← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 145

Sashe 60

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tana faɗin hakan ta fice daga ɗakin tare da banko masa ƙofa, Salman ji yayi wani zazzaɓi na neman kama shi ga wani ciwon kai dake neman tarwatsa masa ƙwaƙwalwarsa.
Sama da marwa kawai yake a cikin haÉ—aÉ—É—an bedroom É—in nasa, tunanin mafita yake amma ya gagara samu gaba É—aya. "What should I do? Ko na faÉ—awa Granny nasan she most do something" zubewa ya yi a kan gadon, ya na dafe kansa.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Hasbunallahu! Ubangiji ka kawo mafita" shiru ya yi yana tunani a fili ya sake ce wa "If na gayawa mayen na Abra gasky tare da faÉ—a masa ina son ta, nine kuma zan aureta fa?" Girgiza kai ya yi yana sauke numfashi ya ce.
"Mami zata tsine min, she's my mother ban son hakan ya kasance"  ganin ya rasa mafita ya ɗauki wayarsa tare da ƙorawa photon Abra kallo, Murmushin da ke shimfiɗe akan fuskar ta shi kaɗai ya isa ya sanya ya samu nutsuwa.
Kwanciya ya yi yana ƙanƙame wayarsa a ƙirjinsa kamar da wasa kuma zazzaɓi ya rufesa tare da ciwon kai mai zafi.

Mami na fita ta kira Anty Suwaiba a waya cikin damuwa ta ce "Ni yaron nan ke son tonawa asiri Anuty Suwaiba?. Babbar matsalar da ya faɗi komai Uban sa sakina zai yi, bana son hakan ta kasance gaba ɗaya na rasa yadda, al'amarin na son fin ƙarfina"
Anuty Suwaiba ta cikin wayar ta saki dariya sai da tayi mai isarta kafin ta ce "akwai shawara, ki bawa mahaifin nasa shawara a kan ya fitar da shi ƙasar waje karatu tun da Abra aure za tai, kuma kina da tabbacin ba zai mai da hankali ya yi karatun da ake buƙatar ya yi ba, idan ya so yana can sai ayi mata Auren idan ya dawo dai duk jarabarsa ta zama matar wani"

Jinjina kai Mami ta yi cike da gamsuwa kafin ta ce "shawara mai kyau, ban yi tunanin hakan ba shi ya sa nake son kawo maki damuwata thank you Anty" tattaunawa suka sakeyi a kan lamarin.

Washe gari da safe bayan Abbi ya yi breakfast, Hajiya Na'ima ta je masa da maganar ta inda ya shiga bata ban yake fita ba, kamar ya ari baki saboda masifa.
"Ban san me kike nufi dani ba, ban san kuma abinda ya ke kan ki ba Na'ima, karatun Salman kuma yanzu ki ke son lalatawa, shirme da haukan na ki har akan ɗan da kika haifa na gaji na gaji" fuuuu! Ya yi waje rai ɓace.

Cikin tashin hankali Mami ta kira Anty Suwaiba "wallahi ba zai yarda ba Anty yanzu yaya zan yi? Ya fara ɗaukar zafi, dama a ƙule yake dani na haɗa shi da mahaifiyarsa"
Anty Suwaiba ta ce "kwantar da hankalin ki, ki shirya akwai mafita, gurin malami zamu kai shi, a rufe masa baki, dolensa ya amine Salman ya bar ƙasar nan" shirya komai suka yi, Na'ima ta amince akan zasu wajan wani malami, saboda samun mafita, kar ramin muguntar da take shiryawa ya rufta da ita.

Kamar yadda Abbi ya yi alƙawari, haka ya cika ta hanyar yin bincike har Kaduna, akan Sp Adnan Aliyu Matawalle, ya samu good Information. Halin Adnan mai kyau ne, kuma mutum ne mai asali, mahaifinsa sanannane ne.

A satin Abbi ya nemi ya zauna da Adnan, shi kansa Abbi ya yaba da hankali nutsuwa, da kuma kamala ta Adnan, dan haka ya bashi damar ya turo magabatansa, su nema masa Auren Abra.
Ko da Adnan yaje da wannan batu gida, farinciki gurin iyayensa ba'a magana, mussaman Hajiya Mama, bata taɓa tunanin abubuwa za su zo da sauƙi haka ba, saboda gani take Adnan ba zai iya kwantar da kai yayi Soyayya ba, saboda tsananin zafin zuciyar sa.
Sosai Mama da Abba suka yaba da Abra, da ya nuna musu hotonta, kuma suka yi duk binciken da za suyi a kanta, amma ba su samu wani mummunan abu ba akanta, mussaman da ya zamana Major Khamal Khamis, sunansa shahararre ne a ƙasa.

Abban Adnan ya wakilta 'yan uwansa, zuwa nemawa Adnan É—in Auren Abra, kuma, Abbi ya basu auren cikin aminci, farin ciki wajan Mami ba'a magana, gani take ta samu mafita da kaso mai rinjaye na matsalolinta.
gefe guda a ranar Sp Adnan Aliyu Matawalle da Abra Khamal Khamis raya daren sukai da Soyayyar juna ta waya.
Sp Adnan ya koyar da Abra Soyayya, ita kanta wasu lokutan har mamakin kanta take, saboda irin soyayyar da take nuna masa. Duk zafin zuciyarsa, ya ƙware a fannin iya rarrashi da tarairayar Abran, da biyewa dukkanin shagwaɓarta da shirmenta. Haka suka raba dare, Adnan yana tsara musu yadda zasu gina rayuwarsu, bayan sun yi Aure, har sai da ya kusa fara sakin layi, Abra tayi masa sallama ta kashe wayar.

