Sashe 58
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Abra burin kowacce Uwa ta gari ta ga aurar da ƴarta, shi ya sa kina mini batun yaron nan na ji daɗi a raina, musamman da na fuskance shi da gaske yake, ba kamar sauran samarin yanzu mayaudara ba, dan haka kar ki bari ya kufce miki, ki riƙe shi hannu bibbiyu."
"Insha Allah Mami na gode." Abra ta faɗa cikin gamsuwa, dan malaminsu na islamiyya ya taɓa faɗa musu cewa duk Uwa ta gari burinta da fatanta ta ga ta kai ƴarta ɗakin Mijinta. Wannan dalilin ya sa yau ta fara kawar da tunanin da Mami ba mahaifiyarta ba ce kamar yadda take tunani a baya. Ganin Salman bai fito ba ya sa ta miƙewa ta shiga ɗakinta don ta kira shi a waya ta lallaɓa shi ya fito ya ci abincin.
Tana É—aukar wayar ta tarar da 3 missed call na Adnan, bin bayan kiran ta yi cikin sauri. Tana shiga ya katse ya kira ta.
"Amincin Allah ya tabbata ga kyakkywar Amaryata." Abun da ya faÉ—a kenan bayan ta É—aga wayar.
Murmushi ta yi tare da zama ta ce. "Tare da kai."
"Ina kika shiga mijinki yana kiran ki ba ki É—auka ba, na kasa komai saboda rashin jin daddaÉ—ar muryarki mai mantar da ni inda nake."
Dariya ta yi ba tare da tunanin komai ba ta ce. "Na je É—akin Faris ne."
Shiru ya yi na 2 seconds sannan ya ce. "Faris, Faris dai, magana É—aya sai kin ce Faris."
"Faris is my best friend, he is my everything at all."
"Ko?" Ya tambaya cikin gatse.
"Yeah." Ta ba shi amsa iya gaskiyarta.
"Ina son na maye gurbin Faris a cikin zuciyarki ko ma na zamo fiye da shi. Now tell me, me Abbi ya ce game da maganata, na san yau Sunday yana gari."
"Mami ta faÉ—a masa."
"Ya amince?"
"Idon't know, amma duk yanda ake ciki zan sanar maka."
"Allah ya sa mu ji Alkhairi matata, ya nuna mana ranar da za ki kasance mallakina, ban san irin farincikin da zan yi ba a ranar Angel, because I love you will All my heart."
Murmurshi ta yi cikin jin daɗin kalamansa, hira suka cigaba da yi, Adnan na faɗa mata yanda yake tsananin ƙaunar ta, tare da son koya mata ƙaunar shi. Har sai da Mami ta shigo ta kira ta tare da sanar mata Abbin ya dawo.
Cikin faɗuwar gaba ta miƙe ta bi bayan Na'ima zuwa part ɗin Abbi, yana zaune akan kujera suka shiga, Na'ima ta zauna a gefensa Abra kuma a saman carpet ɗin dake shimfid'e a parlour'n.
"Sannu da hutawa Abbi." Ta faɗa kanta a ƙasa.
"Yawwa Daughter, Mamanku ta zo mini da wata magana jiya wadda ban amince da ita ba, ki faÉ—awa shi yaron da kika kawo shi gidana ba tare da iznina ba ya nemi wata, ke yanzu karatu zaki yi ba aure ba."
Dam zuciyar Abra ta buga, satar kallon Na'ima ta yi, Signa ta yi mata alamun ta faÉ—i duk abubuwan da ta ce mata.
"Dan Allah Abbi ka yi haƙuri ka amince wallahi ina son sh....."
"Shut up! Ni zan dinga faÉ—ar abun da za a yi kina cewa ba haka ba? Wato har kin yi girman da zaki fara jayayya da ni ko? To na faÉ—a na kuma faÉ—a, ba zan yi miki aure yanzu ba karatu zaki yi." Khamal ya katse ta da faÉ—in haka cikin tsawa.
Kuka Abra ta saka ta fara bawa Abbi haƙuri, bai saurare ta ba ya ce ta tashi ta tafi. Kallon Khamal kawai Na'ima take yi cikin ƙunar zuci, cike da takaici ta ce. "Gaskiya Major abun da ka yi ba ka kyauta ba, wai mene dalilinka na ƙin son aurar da yarinyar nan ne? Ni fa ban gane ba, ko kwaɗata za mu yi mu cinye? Haba yarinya ta fi 20 years amma ka ce ba za ka aurar da ita ba wani karatu za ta yi, karatun me? Ai aure ba ya hana karatu, haka ma karatu ba ya hana Aure." Wani mugun kallo khamal ya wurga mata sannan ya miƙe ya bar parlour'n. Jijjiga kai ta yi tare da miƙewa ta fice ita ma.
Ɗakin Abra ta je, tarar da ita ta yi ta kifa kanta akan gado tana kuka. A hankali ta ɗago da ita ta rungume ta. Cikin sigar rarrashi ta ce. "Ki yi shiru haka kar kanki ya yi ciwo, ki bar ni da Abbi na san ta inda zan ɓullo masa." Cikin kuka Abra ta ce. "Mami na haƙura tunda Abbi ba ya so, bana son in ga yana fushi da Ni." Da sauri Na'ima ta ce. "A'a Daughter, tunda kina son shi yaron zan yi duk yanda zan yi na ga kin Aure shi, kar ma ki ƙara tunanin za ku rabo, ko ba kya son shi ne?"
"Ina son shi."
