokin, tare da ba da umarnin bincikar duk wani ɗan majalisa da ya soki wannan ƙudurin.
Da yawa cikin marasa gaskiya ya ɗuri ruwa, dan wannan gwamnati da gaske ta ke, irinsu General Ibrahim kuwa, ciki ya ɗuri ruwa gashi akwai yiwuwar ai musu retire, kuma shugaban ƙasa ya kafa kwamiti na musamman, dan bincikar yadda akai da maƙudan kuɗaɗen da aka dinga sawa a harkar tsaro, gwamnatin baya.
Yau ta kama Saturday, da rana bayan su Abra sun dawo daga Tahfiz suna zaune a parlour suna game ita da Salman, Na'ima tana kallon wani program a tv, Khamal kuma yana karanta News paper.
A shagwaɓe ta ɗago fuskarta tana kallon Salman dake ƙunshe dariyarsa, dungurar masa da Game ɗin ta yi ta ce. "Ni dai ban yarda ba wayo kawai kake mun."
Dariyar da yake ƙunshewa ya saki ya ce. "Akan me zan miki wayo, ki yarda kawai na fiki iyawa."
Turo ɗan ƙaramin bakinta ta yi tare da kawar da kanta gefe. Murmurshi ya yi ya ce. "Shikenan mu sake yin wani, ke zaki ci insha Allahu."
"Ba zan yi ba É—in, girki ma zan tafi in É—ora."
"Haba ƴar ƙanwata ki tsaya mu ƙara ɗaya Please, ƙara koya miki nake son yi yanda gobe zaki winning a kaina."
Na'ima dake sauraren su ta harare shi ta ce, "Ka bar ta, ta je yi aikinta, kai tunda ba ka da abun yi sai zama a cikin gida tare da mace sai ka yi ta yi ai." A hankali ta yi maganar yanda Khamal ba zai ji ba, kasancewar ta fi shi kusa da su.
Jiki a sanyaye Abra ta miƙe da niyyar zuwa kitchen.
"Daughter ku shirya ku je ku gaishe da su Mama yanzu."
Muryar Abbinta da ya faɗi haka yasa ta tsayawa cak ƙirjinta ya faru dukan uku_uku, domin ko kaɗan ba ta ƙaunar abun da zai kai ta gidansu Mahaifiyarsu ko gidan wani nata, saboda tsana ƙarara da suke nuna mata.
Salman da shi ma ba son su je yake ba saboda kar a ɓata ran Yayarsa ya ce. "Abbi akwai Islamiyya fa, ƙarfe huɗu za mu koma."
Khalmal ya ce, "Za ku iya zuwa ai ku gaishe su kafin time É—in, tunda yanzu ko 1:30 ba ta yi ba, weekend É—in nan shi kaÉ—ai time É—in da kuke da shi na ziyara, dama suna ta complain ba kwa zuwa sosai." Jiya Mama ta kira Na'ima a waya ta bawa Khamal dan su gaisa, shine bayan sun gaisa É—in cikin kissa take ce masa su Abra ba sa zuwar musu sosai, shi yasa ya ce su je yau su gaishe ta.
"Abbi to ai girki Yaya Abra za ta yi."
"Salman! Gidan namu ne ba ka san ku je ko me? Dan girki idan kun tafi ba sai in yi ba?" Cewar Na'ima cikin haÉ—e rai.
"Allah ya baki haƙuri Mami, ba haka nake nufi ba." Ya yi maganar tare da miƙewa tsaye.
Numfashi Abra ta sauke ta ce. "Bari mu shirya sai mu je yanzu Abbi."
"Yawwa Æ´aÆ´an albarka, Allah ya albarkaci rayuwarku."
"Amin." Suka amsa gaba-É—aya.
Salman yana duban Abra ya ce. "Ki yi sauri ki shirya kar ki tsayar da ni, dan na san hali."
MurguÉ—a masa baki ta yi ba ta ce komai ba ta shige É—aki.