← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 145

Sashe 95

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau ya kama Weekend ne cikin jerin watannin da Abra tayi a gidan Adnan a satin ƙarshen watan da zai sanya ta cika wata biyar cif a gidan aurenta. Amma duk tsayin kwanaki da kuma satittika zuwa watannin data riska babu wata rana data zame mata ranar farin ciki, tun ranar da aka kawota gidansa matsayin Amarya har zuwa Yanzu da take cika wata biyar dayin aure. A hankali ta ɗora hannunta a saman cikinta wanda ya fara girma sosai kasancewar ta mara jiki yasa cikin fitowa ya zauna das ƙasan mararta ya ƙara mata kyau na jiki. Amma tana nan yadda take a rame tai duhu sosai kamar ba ita ba. Fararen idanunta da suke a buɗe ta lumshe a karo na farko taji soyayyar abin da yake cikinta ya ratsa Zuciyarta. Musamman yanzu da take jin gilmawar abin da ke cikin nata, tabbacin yana cikin lafiya. "Banso aka samar dakai ta wannan hanyar ba, nasan ba zaka jure ganin wacce ta haifeka cikin uƙubar mahaifinka ba, amma zan tabbatar da cewa ba kayi masa kallon uba ba, zan shaida maka irin wahala da azabtarwar da mahaifinka ya yi mini, tun bayan rabuwata da Salman nake jin kamar na rabu da dukkan wani farin cikina. Amma yanzu sabuwarka cikin mahaifa ya sa naji na samu wani abokin rayuwar wanda zai maye gurbin Salman a zuciyata" hawayen da take ta ɓoyewa ne suka sakko mata cikin sauri ta goge ta ce. "why should i cry? Cry for no reason nayi Al'ƙawarin ba zan sake zubar da hawaye akan azabtarwar da Adnan ke min ba, zanyi hawaye na dalilin rashin sanin asalina da tushena" kukan da yaci ƙarfinta ne yasa ta kasa faɗin sauran maganar wanda kamar suke fitar da kansu bata shirya faɗar su ba.

Mai aikin Hajiya Mama ce ta fito daga kitchen tare da kallon Abra ta ce "Hajiya ƙarama an gama lunch ɗin, na kawo maki nan?" Girgiza kai Abra tayi cikin sakin fuska bayan ta share hawayen idanunta ta ce. "Bana jin zanci abincin nan Laure, kawai ki zuba yadda zai maki kici sannu da ƙoƙari"
"Ko babu yawa ya dace ace kinci sbd abin da yake cikinki ya samu kyakkyawar kulawa" Abra ta kalli mai aikin cikin tunani sai kuma ta ce "Shin abin da yake cikina zai samu illane game da rashin cin abincin nawa?" Da sauri mai aikin ta ce "Sosai, domin sai Kinci shima sai samu wanda zaici, rashin cin babbar illa ne zaki iya haifar babyn babu girma ko kuzari". Murmushi kawai Abra tayi ta ce "Ok thank you" "na kawo maki ko kaɗan ne?" Abra ta girgiza kai ta ce "ba zan iya ci ba Laure, ni bana jin wata yunwa" daga baƙin ƙofa suka ji ance "Idan kin gama aikinki jeki kawai" Laure ta juya ta kalli Adnan jiki na rawa ta gaida shi bai kula ba, da sauri ta nufi sashin da aka bata.
Rufe idanu Abra tayi kamar mai bacci, a hankali Adnan yake binta da idanu yana mmkin lalacewar da take a kullum, ba ƙima, hasken ya dishe sai ƙirji kamar zai fasa riga ga kuma yadda cikin ya sake fitowa fili. Taɓe bakinsa ya yi irin ko a jikinsa ɗin nan kafin ya nufi kitchen babu jimawa ya dawo ɗauke da plate na abinci dambu ne, wanda ya sha kayan lambu da kuma zallar hatta yaji gyaɗa da zogala sai ƙamshi yake. Zama ya yi very close to her yana kame iyayen tare da faɗin "zaki iya zama da yunwa until unborn ɗina ya samu abincin, dan haka get ready zanyi feedings babyna"

