Sashe 21
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"A'a, Lafiya? Me ya faru? Wani abun ne ya samu Khamal ko Salman zaki kira ni a daren nan ki saka mun kuka?"
Aunty Suwaiba ta tambaye ta cikin kid'ima.
Cikin kukan ta ce. "Na shiga uku na lalace Aunty, ta tabbata Abra Æ´ar Khamal ce ta cikinsa, duk abubuwan da ya faÉ—a mun a baya ashe duk k'arya ne, shashasha wadda ba ta san abun da take yi ba kawai ya mayar da ni."
"Ke wa ya faÉ—a miki? Mene hujjar ki na cewa hakan?"
"Wadda ya yiwa cikin ta haifa masa ita ce ta kira ni ta tabbatar mun da zargina."
Kwashe duk yanda suka yi da wadda ta kira ta, da yanda suka yi da Khamal ta yi ta faɗawa Aunty, ta ƙara faɗin. "Ni kam yarinyar nan ta zame mun bala'i da masifa a gidan Aurena, da ina rayuwata da mijina hankali kwance amma yanzu ta shigo duk ta wargaza mana farincikinmu."
"Na rasa yaushe zaki yi hankali Na'ima, shegen kishi ya rufe miki ido kin kasa ganin dai_dai, idan ma ta tabbata mahaifiyar Abran ce ta kira ki sai ki yi masa wannan haukan? Ke sai ka ce ba jinin Mama ba? Yaushe zaki ko yi kissa ne.
"Aunty wannan abun fa ba zancen wata kissa ba ne, ba za ki gane yanda nake ji ba ne a cikin zuciyata, kamar ana rura garwashi haka nake ji, ni yanzu kawai ki faÉ—a mun yanda zan yi Yarinyar nan ta bar gidan nan, dan wallahi ba zan cigaba da zama da ita ba."
Numfashi Aunty Suwaiba ta sauke ta ce. "Na ji zan faɗa miki, amma sai kin mun alƙawari zaki je ki bawa Khamal hak'urin maganganun da kika faffaɗa masa."
"A saboda me zan ba shi hak'uri? Shi fa ya mun laifi, har da mari fa, abun da tunda nake da Khamal bai taɓa mun ba. Ki bar ma wannan maganar, kawai ki faɗa mun yanda zan yi, abun fa bana sanyi ba ne, na ga baki ɗauki abun serious ba, ko dan bake aka yiwa haka ba?"
Ta yi maganar fuskarta na nuna tsantsar ɓacin ran da damuwar da take ciki.
Aunty Suwaiba ta ce. "Ba haka ba ne Na'ima, kin san bayan ke babu wanda ya kai ni baƙin cikin zaman Yarinyar nan a gidanki, amma bana son ki yi abun da zaki zo kina da na sani ne."
"Babu wani da na sanin da zan yi, wallahi sai dai mu rabu da Khamal, matuƙar ya zaɓi cigaba da zaman yarinyar nan a gidan nan, haba abun ya ishe ni haka, hak'urina ya ƙare."
Ta ƙarashe maganar cikin kuka, wani irin kishi na nuƙurƙusar zuciyarta.
Daƙyar Aunty Suwaiba ta rarrashi Na'ima ta yarda za ta je ta bawa Khamal haƙuri, shi ma dan ta ce idan ba ta je ta bashi ba, baza ta faɗa mata yanda za ta yi Abra ta bar gidan cikin sauƙi ba, ba tare da an yi tunanin da saka hannunta ba. Ita kuma Na'ima gani take Aunty Suwaiba ba za ta gane halin da ta ciki ba ne, a ganinta ita aka cuce ta, kuma an hana ta kuka. Aunty Suwaiba ba kuwa tsoron kar Auren Na'ima ya mutu su shiga uku take, dan ita suka dogara ita da sauran ƴan'uwansu. Domin ta fuskanci babu abun da Khamal ba zai iya ba akan Abra.
