← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 145

Sashe 129

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mahaifinsu ya saka su a makarantar boko da islamiyya, amma sai ya fi mayar da hankali a kan karatun boko, a cewar shi saboda shi ne karatun samun kuɗi. Suna daf da kammala secondary school suna SS 3 Allah ya yiwa mahaifinsu rasuwa. Bayan Mahaifiyarsu ta fita daga takaba sai Bulama ya fito da buƙatar cewa yana son ya cigaba da karatu, Mahaifiyarsu ta ce A'a, ita dai ta fi son ya zauna ya cigaba da kiwo ya gaji mahaifinsa, a ganin Bulama hakan faɗuwa ce a ce kamar shi wayayye ɗan boko da kiwo, ba zai iya ba gaskiya. Lallaɓa mahaifiyarsu ya dinga yi tare da nuna mata alfanun karatun fiye da Noma, har ya samu ta amince, aka siyar da wasu daga cikin shagun da baffansu ya bari aka damƙa masa kuɗin akan ya je ya cigaba da karatun da su. Yadda ake ba shi labarin ABU Zariya da kuma wasu daga cikin abokansa da suke can ya sa shi ma ya je ya fara karantar medicine.

Shigar shi makaranta ya ƙara masa ƙarfin burinsa a cikin ransa, saboda ganin yadda ƴaƴan masu kuɗi suke rayuwa, abun yana matuƙar burge shi. Ba ya abota da ƴaƴan talakawa yan'uwansa sai dai da masu kuɗi, kasancewar shi kyakkywa kuma ɗan gayu ya saka ake ɗauka shi ma ɗan masu kuɗin ne. Suna level 3 aka tafi wani strike mai zafi, a lokacin wani abokinsa Munnir yake sanar masa mahaifinsa ya tura shi ƙasar Dubai akan harkar kasuwancinsa, zai tafi idan aka koma school sai ya dawo. Ranar da ya faɗa masa kasa bacci ya yi, don ji yake dama a ce shi ne zai tafi Dubai ɗin nan, ya dinga ƙissime-ƙissimen me zai siyar a cikin gadon da mahaifinsu ya bar musu wanda zai ishe shi kuɗin jirgi zuwa Dubai ya bi Munnir su tafi tare, amma duk abin da ya ayyana zai sanar sai ya ga ba zai kai ba, don duk saboda karatunsa da ƙaryayyakin da yake kiran Inna ya yi mata akan kuɗi, ya sa duk ta sissiyar da abubuwa da dama na gadon ta tura masa kuɗin. Bayan kwana biyu abin yana cin shi a rai ya kasa dannewa, hakan ya sa ya yanke shawarar kawai ya kira Munnir ya sanar masa, ko Allah zai saka a dace su tafi tare.

Kamar wasa Munnir yana kai maganar gaban mahaifinsa ya amince, bayan ya kai masa Bulama ya yi masa tambayoyi a game da rayuwarsa, jin Maraya ne kuma ba shi da aikin yi ya sa ya amince, amma bisa sharaɗin sai iyayensa sun amince. Cikin tsantsar murna Yusuf ya koma gida ya sanar da Inna, da farko ƙin amincewa ta yi, sai da ya kira mahaifin Munnir ya yi mata bayani sosai yadda za ta gane sannan ta amince da ƙyar. Sun ci kuka lokacin da zai tafi ita da Murja wadda ake shirin aurenta a lokacin, amma shi ko ɗigon hawaye saboda farinciki da murnar da yake ciki, a ganin shi wannan dama ce da za ta taimaka wajen cimma burinsa.

Sun isa garin Dubai lafiya, babu ɓata lokaci kuma suka shiga abin da ya kawo su na business, Bulama jin zuciyarsa yake fess yau ga shi a Dubai, tamkar wanda aka tsunduma a Aljannah haka yake jin kansa don farinciki. Ranar wata Juma'a da ba zai taɓa mantawa da ita ba a rayuwarsa sun je wani shago siyayya suka haɗu da Rumaisa.

