← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 145

Sashe 43

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yace "Well, gaskiya Yakamata ku dinga kulawa, iyayenku karatu suka turoku, irin wannan rayuwar ba in da zata kai ku, mussaman kasancewar ku mata, Aure ko karatu shine ya dace da ku, duk abunda Namiji zai yi ado ne, yanzu Gashi nan su suna can hankalin su a kwance, ku kuma kuna wahala, ai haka ba daÉ—i" su kayi shiru kamar gaske.

Yace "dubu ɗari ne kowacce, amma saboda wannan ƙawartaku patient ɗin gidan nan ce, ku bada 80k each of you".

"Masha Allah, mun gode sosai doctor, Allah ya saka da alheri".

Yace "Bakomai Allah ya kiyaye gaba,idan a shirye kuke, kuje ku biya kuÉ—in, za'ai aikin yanzu insha Allah" su kai tayi masa godiya, sannan suka bar Office É—in.

Suna fita É—ayar tace "Beb amma doctor nan É—an rainin hankali ne, shi ba aikin zunubin ze yi ba, amma yake mana nasiha ya fara yiwa kansa mana"

"Ke, nifa hankalina a tashe yake Wallahi, kar inje wani abun ya faru, tsoro nake ji". Cewar É—aya daga cikin su.

Wadda ta yi musu rakiyar ta kwaɓe baki tace "kina jin tsoro, amma kin iya kwanciya da namiji, mu biya kuɗi a cire cikin, mu koma in ci uban gayen nan, dan daga nan Abuja zan wuce, dan baze tonan Asiri ba, sai ya biya kuɗin aikin nan da zan biya, tijara zamu yi masa, kuma kar ki mana wannan sakacin naki Ke Ihsan, ki buɗe baki ki tatse shi".

Wadda aka kira da Ihsan tace "Baby to ta yaya?".

Baby tace "Au tambayata ma kike? Waye be sanshi a ƙasar nan ba, babban sojane da ƙasa take ji da shi, idan ya musa biyan kuɗin, vidoen tsiraicinsa zakiyi mana, mu saka a YouTube wallahi"

Jannah ta kwashe da dariya tace "kai Baby baki da dama".

Ihsan kamar za tayi kuka tace "Baby soja ne fa, idan ya harbeni fa?".

Baby tace "Sojan me? Ina ruwan wani da aikinsa? Ya san sojan ne amma yayi iskanci, Wallahi kika ƙyaleshi, ya cuceki a banza"

Da wannan hirarrakin nasu, suka ƙarasa reception dan biyan kuɗin.

Nurse Jamila ce ta koma ofishin MD, hannunta riƙe da file, ta shigo Office ɗin, taje gaban teburin Bulama tace "doctor ga file ɗin nasa, an yi masa gwajin sakamakon yana ciki".

Ya karɓa ya duba sannan yace "Ki turomin 'yan uwan patient ɗin"
Ta amsa da to, sannan ta fita suka dawo tare da wasu maza guda biyu.

Suka sake gaisawa sannan yace "yawwa duba da yadda mara lafiyan ya rasa jini sosai, akwai buƙatar mu ƙara masa jini, kamar leda uku haka, kuma muna buƙatar jinin da gaggawa kar ya rasa ransa".

Sai da mamaki ya kama 'yan uwan nasa, ganin mara lafiyan nasu yana hayyacinsa, kuma ana ta hira da shi, amma ance wai sai an ƙara masa jini, kar ya rasa ransa, amma suka ɓoye manakin nasu, duba da aikinsa me ba nasu ba, ɗaya yace "to nawa ne jinin?"

Bulama yace "eh to, duba da yadda kuka kashe kuÉ—aÉ—e sosai, zakuje lap a duba wanda jininsa zai yi, a É—iba a saka masa, zaku biya dubu Arba'in, idan muma ba'a samu wanda jininsa yayi ba, zaku biya dubu saba'in, jini leda uku".

Ɗayan yace "doctor babu ragi, naga baku karɓe mu bama, sai da muka ajiye dubu hamsin?".

Bulama yace "Amma da bamu karɓeku ba kamar yadda Asibitin gwamnati sukayi, ai da wani zancen ake ba wannan ba, nan fa ba Asibitin gwamnati bane".

