Sashe 55
Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Look up" yai maganar yana sake tsareta da idanunsa.
Yayi ajiyar zuciya yace "Shikenan, ba gaisuwa ma, ko ba ki yi murna da zuwana ba?"
Ta girgiza masa kai.
"Talk mana, ya kike mini rowar muryar ta ki".
"Ina wuni".
A shagwaɓe yace "gaskiya sai kin kalleni".
Murmushi ne ya suɓuce mata, har sai da ta rufe bakinta tana dariyar.
Yace "Na baki dariya ko? In dai ni ne za ki sha shagwaɓa, dan shagwaɓaɓɓe ne ni, the only son of his parents, dan haka sai kin yi haƙuri".
"Ba ka da ƙanne?" Ta tsinci kanta da yi masa tambayar, ba tare da ta shirya ba.
Ya yi murmushi ya ce "Ni ka ɗai ne, shiyasa Aka takura mini in yi Aure, ko iyayena saga jikokinsu, ban yi planing ɗin yin Aure ba yanzu Abra, na fi son mai da hankalina akan aikina sosai, saboda yanayin aikina na rashin zama guri ɗaya, amma ina ganinki komai nawa ya canza, ni ban ma zaci zan iya soyayyar ba, dan ban taɓa yi ba, shiyasa na ke jin tsoro, Allah ya sa kar wani ya yi mink kutse" shiru Abra tayi ba tace Komai ba.
"Angel" ta É—ago ta kalleshi.
Yace "Say something mana".
"To me zance?" Yadda tayi maganar ne, cikin halin na ta na shagwaɓa ya sa ya sake ƙure ta da ido.
"Abra kina son Adnan?".
Jin Maganar ta yi a bazata.
"Ki gayamini, ba na son doguwar magana, amma saboda ke sai surutu na ke, duk na gaji, kuma kin ƙi yin Magana".
"Ba ka sha ruwan ba" Abra ta faɗa tana ƙoƙarin basar da Maganar da yake yi.
"Ni ba ruwa zan sha ba, ki gaya mini idan kina so na?".
Tura baki tayi, ta ƙi magana, sai ma ta nuna kamar ya takura mata.
Hannayenta ya sake haɗewa a cikin nata, yana ƙurawa fuskarta ido, "Abra talk, do you Love me?"
ÆŠago fararen idanunta ta yi tace "ka sakar mini hannuna".
"Sai kin bani amsa tukuna" wata irin kunya ce ta mamaye Abra, ga kwarjini da yayi mata.
"Shikenan, bari in tashi in koma, in gayawa Abba na kince ba kya sona" yai maganar yana ƙoƙarin tashi tsaye.
"A'a nifa ba haka nace ba" tai maganar kamar me koyon magana".
"To me ki ka ce?".
"To ni kunya na ke ji"
Adnan ya zauna yace "Na rufe idona, gaya mini".
"A'a ba Yanzu ba"
"Sai Yaushe?".
Tace "in ba ka nan" murmushi yayi, gaba É—aya yarinyar ba ta da wayo.
Ya ce "Shikenan, tun da kin mini wayo. Kin yi kyau sosai kamar in tafi da ke gidana daga nan".
Lumshe idonta tai, ta na jin daÉ—in yabonta da yake yi.
"My wife, ina Faris ne?"
Murmushi tayi tace "ya tafi ball"
"Da alama, dan da yana nan wataƙila tare zaku zo zancen"
Ba ta san lokacin da dariya ta ƙwace mata ba, ƙasan zuciyar ta na fargabar kar ma Salman ya dawo ya tarar da Adnan, dan zai iya ɓata mata rai, kuma ga Adnan ba sa'an Faris ɗin ba ne.
"My wife, zuba mini ko ruwan ne in sha".
Ba musu ta fara ƙoƙarin zuba masa ruwa, ya zuba mata ido yana kallon yadda take komai a nutse.
"Which tribe are you?" Ya tambayeta.
Abra ta É—an yi Jimm sannan tace"Hausa Fulani".
"I doubt" ya faɗa a taƙaice.
Tace "Why?".