Shagon sayar da Gold's ne, su Bulama sun zo siya wanda za su tura wa Baban Munnir Nigeria ya sayar. Suna cikin zaɓa Bulama ya kai hannu zai ɗauka ita ma ta kawo kyakkyawan farin hannunta. A tare suka janye hannayen nasu tare da duban juna da sauri. Kasancewar ta mace mai fara'a sai ta sakar masa murmushi tare da faɗin. "I'm sorry." Cikin siririyar muryarta. Murmushin ya mayar mata tare da ɗaga mata hannu alamun babu komai, sannan ya bar gurin. Da kallo ta bi shi har ya ɓacewa ganin ta, ajiyar zuciya ta sauke ta cigaba da duba sarƙoƙin.

Tunda Rumaisa ta koma gida sai Bulama yay ta faɗo mata a rai, abin ya ba ta mamaki ba kaɗan ba, don duk da kallo ɗaya ta yi masa amma ta gane ba ƙabilarta ba ne, bai ma yi mata kala da fararen fata ba, ya fi mata kala da ƴan Africa, duk da fari ne tass shi ma. Bayan wasu kwanaki suka ƙara haɗuwa a hanya, a lokacin suna tare da ƙaninta Abdallah, amma duk da haka sai ta yi masa magana, abin mamaki shi ma ya gane ta, gaisawa suka yi cikin fara'a kamar waɗanda suka daɗe da sanin juna.

Watarana su Munnir sun je gurin da suke sayayyar kaya suka tarar kayan gurin duk an kwashe sai kaɗan, mai gurin ya ce su bari sai zuwa washegari za a jera wasu sai su zo su saya. Cikin rashin jin daɗi Munnir ya ce masa. "Ai kayan nan yau ake buƙatar su, saboda mahaifinmu yana ta kiran mu akan nasa sun kusa ƙarewa, kuma mun riga mun yi bucking Flight ɗin da zai tafi da kayan." Mai gurin ya ce musu babu damuwa, zai haɗa su da wata abokiyar kasuwancinsu, wadda Insha Allahu komai suke so za a su samu a gurinta. Ba su yi musu suka amince masa, bayan sun je suka tarar da fiye da abin da suka yi tsammani, don duk wani nauyi na Dubai gold akwai shi a shagon, kuma kayan gurin da sauƙi har ya fi na inda suke saya. Alokacin ba su haɗu da mai shagon ba sai yaranta, don ba ta zama ita a sati sau ɗaya take zuwa ta ga yadda abubuwa suke tafiya. Da za su ƙara sayan kaya sai suka koma gurin, saboda mahaifin Munnir ya yaba kayan sosai, ya ce idan za su ƙara saya su je can idan za a samu. A wannan zuwan Bulama suka ƙara haɗuwa da Rumaisa, ashe ita ce mai gurin. Ta yi mamakin ganin su sosai, shi ma haka. Tun daga ranar idan suka zo siyayya sometimes suna haɗuwa, har suka saba suka yi musayar contacts ɗin juna. Munnir ya dinga tsokanar Bulama yana cewa. "Ɗan fillo ko dai da ƴar Balarabiyar nan za a yi ne?" Idan ya faɗi haka sai ya yi murmurshi ya ce, babu ɗaya haɗuwar jini ce kawai.

Asalin Rumaisa Balarabiya ce Ƴar ƙasar Dubai, kyakkyawa ce don ko a cikin larabawan mai kyau ce, ita kaɗai iyayenta suka haifa, tun tana yar ƙarama mahaifinta ya rasu. Mahaifinta shahararren mai kuɗi ne, ya mutu ya bar dukiya mai ɗimbin yawa. Mahaifiyarta ta ƙara aure bayan rasuwar mahaifinta ta haifi Ɗa Namiji Abdallah.