ÆŠayan yace "shikenan, bari muje mu biya".

Bayan fitarsu, cikin damuwa Nurse Jamila tace "doctor, PCV ɗinsa fa 31%, meye amfanin jinin da za'a ƙara masa?"

"Jamila ban hanaki yi mini shishshigi a aikina ba? Shekarata nawa ina aiki? Dan kinyi Nursing shekara uku shine zaki dinga min shishshigi a aikina, banda ina duba wani abu, da tuni na salamemeki, get out from my sight" yayi Maganar yana nuna mata hanyar fita.
Tabbas Jamila akwai aiki, kamar jaka sam bata da son jiki, aiki take tsakani da Allah, yana jin daɗin aikin da ita, shikuma yana kyautata mata, dan Bulama akwai kyauta, mussaman ga ma'aikatansa masu ƙwazo, idan ya bushi iska, sai yasa a dire katan-katan na taliya da makaroni a raba musu, ko haka nan tsakiyar wata ya bisu me dubu ɗaya mai ɗari biyar ya raba musu, shiyasa ya samu masu goyon bayansa a harƙallar da yake a Asibitin nasa, kuma Asirinsa yake a rufe.

Sai ƙarfe biyu sannan su Abra suka samu sukunin fitowa daga lectures, dan yin salla suci Abinci, su koma ta 2_4.
A gajiye take sosai, sam Abra ba ta son takura, ita da Khairy suka fito, suka tafi masallaci dan yin salla.
Bayan sun idar Khairy tace "Abra muje Cafeteria mu samu Abunda zamu muci".

Abra tace "A'a ni ba zani ba"

"Me yasa, ba kya jin yunwa ne?"

"Zuwa zan in jira Faris, idan ya fito daga lectures maje muci Abincin"

Khairy tace "Ikon Allah, ko kashin awaki kuka fito da Faris É—in nan, wataran zaki Aure ku rabu, ai se kije ki tayi me É—an uwa, nikam na tafi cin abinci bana iya ba".

Abra gyara zaman facemask ɗinta tayi, ta miƙe tare da ɗaukar jakarta ta nufi hanyar barin masallacin.

Wani guri ta samu can nesa da É—alibai, ta zauna ta cire mask É—in fuskarta, ta É—akko wayarta tana trying lambar Faris.

Jikinta ne ya bata ana kallonta, lokaci ɗaya kuma wani irin ƙamshi ya mamaye ilahirin gurin nan, duk da ba ta samu ɗaga kai taga waye ba, amma wani irin tsoro ya shigeta, a jikinta taji cewar kowaye yake ƙamshin nan ma'abocin kwarjini ne.

Ba ta gama tunanin ba taji mutum ya zauna a kusa da ita, a razane ta fara bin ƙafafuwansa da kallo, sai dai ta kasa ɗaga kai ta kalli waye.

Kamar an masa dole yace "Abra Khamal Khamis"

Dam ƙirjinta ya buga, jin yadda ya ambaci sunanta, bata san lokacin da ta buɗe manyan idanunta, ta kalleshi ba, sai dai kallon nasa ya sake jefata cikin wani rikitaccen al'amari da ita kanta ta kasa gane wane irin yanayi ne haka?.

"Is that not your name?" (Ba sunanki bane?) Ya tambayeta.

Sunkuyar da kai tayi, ta ƙi yi masa Magana.

"Are You deaf?" (Ke kurma ce?)

Da sauri ta jinjina masa kai alamar eh.

Yace "And how do you heard what I said this time?" (Ya akayi ki ka ji abunda nace, a wannan karon?)

"Am using aid to hear" ta faÉ—i Maganar ba tare da ta shirya ba.

Jin maganar ta ta yayi, tamkar rainin hankali, amma ya basar yace "Yaushe kuka fara lectures?" Ji tayi gaba É—aya ya takura mata, ita ba ta sani ba malami ne ko É—alibi, to yama za'yi malami ya zo ya sakata a gaba haka.

Wayartace ta fara ringing, tayi sari ta É—aga ta kara a kunneta tace "Hello Faris".