Ɗauke fuska tayi tare da ƙoƙarin Miƙewa zata bar wajan, amma gaba ɗaya jikinta ya saki sosai take jin ciwon jiki da wani zazzaɓi na cikin ƙashi. Hannunta ya kama yana mayar da ita zaune kafin ya ce.
"Kina tacin albarkacin abin da yake cikinki, shine dalilin da yasa nake raga maki,amma ke baki ganin hakan ko? Nidai duk abin da ya sameki matsalarki ce kawai ki tabbatar jinina lafiya yake"
Bata kulasa ba, ko fuskarsa bata ƙaunar gani nesa take da dukkan abin da zai sanya tai masa mgn ko yai mata. "Dole kici abincin nan Abra" a ɗan fusace ta ce "to ana dole ne? Don girman Allah dan darajar iyayenka ka rabu dani, stay away from me don Allah" ta faɗa tana runtse idanunta sbd kissing bakinta da taji ya yi a hankali. Plate ɗin abincin ya ajjiye a gefe tare da jawota jikinsa hannunsa ya ɗora akan cikinta yana lumshe idanunsa.
"Kina cewa kin tsaneni, bayan so na da kike yasa idanunki ya rufe kika kasa fahimtar son da Salman yake maki, hakan na nufin duk wata ƙiyayya da zaki nuna min iya baki ne bai kai zuciya ba Angel" harara ta watsa masa ta ce.
"Na soka a lokacin da nake tunanin zaka zame farin ciki, abokin rayuwa, zaka zama mai tausayi a gareni, da bani garkuwa, na soka a lokacin da nake ganin kyawawan halaye a tattare dakai. Amma wallahi wallahi Allah babu sonka a zuciyata, ban taɓa tsanar wani ba, ban taɓa jin akwai wani rai da zanji bana son ganin ko fuskarsa ba irin kai. Sp Adnan Aliyu Matawalle! Abra Khamal Khamis hate you. I hate you na tsaneka wallahi bana ƙaunar ganinka, zakai ladama, zakai dana sani ka rubuta ka Ajjiye zakai kuka da idanunka"
Tana faɗin hakan ta miƙe tsaye jiki babu ƙauri ta nufi hanyar part ɗin ta. Cikin zafin nama Adnan ya sha gabanta ya ce "Ke har kin isa ki furta kalmar tsana a gareni? Wallahi ƙarya kike kina sona, kuka? Ko mugun azzalumi Ubanki mai zuciyar fir'auna bai sanya na zubar da hawaye ba, balle abin da ya haifa. Ki rubuta kema ki ajjiye a duk sanda nai kuka sbd ke a ranar wallahi zan daina duk wata mugunta da nayi miki, a lokacin zan fita daga sabgarki a lokacin zan zubar da makaman ɗaukan fansa na" Murmushi kawai tayi tana mmkin muguwar zuciya irinta Adnan a hankali tana jan numfashi ta ce. "Ta ina zan san kayi kukan? Abin zai zo maka ta hanyar da bakai tsammani ba, ka tsammaci abin da baka tsammani shi ne kawai" tana faɗin hakan tai ɗakin ta. Ya daɗe tsaye yana tunani ya kasa fahimtar komai.