"To kuma, abun da nake so dake kawai guda É—aya ne, ki daina mayar da hankali akan karatunki."
Cikin mamaki Abra ta ce. "Ban gane ba Mami."
Zama ta yi a gefenta ta ce. "Yawwa, abun da nake nufi ki daina karatu, idan an ba ku assignment ki daina yi, ba dai saboda karatun ya ce ba zai aurar da ke ba?" GyaÉ—a mata kai Abra ta yi.
"To idan ya ga an kafe result duk kin faÉ—i dole ya aurar da ke ai."
Shiru Abra ta yi tana nazarin abun da Mami ta ce, anya kuwa za ta iya? Idan ta yi hakan fa tamkar ta watsa wa Abbinta ƙasa a ido ne, wani b'arin na zuciyarta kuma hango mata yake rabuwar su da Adnan, gaskiya ba za ta so su rabu ba, kawai za ta bi shawarar Mami. Cikin rashin wayo ta ce. "Za mu yi text gobe, kar na yi karatun ta kenan Mami?"
"Kar ki yi, idan kin je class an yi muku attendance kar ki kuma yi, ko assignment aka ba ku ki daina yi kin ji yarinyar kirki?" Shiru Abra ta yi tana tunani, ganin kamar ba ta gamsu ba ya sa Na'ima ta gyara zama ta shiga kalailame ta da nuna mata illar rabuwar ta Adnan, har ta samu ta amince da shawarar tata ta daina yin karatu, cikin murmushin mugunta ta rungume ta ajikinta tare da saka mata albarka. Abra har cikin ranta ta yarda da abubuwan da Mami ta faɗa mata, soyayyar Adnan da ta yiwa zuciyarta mugun kamu gami da tsoron rabuwa da shi su suka taimaka gurin ƙara assasa amincewa da hakan, ta manta Abbinta mutum ne mai magana ɗaya gami da kafiya akan abun da ya ce, ko da ba ta mayar da hankali akan karatun ba idan bai so ba, ba zai aurar da ita ba.
Bayan Magriba Na'ima na zaune a parlour suna waya da Ammi tana sanar mata halin da ake ciki. Bayan ta gama Ammi ta ce. "Wacce irin magana ce wannan? Me Babana yake nufi da aikata wannan ɗanyen aikin da yake ƙoƙarin yi? Idan ba a aurar da yarinyar ba saka ta za mu yi a gaba mu dinga kallon ta? Ai aure shi ne mutuncin kowacce mace, kowa na addu'a Allah ya kawo wa yarsa miji na gari shi kuma ya samu zai ce a'a, to bai zai yiyu ba, zan zo har gidan in same shi in nusar da shi illar abun da yake ƙoƙarin aikatawa? Bokon me? da za a ce saboda ita za a jinkirta aure, komai fa lokaci ne da shi, ban da abun Babana ai wannan abin farinciki, addu'a kawai ya kamata ya yi tare da bincike akan yaron da ahalinsa dan tabbatar da nagartar shi."
Cikin jin daɗi Na'ima ta ce. "Abun da na yi ta faɗa masa kenan Ammi, amma ya ƙi ji ya yi biris da ni, kuma wallahi Ammi ba ki ga yaron ba nutsatstse ga hankali, daga gani ɗan gidan manyan mutane ne wanda suka san darajar kansu. Gashi ita ma Abran tana son shi sosai, dan baki ga yanda take kuka ba da Khamal ya ƙi amincewa."
Salman da ya fito dan zuwa kitchen ya samarwa kansa abun da zai ci jin yunwa na ƙoƙarin hallaka shi kalaman Mami suka doki dodon kunnansa. Cak ya tsaya cikin wani irin yanayi, a razane ya ce. "What? Mami! Ammi kika sanarwa da wannan maganar?" Hararar shi Na'ima ta yi ta cigaba da sauraren Ammi dake sanar mata gobe da safe za ta yi sammako ta zo ta sami Khamal kafin ya tafi gurin aiki, don ta ba shi umarnin amincewa da batun neman Auren Adnan da Abra.
Dafe kai Salman ya yi cikin takaici, Mami ba ƙaramin gamawa da shi ta yi ba da ta sanar da Ammi maganar nan, saboda yanda Ammi ba ta zance kodayaushe sai na Allah ya kawo wa Abra miji ta yi aure. Amma duk da haka ba zai haƙura ba, matuƙar yana numfashi ba zai bari wani ya auri Abra ba shi ba, dan haka zai fasa ƙwai kowa ma ya san abun da yake faruwa, zai sanar da Abbi cewa yana son Abra zai aure ta a yau ba gobe ba, in ya so duk abun da zai faru sai dai ya faru![10/4, 3:15 PM] Abk: A fusace Salman ya juya kai tsaye kuma Part ɗin Abbi ya nufa, zuciyarsa babu daɗi ji ya ke tamkar zata faso ta tsakiyar ƙirjinsa ta fito, saboda tsananin bugawa da ta ke da ƙarfin gaske.
Gane nufin Salman ya sanya Mami saurin miƙewa tare da shan gabansa, fuskarta sam babu walwala a kaushashe ta ce. "Well-done, wato kana nuna mini ban isa da kai ba? kada ka manta ni na ɗauki cikin ka, nai dakonsa na tsayin watanni tara, na haife ka. Haihuwar da babu shiri, kana na raine ka, na shayar da kai nonona na tsayin shekaru biyu. Amma yau ni nake faɗa maka magana kana yi mini musu? Yarinyar da ba ni na haife ta ba, ta fika yin biyayya a gareni ko Salman"