"You are very beautiful My Wife, kamar ba kya jin Hausa ma, gaskiya zan so in ga Abbi da wuri, kar wani ya rigani, a sa ranar Aurenmu nan kusa".
Zaro ido tayi tace "Aure kuma?".
"Yes my dear, ko ba kya sona ne?"
Jiki a sanyaye tace "Abbi ba ze mini Aure yanzu ba, ni karatu na ke so".
Murmushi yayi bece komai ba, ya kai ruwan bakinsa yana sha, idanunsa akan Abra.
Hannunsa ya miƙa ya riƙo ɗan ƙaramin hannunta cikin nasa, yana ɗan murzawa a hankali, Abra tai tsuru-tsuru.
Adnan yace "kinga yadda ki ka haskani, nifa cewa Hajiyata nai zan Auri balarabiya, zaki Auri baƙi?".
Zame hannunta tayi daga nasa tace "bari in barka kaci Abinci".
"A'a zauna inci ina kallon ki, Abbi yana nan ne?".
Abra tace "A'a".
"Ok na gaisa da Maman kan in wuce".
Adnan ya ci Abinci yana ta santi yana yabawa Abra, yau gaba ɗaya Abra Adnan mamaki ya bata, farkon mu'amalarsu ta ɗauka ba shi da mutunci, amma yau ta ga saɓanin abunda take tunani.
Ya ce ta kira masa Maminta su gaisa, Abra ta ji daÉ—in hakan, dan dama a takure take.
A falo ta tarar da Hajiya Na'ima, ta kalleta tace "ya na ganki kamar korarriya?".
"Mami wai gaishe ki ze yi".
Hajiya Na'ima tayi murmushi tace "Masha Allah, babu laifi, amma dai ba zuwa ki kayi kina wannan zazzare idon ba, kamar wadda za'a kashe".
"Mami cewa yai wai sai na gaya masa idan ina son sa".
"To ke kuma sai ki ka ce masa me?".
"To ai Mami kunya nake ji".
"Kunya, waike yaushe zakiyi wayau, kamar ba mace ba, sam baki da wayo, in kika ce kina son sa gutsurar ki zai yi?"
Shiru Abra tai ba tace komai ba.
'duk jarabarki da gidan nan dai, dole kiyi aure ki bar shi, gara tun wuri ma ki san abun yi.
Ki je ki ɗakko mini mayafi na, ki shigo da shi". Abra ta kaiwa Mami mayafinta, tana tunanin tayaya za ta gayawa Adnan wai tana son sa?.
Haka taje ta taho da shi falon.
Tun da yai Sallama Na'ima ta ƙare masa kallo, Abra ba ta fi iya ƙirjinsa ba, dogon namiji ne, duk da baƙi ne amma yana da haske, gashi Kyakywa Masha Allah.
A ranta tace "taɓ, wannan ya za tai da shi, oho mata ma koma dai menene sai ta bar mini gida kawai'.
Suka ƙarasa falon, Adnan ya kame a kan kujera ya ɗan sunkuya ya gaida Hajiya Na'ima.
Cikin mutunci ta amsa ta ce "Kai ne sirikin namu?".
Adnan yayi É—an murmushi yace "Eh ni ne".
Ta ce "Masha Allah, ya sunanka?"
"Adnan Aliyu Matawalle".
"Madalla, insha Allah idan har dagaske ka ke, in megidan ya dawo, za'a sanar masa".
Adnan yace "Nagode sosai da sosai, kuma insha Allah ni da gaske nake, da zarar an bani dama zan turo magabatana ayi magana".
Zaro ido Abra ta yi, Hajiya Na'ima tai wurga mata wata irin harara. Wadda ta sa Abra shan jinin jikinta.
Nan dai ta gama yi masa tambayoyi, duk ya amsa mata, sannan suka yi sallama Abra ta tafi raka shi.
Har gaban motarsa ta raka shi, sai dai kanta a ƙasa ba ta iya cewa uffan.
A jikin motar ya tsaya yana cigaba da kallon yadda dressing ɗin jikinta ya karɓeta matuƙa "My wife, gashi zan tafi, amma ba ki gaya mini abunda ke ranki game da ni ba".
Murmushin da ya zame mata É—abi'a, shi ta cigaba da sakar masa.