Har dare Abra bata fito ba, Adnan bai je inda take ba, balle yasan halin da take ciki, taci ko bata ci no one's know. A gefe guda kuma soyayyar abin da ke cikin Abra take da masa mugun kamu. Misalin 12 na dare tana kwance nannaɗe cikin duvet hannunta kuma ɗaya riƙe da azkar amma ko iya karantawa ba tai ba, ta dai riƙe kawai a wajanta ne. Tsaye ya yi a kanta cikin ko in kula ya ce "Madam nazo amsar haƙƙina ne" Shiru tai masa ganin tai shiru yasa shi faɗin "Ko ba zaki ban bane?" Idanunta ta buɗe tare da kallonsa cikin sanyin murya ta ce "Kaji nai mgn Bisimillah, ba zan taɓa hanaka ba" tana faɗin hakan ta ja bakinta tai shiru. Zama ya yi akan gadon yana kallonta sai bai lura da yadda jikinta ke rawar sanyi ba, a haka yaje gareta tare da sauke buƙatarsa da maitarsa. Nan kwance ya barta tana sauke numfashi, baƙin cikin yadda take sake masa jiki sai dai yai komai da kansa shi ke cika masa zuciya a kullum. Yana fita Abra ta ƙanƙame jikinta da shiga addu'ar neman sauƙi wajan Ubangiji. A fili kuma ta fara addu'ar yaye damuwa da ƙunci.

*”لا إلهَ إلَّا أنتَ سبحانَك إنِّي كنتُ من الظالمينَ”*
Daga wannan addu'ar ta koma wannan.
*{اللهُمَّ رحمتَكَ أرجُو ، فلَا تكلْنِي إلى نفسِي طرْفَةَ عيْنٍ ، و أصلِحْ لِي شأنِي كلَّهُ ، لا إلهَ إلَّا أنتَ}*
Haka ta dinga yi da ƙarfin da rage mata har barci ya ɗauke ta bakinta na motsawa.

A hankali Meenal ke fitowa daga cikin part ɗinta zuwa Main Parlour, ganin babu kuwa yasa da sauri ta bar parlourn tai waje, jikinta na rawa ta shiga motarta gatekeeper ya buɗe mata gate tabar gidan cikin 160, na giyyar motarta. Sai da tayi nisa taja tsaki ta ce. "Haba aita takura mutum ana saka masa Idanu, duniyar nan kowa abinda yaga dama yake, amma an tirkeni kamar wata saniyyar ɗaure, daga nan sai club wallahi" number Abdul ta kira ta ce "Hy sweetheart, jiya na kwana da mafarkin madararka" shiru tai tana dry ta ce "Haba never nai maka sambatu sai dai kai, now tell me kana ina?" Jim tai ta ce "Oops hotel ɗin ranar nan? Kai kam kamar mara gsky, shikenan bani 10mnts I'll be there" kashe wayar tayi babu jimawa ta Ƙarasa kai tsaye room ɗin daya kama ta shiga. Knocking ƙofar ta fara, da sauri Abdul ya miƙe yana kallon Zee baby dake kwance a kan gadon ya ce "Hehhhh beb Meenal ta ƙaraso tashi ki ɓoye" taɓe baki tayi ta ce "Wai kai ina ruwana da wata Meenal" "No Beb, kin san bana son abin da zai dameki ke nake so kuma ke zan aura waccar ƴar wahala ce" miƙewa kawai tayi ta nufi toilet. Sai a lokacin ya buɗewa Meenal tana zuwa ta rungomesa ta ce "Me kake yi ne?" Kissing bakinta yai ya ce "Ina shirin yadda zan tarbeki mana, u knw you're special" suna tsaka da yin abin da suka saba. Zee baby ta fito tare da yi musu vedio tana sakin Murmushi duk irin ihu da sumbatun da suke yana cikin Vedion.

Bayan faruwar komai ta ce "Abdul ina da ciki yaya zan?" Murmushi yai ya ce "Abin da aka saba mana" shiru tai ta ce "Na gaji da zub da ciki fa, ya kamata a nemi mafita" "ok kima Usman mgn ya fito ai auren, kin san daman matan aure sunfi daÉ—in harka tunda kince ba zaki auren ba" daga nan hospital suka nufa aka cire cikin.
Chapter 95 · 0% Book details