Sashe 13
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin tsana Na'ima ta wurga mata wani kallo tana huci kamar zata ci babu, ji take tamkar ta fizgo Abra daga jikin Khamal. Tsaki Captain ya yi ya miƙe tare da Abra a jikinsa ya shige bedroom ɗinsa yana rarrashin ta. Ganin haka yasa Na'ima fashewa da kuka tare da zama daɓas akan kujera, ganin yadda ya maida ita mahaukaciya.
"Khamal why? Me yasa zaka mun haka? Ban cancanci haka daga gare ka ba, kar ka saka mun tukwicin k'aunar da nake yi maka da cin amana."
Ta faÉ—i haka cikin sheshshek'a.
Ƙarfe biyar da mintuna su Ammi suka ƙaraso gidan, har lokacin Na'ima tana zaune a inda take, ta ci kuka ta gode Allah, sai wani irin haki take yi saboda tsabar ɗorawa kai masifa, ga nauyin ciki.
Tana jin ana knocking ta miƙe da sauri ta buɗe ƙofar, zatonta ya zama gaskiya su Ammi ne tare da Baffa.
Granny ce a gaba, baki buÉ—e take kallon Na'ima bayan sun shigo, tafa hannuwa ta shiga yi ta ce. "Na shiga uku ni Mari, wannan fita hayyacin naki da kika yi Na'ima na mene ne? Ko waya aka yi miki aka ce tsohuwa ko tsoho wani ya mutu?"
Na'ima ba ta bi ta kanta ba ta yiwa su Ammi sannu da zuwa cikin dauriya.
Kama hannunta Ammi ta yi cikin lallami ta ce. "Na'ima ba ki ji abun da na faÉ—a miki ba ne na cewa ki kwantar da hankalinki? Kin ga yanda kika koma kuwa?"
Sake fashewa tai da kukan tace "To Ammi ya zan yi? Ba ki ji yanda zuciyata take mun wani irin zafi da suya ba ne."
Baffa ya yiwa kansa mazauni ya ce. "Ina shi Khamal É—in yake?"
"Yana É—akinsa tare da Yarinyar." Na'ima ta faÉ—a cikin É—acin rai.
"A'a, wacce yarinyar kuma? Me kuke zance akai ne? Me yake faruwa ne?"
Granny ta tambayi haka tana bin su da kallo.
Ganin babu mai shirin ba ta amsa cikin fusata ta ce. "Yau na ga jaraba, ya ina tambayar ku, kun mun shiru kun mayar da ni wata gantalalliya? Ni dama tun da na ga Buba ya dawo gida hankali a tashe na san da wata a ƙasa, na tambayi me ya faru kuma saboda ba'a ɗauke ni da muhimmanci ba an ce mun ba komai, duba jikin Khamalu kawai za'a zo yi, na zo kuma na ji ana wani zance na daban da ban gane masa ba."
Cikin girmamawa Ammi ta ce. "Hajiya ki zauna zaki ji komai yanzu."
"Wanne irin in zauna kuma kamar wata ruɓaɓɓiya? Ƴarki ce ni da zaki ba ni wannan umarni haka?"
Ammi ba ta kuma magana ba ta nemi guri ta zauna, Na'ima da take jin kamar ta tsinkawa Granny mari saboda takaici ta nufi ɗakin Captain ta fara yin knocking da ƙarfi.
Lokacin yana kwance idanunsa a lumshe, raba Abra ya yi daga jikinsa a hankali wadda ya samu ta koma bacci da ƙyar sannan ya miƙe a fusace ya je ya buɗe ƙofar. Ganin haka yasa Na'ima ta juya ba tare da ta yi masa magana ba, kamar ya share ta ya koma sai dai ya daure ya bi bayanta.
Cikin mamaki yake duban su Ammi ganin su zaune a parlour ba tare da ya san da zuwan su ba. kallon Na'ima ya yi cikin ɓacin rai, akan wannan 'Yar maganar shine ta ɗaɗɗako iyayensa suka zo? Siririn tsaki ya ja a hankali ya ce. "Sannun ku da zuwa."
"Granny ta ce. "Yawwa, ya jikin naka É—an albarka? Na ga jiki ya yi kyau Masha Allah."
"Da sauƙi Alhamdulillah." Ya ba ta amsa ba yabo ba fallasa.
Baffa ya ce. "Nemi guri ka zauna mu yi magana." Bai yi musu ba ya zauna a saman carpet.
"Wacce yarinya ka kawo gidanka Khamal?" Baffa ya jefa masa wannan tambayar.
A nutse ya fara magana cikin ladabi. "Baffa a wannan operation É—in da muka fita na tsinci wata yarinya k'arama daban ba'a cikin yaran da aka yi kidnapping É—insu ba...." Bayanin komai ya yiwa Baffa har yadda suka yi da Na'ima bayan an kawo Abra.
Cikin zuzuta Granny ta ce. "Huhuhu, yau na ga ƙarfin hali, Na'ima ashe dama ke ba matar rufin asiri ba ce ba mu sani ba? Na ɗauka ko dabba Khamalu ya kawo gidan nan baza ki ce uffan ba sai dai ki karɓe ta hannu bibbiyu. To gidan naki ne ko nasa? ban da jaraba irin taki mutumin ba shi da lafiya amma ki saka shi a gaba da fitina, kina fama da narkeken ciki haihuwa ko yau ko gobe maimakon a gan ki da carbi a hannu kina lazimi akan Allah ya sauke ki lafiya, amma ke ta neman bala'i kike? Tirrr da wannan abu."