Adnan yayi ajiyar zuciya yace "Yaushe zan dawo?"
"Gobe" ta bashi amsa.
Murmushi yayi yace "Lallai kin kamu da son ɗan baƙin mijin nan na ki, tun da har kike son in dawo gobe".
ÆŠauke kai tayi, kamar ba ita tace ya dawo goben ba.
"Wai Nikam da wa kike kama ne, a tsakanin Mami da kuma Abbinki?".
Tace "Da Faris nake kama"
"Shi Faris É—in da wa yake kama?"
"Da ni" ta bashi amsa.
Dariya yayi yace "da alama zan sha fama, haryanzu kina fama da yarinta, zan koma My Angel, insha Allah zan dawo in ga Abbi, nan kusa nake son muyi Aure"
ÆŠan yamutsa fuska tayi, ta kau da kai gefe.
"My wife, ya naga kin haÉ—e rai haka, ko ba kya sona ne?".
Ta girgiza kai, yace "to meyasa kika haÉ—e rai?"
"Makaranta fa" tai maganar idonta na tara hawaye.
A ransa ya ce 'lallai wannan yarinyar an shagwaɓata da yawa, komai kuka'
"To ai zaki cigaba da makarantar ki".
"Ni ba na son in tafi in bar su Abbi da Faris".
Yace "idan na Aureki sai in ginawa Faris ɗaki a gidan, tun da ba zaki iya rayuwa babu shi ba" yai maganar cikin gatse, dan ya fara ƙuluwa da yawan zancen Faris ɗin nan.
Ya saka hannu a aljihunsa ya ɗakko bandir ɗin kuɗi ya miƙa mata ya ce "gashi nan, kwalliya tayi kyau, Abinci yayi daɗi sosai, ga wannan kya saka a jakarki".
"A'a ka barshi nagode".
"Ba'a yi mini musu ai, ki dena mini musu bana so, karɓi"
Ta sake girgiza kai a karo na biyu.
"Ki karɓa bana son musu" yai mata wata razananniyar tsawa, wadda sai da ta ruɗe gaba ɗaya, ta karɓi kuɗin ba shiri jikinta yana tsuma.
Ya buÉ—e motarsa ya shiga ya zauna, ya kuma É—agowa ya kalleta, kamar ba shi yayi mata tsawa yanzu ba ya ce "Ina sonki Angel, ki kula mini da kanki, I will call you when I reach home" ya kashe mata ido É—aya, ya ja motarsa ya nufi barin gidan.
Ta jujjuya uban kuÉ—in da yake hannunta, ta koma cikin gida.
Littafin nan na kuɗi ne ₦300 NE
Via 0116886423Â Sulaiman Na'ima s union Bank. Idan katin waya ne mtn na 500 idan transfer ne É—ari uku kacal.
Evidence of payment 07063065680 ko 09047871750
Part É—in Hajiya Na'ima ta wuce, ta tarar da ita a bedroom.
Tana ganin Abra tace "Lallai Yarinya kin iya zaɓen miji, bari Abbin ya dawo, a san abun yi".
"Mami nifa bana son Aure Yanzu".
Sheƙeƙe Hajiya Na'ima ta kalleta tace "Au zaman jiranki za ai har sai kin shirya Auren? Ko kuma jiƙaki za muyi a ruwa mu sha? Aure kuwa dolenki ba bu fashi".
Jiki a sanyaye ta miƙawa Mami kuɗin da Adnan ya bata.
Ta kalleta tace "wannan kuma fa?"
"Bani yayi" tai maganar a sanyaye.
"Roƙarsa ki kayi ko?" Da sauri Abra ta girgiza kai tace "A'a Mami, wallahi ban roƙe shi ba, cewa yayi dole sai na karɓa".
Na'ima tace "Shikenan, ajiye mini su a kan side bed".
Ta ajiye mata kuÉ—in ta juya ta bar É—akin.
A ɗakinta kuwa, wayarta ta ɗauka ta duba, ta tarar da saƙonnin unknown ɗinta.
Murmushi tayi ta fara yi masa reply, daga bisani kuma saƙon dodonta ya shigo wayar, wato Adnan.