Shaƙuwa mai ƙarfi ce ta shiga tsakanin Rumaisa da Yusuf Bulama, daga baya kuma ta rikiɗe ta koma soyayya. Tsakani da Allah Rumaisa take ƙaunar Yusuf, shi kuma yana son ta ne saboda tarin dukiyarta, amma ko kaɗan ba ya nuna mata hakan, don in ta ba shi abu ma ba ya karɓa sai ta nuna masa ɓacin ranta. Ƙauna da kulawa yake nuna mata sosai, wanda hakan yake ƙara dilmiyar da ita a cikin ƙaunar shi. Cikin haka aka janye strike ɗin da aka tafi na watanni goma sha uku, lokaci shekara guda cif da haɗuwar Rumaisa da Bulama. Ranar da za su dawo Nigeria ba ƙaramin tashin hankali da damuwa Rumaisa ta shiga ba, Yusuf ya dinga pretending as ya fita shiga damuwa, da ƙyar ya lallaɓa ta ɗan kwantar da hankalinta, a haka suka rabu zuciyoyinsu babu daɗi. Bayan Rumaisa ta gama cika shi da kayan arziƙi. Sun cigaba da soyayya kamar babu gobe ta waya, Rumaisa ta ɗauki dukkan yarda da k'auna ta damƙa wa Yusuf. Rumaisa macece mai kirki da addini da sanin ya kamata, matsalar ta ɗaya tana da zazzafan kishi, wanda wannan kamar a jinin larabawa yake. Tana mugun kishin Yusuf sosai, a kodayaushe cikin nanata masa kar ya ci amanarta take ko ya kula wata mace bayan ita, zuciyarta ba za ta ɗauki hakan ba, sannan ta yi masa alƙawarin tana nan tana jiran shi, ko shekara nawa zai yi kafin ya kammala karatunsa za ta jira har ya gama su yi aure. A tarayyar su ba ƙaramin kuɗi ta ba wa Bulama ba, duk da a zahiri yana nuna mata ba ya son ɗawainiyar da take shi amma ba ta fasawa. Lokaci ɗaya Bulama ya fara samun kuɗi, ya saya Mota da abubuwan more rayuwa. Inna ta san da zaman Rumaisa, amma ba ta san soyayya suke da Yusuf ba, a yadda ya faɗa mata abokiyar kasuwancinsu ce kawai suka saba da ita.

Bayan kammala karatunsu da N.Y. S.C Ta turo masa kuɗin jirgi ya tafi Dubai ya ɗora karatu, Rumaisa ce ta ɗauki nauyin karatun da gurin zamansa da abin da zai ci da komai na buƙatun rayuwa. A lokacin Rumaisa ta sanar da danginta Yusuf take so, wanda a karon farko suka ce ba su amince da wannan maganar ba, duk larabawa da ƴan'uwanta da suke son ta, ta rasa wa za ta ce za ta aura sai bak'ar fata ɗan Nigeria. Jin haka ya sa Rumaisa shiga cikin tashin hankali da damuwa, ta dinga koke-koke da roƙon su akan su amince, ita a haka take son Yusuf ko ma ɗan ina ne, amma suka ce ba ta isa ba, tun wuri ma ta rabu da Yusuf kafin su saka a ɗaure shi. Mahaifiyarta ce kawai ta goyi bayanta a lokacin, duk da ita ma ba ta so, amma tausayin 'yarta da ƙaunar ta ya sa take supporting ɗinta. An yi badaƙala da ja'inja ba kaɗan ba tsakanin dangin mahaifin Rumaisa da mahaifiyarta kafin su amince ta auri Bulama, amma sun ce babu ruwansu duk abin da ya biyo baya mara daɗi kar ta neme su. Ba a yi Auren ba sai da dangin mahaifiyarta suka zo Nigeria suka ga asalin Bulama, shi kuma ya yi cike-ciken takardu na yarjejeniya a Dubai ɗin. Al'amarin ya ba wa kowa mamaki a Adamawa, musamman Inna da Murja, Yusuf da auren Balarabiya, abun kamar almara.
Chapter 129 · 0% Book details