← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 145

Sashe 107

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin yadda ake ta zuwa yi wa Adnan gaisuwa ya sa Hajiya Mama ta saka aka yi masa rubutun dangana take ba shi yake sha, saboda babu daɗi a dinga ganin shi a birkicen da yake, don ba shi da maraba da mahaukaci. Alhamdulillah kwalliya ta biya kuɗin sabulu, cikin kwana biyu ya fara dawowa cikin hayyacinsa, ya rage surutan da yake yi. Sai dai ba um ba um'um, sai ya wuni baiwa kowa magana ba, abinci kuwa da ƙyar yake yin 3 spoon a yini, sai ruwan bunu da Hajiya Mama take matsa masa yake sha. Gabaɗaya ya lalace ya zama abun tausayi, duk wannan abubuwan har yanzu Abba ba ya shiga harkarsa, ko Kallon inda yake ba ya yi, abun har ya fara damun Hajiya Mama.

A hankali yake tafiya kamar zai fadi saboda rashin ƙwarin jikinsa, hannunsa ɗaya dafe da kansa dake yi masa wani irin ciwo, ɗayan kuma ya ɗora a kan ƙirjinsa da ya ji ya yi masa nauyi. Da kyar ya iya ƙarasawa compound din gidansu, cikin haki ya dubi direban Hajiya Mama wanda ya zuba ido masa cike da tausayawa, muryarsa ko fita ba ta yi sosai ya ce. "Kai ni gidana." Direban kamar ya yi magana sai kuma ya fasa ya miƙe ya nufi parking space, a galabaice Adnan ya mara masa baya.

Da kallon tsantsar mamaki mai gadi yake bin Adnan da shi lokacin da ya fito daga mota, don da farko ma bai gane shi ba, sai da ya nutsu sosai ya gane mai gidan ne. Yana gaishe shi amma ko tsayawa saurar shi bai yi ba.

"Ikon Allah, gaskiya mu ji tsoron duniya, yanzu yallaɓai ne ya koma haka? Ya rame ya ƙara duhu sai idanu ƙwala-ƙwala da suka ƙara fitowa, ga saje da sumar kansa duk sun yi wani iri, kamar ba shi ne ɗan gayun nan mai tafiyar jaruman Maza ba, Taɓdi! Allah dai ya sa mu dace." Mai gadi ya faɗa yana bin bayan Adnan da kallo.

Ƙofar parlour'n a buɗe take, tun ranar da Abra ta fito ta faɗi take a haka, shi ma ranar da ya dawo bai tsaya rufewa ba jin tana asibiti. Hannunsa na rawa ya buɗe ƙofar ya shiga, cak ya tsaya idanunsa cike da hawaye yana kallon gurin da take yawan zama a parlour'n.

"Angel don Allah ki fito, na san kina cikin gidan nan, za ki fito daga ɗaki ki tarɓe ni yanzu kamar yadda kika saba ko? Na san ba ki mutu ba, nan kika zo kika ɓuya." Ya ƙarashe maganar tare da nufar ɗakinta yana kuka wiwi. Tura ƙofar ɗakin ya yi da ƙarfi yana kiran sunanta. Ƙamshinta da bai bar ɗakin ba har lokacin ya ziyarci hancinsa. Kan gadon ya ƙurawa ido, cikin fatan ya gan ta a kwance kamar yadda ya saba ganin ta lokuta da yawa a baya.

"Adnan, don Allah ka sauwaƙe mini wannan ƙaddararren auren naka."

"Me ya sa za ka É—auki fansa a kaina? me na yi maka? Mene laifi na? Don Allah kar ka cutar da ni akan abin da ba ni na aikata maka ba."

"Ina son ka Adnan, don Allah kar ka juya mini baya."

Maganganunta da ta yi masa a mabanbantan lokuta cikin kuka suka yi masa kuwwa a cikin kunne, kamar a yanzu take durƙushe tana roƙon shi.

"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un! Wallahi ina son ki matata, ki yafe mini ki dawo gare ni, na yi nadama da dana sanin cutar da ke a rayuwata." Adnan ya faɗi haka cikin kuka tare da faɗawa kan gado saboda jirin da ya kwashe shi. Ranar da ya fara ganin innocent face ɗinta a school ya tuna, da ranar da suka haɗu a cafeteria har ya ɗauke mata wayarta, da ranar da ya ɗauke ta suka je restaurant daga nan ya kai ta gida. Wani irin kuka ya fashe da shi lokacin da ya tuna yadda ta so shi, ba tare da wani jan rai ba, ta so shi saboda Allah ba don komai ba, amma ya butulce mata, ya muzguna mata, ya ƙunƙuta wa rayuwarta, gashi nan ta tafi ta bar masa duniyar.

Sosai yake kuka tare da bubbuga kansa a jikin gado, muguntar da ya dinga yi mata kala-kala na faɗowa a cikin ransa. Babu abin da ya fi damun shi irin yadda yake zuwar mata ta ƙarfi a mu'amalar Aure, amma ba ta taɓa hana shi ba ko ta nuna rashin jin daɗin ta akan hakan, saboda ta san haƙƙinsa ne. Sai abu na biyu da ya yi mata wanda ba zai yafe wa kansa ba, ranar da ya kawo karuwa gidan, ba ya bin mata, hasalima ya tsani karuwar mace, amma saboda ya ƙuntata mata ya samo karuwar ta dalilin wani abokinsa da yake harkar, ya dinga tattaɓata duk da ƙyanƙyamin ta da yake yi. Saboda kawai ya ɓata wa baiwar Allar da ba ta ji ba, ba ta gani ba.

