← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 145

Sashe 126

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"I love You"
Ya furta a hankali daidai yadda za taji da sauri ya É—ago kanta ta kalle shi ganin kamar ba shi ne ya yi maganar ba, yasa ta É—auke taci gaba da cin abincin maybe kunnuwanta ne kawai suka ji haka.

Murmushi mai laushi Salman ya yi kyansa na fita calmly ya kuma cewa.
"Ina son ki Afra, and I ready to marry you....."

"Kai da Afra har abada domin ta haramta a gare ka ni ne zan aureta" daga Afra har Salman suka ɗago kansu, ganin mutum dake tsaye ya sanya Salman yin murmushi wato tarihi zai maimaita kansa kenan. Jikin Afra na rawa ta miƙe tsaye domin bata tsammani ganinsa ba a daidai wannan lokacin. Ƙoƙarin guduwa take ya sanya hannu tare da cafkota idanun shi sun kaɗa tare da yin jaa sosai kamar gauta cikin rawar murya ya ce.

"Ni nake son ki ƴar baba tun kina ƙauye, ni ne na yi sanadiyar zuwanki nan gida, kuma a shirye nake da aurenki idan kin amince Wallahi ina son ki Please don't say No!"

"Wallahi bana son ka, ba zan taɓa son ka ba, koda zaka mutu, ni ka rabu dani ka takura mini" Innalillahi Adnan gani yake da wannan maganar gwara ta ɗauki wuƙa ta caka masa zai fi masa sauƙin fahimta. Cikin damuwa ya ƙara matsawa gareta tare da ɗora hannunta a saitin ƙirjinsa idanunsa na sauya kala yana cika da hawaye ya ce.
"Ki taimaka, ki taimaki rayuwata Afra, ko baki so na ki aure ni haka, indai zaki zauna dani matsayin miji ban damu da rashin soyayyar ba.
"Ni dai ka sakeni, ba zan iya auren wanda bana so ba, sbd ba zan masa biyayya ba ga mata nan da yawa a duniya haba"

Tashin hankali ya bayyana akan fuskar Adnan yau shi ne mace ke wahalar da rayuwar shi har yake zubar mata da hawaye? Lallai soyayyar Abra tayi tasiri a zuciyar shi,
Domin son da yake mata ya sanya ba zai iya rayuwa babu Afra ba a yanzu komai nasu iri amma me ya sa halinsu ya bambanta?.

Yi ya yi kamar zai jawota jikinsa tayi saurin ja baya kusa da Salman hawaye na zuba a fuskar Adnan sosai ya ce.
"Don darajar Allah ki duba halin da zuciyata take ciki, ki sassauta yanayin ki a kai na, ki bani dama na sauya tunani zaki so ni ina da tabbacin zan sauya miki ra'ayi da kanki zaki furta kina so na, zan fifitaki da sauran mata, zan baki farin ciki da duk abin da kikeso, zaki rayuwar ƴan ci a gidan Adnan Aliyu Matawalle..... I love You Afra, i love You to the rest of my life, I can't imagine life without you wlh ina son ki ba zaki taɓa samun wanda zai so ki kamar ni ba"

Salman ya gyara tsaiwa tare da gyara zaman babbar rigarsa cikin nutsuwa ya kalli Adnan kana ya juya ya kalli Afra a hankali ya saka hannu ya kama nata cikin nutsuwa ya ce.
"Look into my eyes yaya" kasa kallonsa tayi Ubangiji yana gani Salman mugun kwarjini yake mata, yana yiwa idanunta tasiri sosai ba kaÉ—an ba.
"Please yaya" ya ƙara faɗa a taushashe har ƙamshin spraymintt mouth freshener ɗin bakinsa yana dokan hancinta wanda ya sanya tayi saurin lumshe idanunta. ganin da gaske ba zata kalle shi ba ya sanya gaba ɗaya ya tallafo haɓarta yana sauke mata numfashi a fuska kamar zai haɗe fuskokinsu ya ce.
"I love You Afra, From the moment I first laid eyes on you, I knew you were a perfect match for me. I love everything about you. Ina son ki so mai yawa, ina kishin da zai ɗauke numfashin sarrafa rayuwata, kada ki yi mamakin ganin bamu daɗe ba, ina jinki tamkar yaya a raina, ki bani dama na bayyanawa kowa irin soyayyar da nake maki, bana son nayi zurfin cikin da nayi a kan Abra. I will be always by your side in good and bad times, in happy and sad moments… because I love you! Accept my request please yaya"

Ya kama fuskarta da dukkan hannunsa wanda itama a lokacin ta buÉ—e idanunta tare zuba masa su. Tana son fahimtar da gaske wannan kyakkyawan farin ne yake son ta kuma yake son aurenta?