A hankali ta tura ƙofar ɗakin yana kwance ya juyawa ƙofar baya babu abun da yake bayyane a jikinsa sai fuskarsa, gaba ɗaya jikinsa rawar zazzaɓi yake. Da ɗan sauri Abra ta ƙaraso tare da zama a bakin gadon daidai kansa muryarta na rawa ta ce.
"Subuhanallahi Faris baka da lafiya? Wayyo Allah na"
gaba É—aya idanunta ya cicciko da hawaye. Wata irin soyayya ce tsakanin Abra da Salman irin soyayyar da Ubangiji ne kawai ke haÉ—ata, raba irin wannan soyayya kan iya jawo rasa rai ko rayuka.

Juyawa ya yi tare da Kallonta da idanunsa wanda sukai jaa sosai tamkar gauta. Kallon ta ya ke kamar bai taɓa ganinta ba a hankali ya kama hannunta tare da riƙewa cikin nasa.
Abra ta ƙara hawa kan gadon tare da shafa sumar kansa muryarta na rawa ta ce.
"Meke damunka Faris É—i na? bari na faÉ—a wa Mami, Abbi ya riga ya tafi, ya tambayi kana ina Mami ta ce ka fita"
Girgiza mata kai ya yi, yana ƙara matse hannunta da ke cikin nasa.

"Bari na kira Dr ya duba ka" Murmushi ya sakar mata cikin dauriya ya ce.
"Mami, Abbi, Dr. Basu da maganin abin da yake damuna Angel leave them"

"Jikin ka yayi zafi fa, ta yaya ka ke tunanin zan jure ganinka haka?"

"Zaki jure mana Angel? tunda gashi aure zaki ki barni" yayi Maganar a raunane.

Shiru tai ta kasa cewa komai domin ita ma tana hango ranar da za'a ce wai zata bar gidan kuma tabar Faris É—inta?.

"Yanzu me ka ke so?"
"I  just need you by my side, stay with me Angel don Allah".

Kansa ta É—auka tare da É—orawa akan cinyarta a hankali take shafa sumar kansa hawaye na saukar mata ta ce.
"I'm here I'll Spend all my time with you Faris".
Lamo ya yi akan cinyarta yana murza hannunta zuciyar sa sai bugawa take.

"I love You. I love you Angel" Murmushi tayi tana jan hancinsa ta ce.
"I know, and I love you too u don't have to  worry bloody..."

Shiru duk sukai ga mamakin Salman, numfashin Abra yaji yana sauka a hankali, alamar bacci ya ɗauke ta, gently ya miƙe da ga kan cinyarta.

"Angel ragowar yarinya, dana aureki kin daina wahala Insha Allah, da yardar Ubangiji ke matata ce mallakina ce"

A hankali ya sumbaci goshinta ya ce "you're my life"
Gently ya yi 6nata nose Kiss ya ce "My everything" a nuste ya yi mata cheeks kiss ya ce "rest of my life. Mother of my children" ji yake kamar ya maida ita cikinsa, kowama ya dena ganinga.

Wayar Abra ce ta fara ringing kallon screen ɗin wayar ya yi yaga _Heartbeat_  kallon wayar ya yi har kiran ya katse. Sai da akai kira uku a fusace ya ɗauka.

"Ruhin Sp Adnan Aliyu Matawalle. Na kusa mutuwa da rashin jin muryarki"
Adnan dake tsaka da driving gefensa kuma Usman ne yana ta tsokanar sa. Jin shiru Adnan ya ce.
"Hello Angel are you there?"

"She's sleeping in my laps u can call later" Salman ya faÉ—i maganar hankali kwance.
"Who are you? And  a ina take bacci?" Adnan ya furta rai ɓace.

"Tana wajan wanda ya dace mana? Ka faɗi yaren da kake ji, idan baka gane wanda nayi ba, sai nayi maka bayani da shi" sai yanzu Adnan ya ɗauki murya murmushi ya yi yace "Oh! Faris ƙaninmu how are you? I'll call later bye"

Yana faÉ—in hakan ya kashe wayar, Salman datse lip's É—insa ya yi yana jin duniyar na juya masa. Ranar da ya fara arba da Adnan a gidan ya zo gurin Abra, ji yayi tamkar ya haÉ—iyi zuciya ya mutu.
Shi kansa Adnan ya lura da irin mugun kallon da yaron yake masa idan ya zo, amma bai É—auki hakan a matsayin komai ba.
Gyara mata kwanciya Salman ya yi yana zame mata rolling É—in kanta.

An saka ranar bikin Abra wata biyu kacal. A satin kuma Adnan ya sauka Kano, ko da suka haÉ—u da Salman kamar haÉ—uwar zaki da damusa haka ta kasance, saboda Salman ji ya dinga yi tamkar ya kashe Adnan ya huta.

Haka ya shiga ɗakinsa, ya kulle kansa ya dinga kuka kamar ƙaramin yaro.
"Abra is leaving me, why? Abbina kaima ba ka fuskanci halin da nake ciki ba? Na kamu da soyayyar yarinyar da ka tsinta ka riƙe tsawon shekaru, a matsayin yayata, Abbi I love her, meyasa zaka bawa wani?" Haka ya dinga surutai tamkar yana gaban Abbi.
Chapter 60 · 0% Book details