Na'ima ta saka kuka ta ce. "To kuma a rasa mai riƙon yarinyar sai shi kaɗai? Cewa fa ya yi idan ba'a ga iyayenta ba a nan za ta cigaba da zama tare da mu."
Baffa yana duban ta ya ce. "Ki kwantar da hankalinki Na'ima, a yanayin da kike ciki ba'a son kina saka damuwa har haka a cikin ranki."
Ammi ta nisa ta ce. "Amma Khamal daga tsintar yarinya sai ka ce kana son ta zaka riƙe ta? Mene ma'anar yin hakan?"
"Wallahi first love ba da wata manufa nake son riƙe Yarinyar nan ba, tun kallon farko da yi mata na ji ina jin tausayinta sosai a cikin raina. Ni fa ban ga abun ɗaga hankali a wannan abun ba, me yarinyar za ta tsare mata in ta zauna a gidan? Ammi ke uwace ya rayuwar wannan yarinya za ta kasance idan ta faɗa hannun ɓata gari?"
Na'ima ta e "Ai dama dole ka ce haka tun da Ubangiji ya toni asirin ka, to wallahi sai dai ka zaɓa ko ni ko ita, amma ni dai ba zan zauna da ita a cikin gidan nan ba."
"Sai ki san inda dare ya yi miki, gida dai nawa ne kuma abun da na gama zan yi a cikinsa." Ya ba ta amsa cikin haÉ—e rai.
Tsawatar musu Baffa ya yi ya ce. "Ya isa haka! Ba zuwa muka yi mu saka ku a gaba kuna sa'insa ba."
Ya mayar da duban sa ga Na'ima ya ce. "Ki yi hak'uri ki bar yarinyar ta zauna a nan ɗin kafin Allah ya bayyana iyayenta, kar kuma ki saka a ranki na goyi bayan Khamal ne, a'a ko kaɗan, na san halin Khamal na san waye shi, ba'a shaidar ɗan mutum amma zan yabi Khamal akan ba ya aikata zina, tun daa da ba shi da mata bai yi ba balle yanzu da yake da ke. Taimako ne zai yi na riƙon yarinyar, domin idan ya bar ta ba'a san yanda rayuwarta zata kasance ba, duk da gwamnati za ta kula da ita tare da ba ta kariya amma nan ɗin sai ya fi safe."
Granny dake bin su da ido ta fashe da kuka ta ce. "Allah wadaran naka ya lalace, yanzu Na'ima saboda tsabar baki da ta ido mijinki kike dangantawa da zina? To ki je dan kanki, Allah kuma ya saka mana akan wannan k'azafi da kika yiwa jikana."
Ta share hawayen fuskarta tana mitsi_mitsi da ido ta ce. "Kin ci albarkacin cikin dake jikinki, amma wallahi da yau a bazawara zaki kwana a gidan Ubanki, domin kuwa ke ba matar mutunci ba ce, ja'ira da ido kamar an soya Aya."
Baffa ya ce. "A'a Hajiya a dai bi komai a sannu.."
Bai gama rufe baki ba ta hayayyaƙo masa da faɗin. "Na ƙi na bi a sannun, Sharrin zina fa ta yiwa jikana, ku kuma yana ɗanku kun zauna kuna yin abu wani lako_lako kun ƙi yin abu da jiki ki ɗauki mummunan mataki a kanta."
Ta ƙasan ido Na'ima ta dinga wurga mata harara. Nasiha mai ratsa jiki Baffa ya yi musu akan su ƙara hak'uri da juna, sannan ya yiwa Na'ima faɗa akan zargin da ta yiwa Captain, ya nuna mata hakan ba daidai ba ne, musamman da already dama ta riga ta san halin Captain, bai kamata daga ta gan shi da yarinya ta ce ƴarsa ba ce. Sannan ya ba ta hak'uri akan riƙon Abra da ya ce su yi, dan ya gani baro baro a fuskarta ba ta ji daɗin hakan ba ko kaɗan. Shi kuma Baffa haka Ubangiji ya yi shi, mutum ne mai faɗar gaskiya komai ɗacinta, ko da ba za ta yi maka daɗi ba sai ya faɗa, sai dai ka ji haushin sa. Ammi ma ta ɗora da ta ƴar nasihar da ban baki a gare su gaba-d'aya. Na'ima kawai jin su take yi amma ba ta fahimtar me suke cewa, ita kawai gani take yi sun goyawa ɗansu baya ne.
"Sai masifa da wasu surutai ake yi, amma ko yarinyar da ake jarabar a kanta ba mu gani ba." Cewar Granny tana yatsina fuska cike da rikicin tsufa.
Captain da hankalinsa gaba-d'aya yana kan Abra, ya miƙe ba tare ya yi magana ba ya nufi ɗakinsa, Na'ima ta bi shi da kallo hawaye na zuba daga cikin idonta, wani irin haushinsa cunkushe a cikin zuciyarta.
Yana shiga ya tarar Abra ta tashi daga baccin, tana ta kuka tare da kiran sunansa. Rungume ta ya yi tsam a jikinsa ya shiga rarrashin ta. Ajiyar zuciya ta saki tana kallon fuskarsa cikin maganarta da ƙarfi ta ce. "Abbi"
"Na'am My daughter, I'm sorry na tafi na bar ki ke kaÉ—ai ko?" Ya yi maganar yana shafa kanta. Duk da ba ta ji me ya ce sosai ba sai ta tura bakinta gaba. Kissing kuncinta ya yi cikin murmurshi sannan ya É—auke ta suka fito parlour.
Kallon Abra kawai su Ammi suke cikin mamaki. Ammi ta ce. "Ikon Allah, wannan yarinya haka kamar Balarabiya?"