"Please yaya"
Ya marairaice fuska yana narke mata. Kasancewar rayuwar ƙauye tayi babu wanda kunya sosai a tare da ita bakinta kuma baya sarrafa wani abubuwan kafin ta faɗa. Muryar ta na rawa ta ce.
"Ina son ka ni ma, kuma zan aureka in dai da gaske kake zaka aure ni"
Ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya Salman ya sauke yana ƙara riƙe fuskarta da kyau! Wani farin ciki na ratsa zuciyarsa.

A fusace Adnan ya fisge Afra daga wajan Salman idanunsa na zubar da ruwa bakinsa da gaba É—aya jikinsa suna rawa kamar ana kaÉ—a masa gangi ya ce.
"Ƙarya yake Afra, ta ya ya zaki aure wanda ki ka girma yayanki ne shi bai dace ya zama mijinki ba, ni ne daidai da rayuwar ki" ya faɗa yana jawota jikinsa sbd zafin da zuciyarsa ke masa.

"Don't try to hug the girl I'm going to marry again, na fika hauka zafin kishina yafi naka, kuma ka kusa daina ganin ko fuskarta, ita É—in mallakina ce"

"Idan kai namiji ne sai ka hanani abin da na yi niyya" Adnan ya faɗa cikin raunin murya tare da ƙoƙarin kama bakin Afra da niyyar kissing. Cikin zafin zuciya Salman ya tattare hannun rigarsa farar fuskarsa ta yi jajir sbd abin da Adnan ɗin yake ƙoƙarin yi ɗin.

Saukar marin da Salman ya ji ne ya sanya ya tsaya da sauri baki buɗe yake kallon Afra wacce ta fisge kanta da ƙyar daga hannun Adnan ta kuma sauke masa marin da ita kanta bata san tayi ba. Idanuna ya cika da hawaye sbd nauyin marin da tayi ya kalli Adnan ta ce.

"Wa kake da suna? Wallahi na tsaneka ba zan taɓa son ka maye kawai"

"Koda zan faɗa miki su waye iyayenki na gaskiya?" Ta watsa masa harara ta ce "Ai ƙarya kake tun a garinmu kake yaudarata, babu wasu iyayena daka sani"

Adnan ya fara tari sosai idanunsa na rufewa tari yaci ƙarfin sa. Abbi da Mami da suke tsaye tun ɗazo suka ji kuma suka kaga abin da ke faruwa suka shigo cikin parlourn da sauri.
"Subuhanallah! Adnan lafiya me ya sameka? Na'ima kawo mini ruwa" Adnan yakai hannu bakinsa sai ka jini ya wanke masa tafin hannun da alama kamar aman jini yake. Bai damu da halin da yake ciki ba, tarin na sarƙafe masa numfashi cikin mayuyacin hali ya kalli Afra da jikinta ya gama sanyi baki ɗaya ya ce.

"Ko da zance maki Dr G.Y Bulama shi ne mahaifinki na gaskiya..." Cak numfashin sa ya tsaya jikinsa ya saki a jikin Abbi, a kiÉ—ime Abbi ya ce "Salman get the car"

A hankali cikin nutsuwa da kamala Abdullah ke driving motar daga Airport zuwa gida. Yana mamakin abin da ya hana Uncle É—in magana, girgiza kai ya yi yana mai da idanunsa kan titi yasan yau Ummi kwanan farin ciki za tayi speaking calmly ya ce.
"Uncle lafiya dai?" Wanda aka kira da Uncle ya juya ya kalli Abdullah a hankali ya ce.
"Alhmd Abdullah" ba wanda ya sake magana a haka suka ƙarasa gida, Abdullah yai horn a gaban makaken gidan iya haɗuwa ya yi gatekeeper ya buɗe, a parking lot sukai parking kafin Abdullah ya fita ya riga shi.
Ummi na zaune ta yi ado cikin wani dakakken lace sai ɗaukan ido yake ga gwalalen dake zube a hannunta. Ƙamshin turaren shi yasa ta tabbatar da zuwan mijin nata bayan wasu watanni zuwa shekara. Tsaye ta gansa ya zuba mata idanu cike da tunani a ransa da kuma son Ummi ɗin saura kaɗan ya yi kuskure a rayuwarsa.
Ummi ta miƙe tsaye tare da ƙara sawa gabansa ta ce. "Wlcm Man" murmushi ya ƙirƙira kafin ya ce "I missing Maaah" girgiza kai kawai tayi suka ƙarasa parlour idanunsa a kanta ya ce "Kiran gaggawa ina tsaka da buɗe sabon company hope lafiya dai?" Tai murmushi cikin sanyin maganar ta ce.
"Ka fara yin wanka kaci abinci?"
Chapter 126 · 0% Book details