"Angel kina ina ne? Na zo department É—inku ban ganki ba, ko kinje cin abinci ne?".

Tace "Aa banje ba, dama kai nake jira, bari yanzu zaka ganni" ta ƙarasa Maganar tare da miƙewa tsaye, Caraf ya sa hannu ya riƙo hannun Abra, wanda ya koma ɗan ƙarami a cikin nasa hannun, sai laushi hannun nata tamkar ya riƙe audiga.

Zare ido tayi, tana bin hannunta dake cikin nasa da kallo, take hawaye ya taru a idonta tace "ka cika mini hannu na".

Sai da ya ƙurawa kyakywar fuskarta ido sannan yace "Ina miki magana zaki tashi ki tafi?"

Da ƙyar ta iya cewa "Brother na ne yake jirana, zanje muci Abinci".

"Saurayinki dai ko?" Yayi Maganar ba tare da ya saki hannunta ba.

Tayi sarin girgiza kai tace "A'a ni bani da surayi, ƙanina ne".

Kallon Abra yake, tare da jinjina rainin hankali irin na Abra, wai duk wannan kyan nata take ce masa bata da saurayi, dan ta raina masa hankali.

Hannunsa ɗaya ya sanya a cikin aljihunsa, ya ciro ID card ɗinta, ya danƙa mata a hannunta.

ÆŠan buÉ—e idanunta ta kuma yi, tan juya ID card É—in ta kalleshi, amm ta kasa ce masa ta gode.

Wayarta ce ta sake ɗaukar ruri, tana ɗaga wayar cikin shagwaɓa tace "Faris, gani nan yi haƙuri"

Ta katse kiran, ta kalli Adnan tare da ƙoƙarin zame hannunta daga nasa, amma yaƙi sakin hannun, sai ƙara riƙe shi da yayi gam.

"Dan Allah ka sakar mini hannuna, jirana ake".

"Baki iya godiya bane?".

"Yi haƙuri nagode" a hankali ya sakar mata hannu, cikin hanzari ta bar gurin ko waiwayawa baya ba ta yi.

A ƙofar ajinsu ta tarar da Salman, aikuwa tana zuwa ya fara mita "Wai ina kika je ne haka?"

A É—an dirirce tace "Can gurin naje karatu, mu tafi kawai"

Ya É—an dubeta yace "meye wannan a hannunki?"

Ta duba hannunnata tace "ID card É—ina ne"

Yace "Hmm, a ina kika ganshi?"

"Wani ne ya tsinta shine ya kawomin"

Tsuke fuska Salman yayi yace "Wani kuma?"

Tace "eh"

Ya yi tsaki yace "wataƙila ma zama yayi yaita kallon hotonki da yake jiki".

Murmushi tayi tace "Faris Allah ya shiryeka"

Ƙara tsuke fuska yayi yace "Ki mai da mask ɗinki, har an fara binki da kallo".

Ta sa hannu ta ja mask É—in, ta rufe fuskarta sosai tace "Shikenan?"

"Muje" yai maganar cikin bada umarni.

Adnan kuwa yana nesa da su Abra kaɗan, yana hangota ita da Salman, kallonsu yake sosai yana ƙoƙarin tabattar da abunda Abra ta gaya masa na cewar Salman Brother ɗin ta ne.

Salman ma dai Fari ne sosai, sai dai babu ta in da suka haÉ—a kamanni da Salman É—in, kamanninsa daban nata daban.

A hankali ya juya, ya bar department É—in gaba É—aya.

Hajiya Na'ima ce ta shiga sashen Abbin Abra, ta tarar da shi yana ta shiri, ta kalleshi tace "Yallaɓai ya naga haka? Jiya fa ka dawo kuma na ga kana haɗa kaya, ina zaka kuma?"

Ba tare da ya kalleta ba ya cigaba da haɗa kayan yace "lamarine na gaggawa, akwai buƙatar inje Abuja a yau ɗin nan"

Tace "Amma meyasa?".

"Sojojin da ake bincike akansu ne, wai sunci guba sun mutu".

Tace "ta yaya? Waye ya basu gubar?"
Chapter 43 · 0% Book details