"Amma fa Aunty daƙyar in zai hak'ura, dan yanda ya hasala ko su Ammi na zaga sai saka."
"Zai hak'ura mana, kamar kin manta halinsa ne, yana da zafi amma kuma yana da sauƙin kai wani lokacin, ki nuna kin damu kin yi nadamar maganganun da kika faɗa masa, duk taurin ransa zai hak'ura. Su Maza suna san ka yi musu laifi ka amsa ka yi, kuma kar ki bari sai gobe, da zafi_zafi ake dukan ƙarfe, ki je yanzu yanda zai gane da gaske kin yi nadamar, in ya so cikin nutsuwa sai ki faɗa masa komai na kiran wayar da aka yi miki."
Numfashi Na'ima ta sauke ba don son ranta ba ta ce. "Shikenan Aunty, zan yi duk yanda kika ce."
"Yawwa, ki fa yin fa, dan na san halinki sai ki amsa ki kuma ƙi yi."
"Zan yi fa da gaske."
"Shikenan, sai mun yi waya da safe, ki kwantar da hankalinki, na miki alƙawarin zaman Shegiyar yarinyar can a gidanki ya zo ƙarshe."
Duk yanda take jin tsananin zafi da k'una da baƙin ciki gami da takaici a cikin ranta, haka ta taushi zuciyarta ta miƙe tana goge hawayen fuskarta bayan sun gama wayar ta nufi ɗakin da Khamal yake.
A hankali ta tura ƙofar ɗakin, ta yi sa'a ƙofar a buɗe take, a zaune ta tarar da shi akan bedside drawer ya riƙe kansa da hannayensa, alamun ransa ya kai ƙololuwar ɓaci. Jin ƙamshinta ya saka shi ɗago kansa da sauri tare da miƙewa yana kallon ta.
Kafin ta ce uffan ya nuna mata ƙofa da hannunsa cikin ɗaga murya ya ce. "Get out!"
Marairaicewa ta yi ta buɗe baki za ta yi magana amma ya ƙi ba ta damar hakan.
"I said get out from this room." Ya faÉ—a a tsawace kyakkyawan idanunsa da suka rine zuwa ja duka a waje.
Jikinta ne ya ɗauki ƙyarma, ba ta yi tunanin ya ɗauki zafi haka ba, tsugunnawa ta yi akan ƙafafuwanta ta fashe da kuka ta ce. "Please My Man listen to me, ka saurari abun da zan faɗa maka."
"Me kuma ya rage baki faɗa mun ba Na'ima? Me zaki ce mun? Duk yanda nake danne zuciyata akan kar mu matsala amma ba kya gani? To tunda haka kika zaɓa mu zuba ni da ke a gidan."
"I'm sorry, dan Allah ka saurare Ni, wallahi na yi nadamar maganganun da na faɗa maka, amma ka mun uzuri raina ne a matuƙar ɓace a lokacin."
Numfashi ya sauke ganin yanda take kuka sosai sai zuciyarsa ta fara karyewa, ya yi tunanin da gaske ta yi nadamar ne har cikin zuciyarta.
Fuska a É—aure ya ce. "Ba na son jin komai daga gare ki a yanzu, maganganun da kika faÉ—a mun É—azu ma sun ishe ni."
Wani yawu ta haÉ—iye mai É—aci ta shiga girgiza masa kai.
"Dan Allah Khamal ka saurare ni ka ji bayanin da zan yi maka."
Zama ya yi a gefen gado ya ce. "Ina jin ki."
Ajiyar zuciya ta sauke ta bashi labarin kiran wayar da aka yi mata. Kallon ta kawai yake har ta miƙo masa wayarta tana nuna masa kiran da aka yi mata da Private Number. Karɓa ya yi ya duba amma bai ce komai ba, ita ma ba ta ce komai ba sai idanu da ta zuba masa, imagine kawai take yi a cikin ranta ƙaramin yaƙin da za'a yi idan ya amsa laifinsa.