Dama ana dawo da rayuwa baya, da ya dawo da tasa ya goge duk abin da ya yi wa Abra, ya maye gurbinsa da sanyata farinciki da jin daɗi, sai dai kash! Ba shi da wannan damar. Miƙewa ya yi a haukace ya buɗe wardrobe ɗinta ya shiga ɗebo kayanta yana shinshinawa tare da yin surutai irin na fitar hayyaci. Gabaɗaya ya hargitse ɗakin da sunan neman inda ta ɓuya yake, cikin haka ya ga wayarta a ƙasan gado. Jiki na rawa ya ɗauko ya kunna, ya yi sa'a da guntun chaji a ciki, kuma wayar babu key. Direct Gallery ya shiga ya fara kallon pics ɗinta da short videos.

"Why Abra? Me ya sa za ki tafi ki bar ni? Ya Allah ka ɗauki raina cikin gaggawa, domin rayuwata ba ta da amfani idan babu Angel." Ya ƙarashe maganar tare da cillar da wayar saboda wani irin tari da ya turniƙe shi. Daidai lokacin direban da ya kawo shi ya shigo parlour'n, saboda tun ɗazu Hajiya Mama take kiran shi akan ya dawo da Adnan gida, ta shiga ɗakin Adnan ba ta gan shi ba sai ta fito harabar gidan ta tambayi mai gadi ko ya kan shi? Ya sanar mata ya ga driver ya ɗauke shi sun fita. Bai gan shi a parlour'n, hakan ya sa ya nufi ɗakin da yake jiyo ɗan motsi ya yi sallama, jin ba a amsa masa ba ya sa shi kutsa kai ciki ya tarar da Adnan cikin mawuyacin hali.

Ganin yadda Adnan yake tarin kamar wadda ake zarar ransa ya sa ya kama shi cikin sauri suka fita. Fuskarsa duk dagaje-dagaje da hawaye da majina, ga gefen kansa ya fashe saboda buga kansa da ya dinga yi, gaban jallabiyar jikinsa ya jiƙe sharkaf da hawaye da gumi. Suna dawowa gida Hajiya Mama ta ce su tafi asibiti kawai, don a lokacin har ya sume. Kwanansu uku a asibitin aka sallamo shi, duk da bai warke ba amma ya fara jin sauƙi, bayan sun dawo gida Hajiya Mama ta same shi a ɗaki yana sana'ar tasa ta tunani, zama ta yi a kusa da shi cikin sanyin murya ta fara magana.

"Adnan, ka takura sai an sallame ka mun dawo gida, to mun dawo É—in, amma don Allah ka cire damuwa da tunanin da ka saka a cikin zuciyarka, ka ji likita ya ce jininka ya hau sosai, sannan kuma ciwon zuciya na daf da kama ka, ko so kake Æ´arku ta rayu marainiya ba uwa ba uwa?"

Girgiza kai ya yi a hankali.

"To ka daina, ka bar wa Allah komai sai ka ga ya ba ka wata wadda ta fita."

"Babu macen da tafi Abra a duniya Mama, ba zan taɓa samun mai haƙuri da ladabinta ba, na riga na yi babbar asara a rayuwata." Ya faɗi haka cikin kuka.

"Wai yaushe za ka bar kukan nan ne, kamar ba namiji ba? Namijin ma Jarumi irinka, ka zamo mai tawakkali mana da miƙawa Allah al'amuranka, sai ka ga ya kawo maka komai cikin sauƙi."

"Na cutar ita! Na zalunce ta! Na ƙuntata mata, akan abun da ba ta da masaniya a kai, na yi nadama mara adadi."

"Ashsha! Shi ya sa ba komai zuciya take faɗawa mutum ya bi ba, domin ita ba ta da ƙashi, ka tafka babban kuskure a rayuwarka Adnan, ka yi wauta."

Bai ƙara magana sai kansa da ya kifa akan pillow yana sassauke numfashi, girgiza kai Hajiya Mama ta yi ta tashi ta fice. Parlour'n Abba ta je ta same shi yana waya, bayan ya gama ta dube shi ta ce. "Alhaji don Allah ka sassauta fushin da kake da yaron nan, ko ya samu sauƙi a rayuwarsa, kwanansa uku a asibiti amma ba ka je ka duba shi ba."

"Ni na ce fushi nake da shi ne? Abin da yake so ya ga dama ya aikata, to me zan yi masa kuma? Da na sani da kaico ne yanzu ya fara gani a cikin rayuwarsa."

"Subhanallahi! Kar ka yi masa baki mana Alhaji."

"Ba baki na yi masa ba, amma ni da ke da shi duk mun san *ABIN DA KA SHUKA* shi za ka girba, don haka bai ma fara girɓar abin da ya shuka ɗin ba, tukunna dai."

Hajiya Mama ba ta kuma magana, don ta san idan Abba ya yi irin wannan fushin ba mai iya sakko da shi, sai ya ga dama ya sakko da kansa.

4 weeks later

Mami ce zaune a ɗakinta rungume da A'isha Humairah tana yi mata wasa, ita kuma ta yi mata ƙuri da ido. Wata irin ƙaunar yarinyar Nai'ma take yi, musamman yanzu da kammaninta suka juye sak na Mamanta. Sai da ta yi bacci sannan ta kwantar da ita a kan gado ta ɗauki wayarta ta kunna data ta shiga WhatsApp.

Reply na messages ta dinga yi, bayan ta gama ta tafi status ta fara kalla. Wata irin zabura ta yi lokaci ɗaya ta miƙe tare da cillar da wayar tata, kamar wata mahaukaci ta ƙwalla ƙara tare da murza idonta.
Chapter 107 · 0% Book details