"Ba zance k'arya kike yi ba, amma gaskiya ban yarda da wannan abun ba, babu wanda zai kira ki ya faÉ—a miki haka, because ban da Family na da naki da wasu daga cikin abokan aikina, babu wanda ya san ta yanda muka samu Abra da matsayinta a gidan nan."
Wani malolon baƙin ciki ne ya ƙara cika zuciyarta, wato ma maƙaryaciya ya mayar da ita? Ita ta shirya hakan nufinsa ko kuma cigaba da raina mata hankalin da yake yi tun lokacin da ya kawo Abra zai yi? Ji take kamar ta tsinka masa mari dan baƙin ciki, amma dai ta daure ta yi kalar tausayi ta ce. "Wallahi da gaske nake, akan me zan ƙirƙiri wannan abun? Kar ka manta tun lokacin kawo Abra gidan nan na yiwa abun mummunar fahimta har muka samu saɓani ban ƙara tayar da hankalina ba, na cigaba da rainon ta cikin kulawa da zuciya ɗaya, to me zai saka yanzu kuma in yi haka?"
"Duk da haka, amma ko da hakan ne, daga kiran ki an faɗa miki wannan maganar sai ki zo ki dinga jifa na da waɗannan miyagun kalaman? Why Na'ima? Idan rai ya ɓaci sai kuma hankali ya gushe?"
Shiru ta yi ba ta ce komai ba, cigaba da magana ya yi idanunsa a cikin nata.
"Baki yarda da kanki ba, ba kuma ki yarda da ikon Allah ba, da kin yarda da baza ki dinga wannan abubuwan kamar wata illiteracy ba, ki saka a ranki Ubangiji ne ke yin komai, kuma shi ya nufa sai Abra ta yi rayuwa a gidanmu. Sannan kuma k'arya fure take ba ta ƴaƴa, ki saka a ranta komai daren dad'ewa gaskiya za ta bayyana, idan ma ƙarya nake miki Ubangiji ba zai barni ba, dole watarana sai ya toni asirina."
Na'ima ta kwantar da kanta ta dinga nuna masa ta yi nadama, sharrin shaiɗan ne da kuma tsananin kishin sa da take yi, amma Insha Allahu haka baza ta kuma faruwa. Ganin yanda take kuka da kalar tausayin da ta yi yasa Khamal ya janyo ta jikinsa ya ce. "Shikenan Wifey komai ya wuce, amma kar ki ƙara mun irin haka, ban ji daɗi ba, raina ya ɓaci sosai, yanzu fa ba da ba ne, mun girma mun zama iyaye, ya kamata irin wannan abubuwan duk mu daina su."
"Insha Allahu bazan kuma ba."
Ta yi maganar cikin sanyi tana ƙare shigewa jikinsa kamar ba Uwar ɗan saurayi Salman ba.
Bayanta ya shafa ya ce. "Allah yasa, bana son muna samun saɓani, musamman akan Abra, dan watarana yaran nan za su iya ji su gane halin da ake ciki. Ke Mace ce mai daraja a idona, ko dan yanda kika riƙe mun Abra da amana ba zan so wani abu na ba dai-dai ya shiga tsakaninmu ba."
Ƙwafa ta yi a cikin ranta tsanar Abra na ƙara cika mata zuciya, wato saboda ita ne ma yake ragwanta mata? Lallai dole ta san abun yi, dan gaba zai iya cewa ma saboda Abran yake zaune da ita. A fili kuwa murmurshin yaƙe ta yi ta ce. "Na gode Mijina, Abra kuma she is my Daughter, ka daina danganta ni da mariƙiya a gare ta, ni mahaifiya ce a gurinta, dan kallo ɗaya nake yi musu ita da Salman, matsayinsu ɗaya a cikin raina."
Murmurshi ya yi yana jin ɓacin ransa fiye da rabi ya tafi.