← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 145

Sashe 67

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"But this is not fair Daddy, yaya mutum zai idan bai da kuÉ—i gsky ana kulawa wanda ya taimaki wani sai Allah ya taimake sa" kallon Meenal Daddy ya yi kafin ya ce.
"That's why na ware ɓangaren marasa ƙarfi ana musu komai as voluntary"

Yana zaunar da itace a office ɗin ya fito da sauri yana haɗa kan Likitocin da nurse's ɗin ya ce. "Duk wanda suke reception a duba so kyauta don't make any mistake" kamar yasan Meenal zata zaga asibiti ganin komai lafiya wasu sai godiya suke ta ƙara gasgata girman tausayin Mahaifinta.

A hankali lokacin ya fara juyawa, satittika suka fara zama kwanaki har Ubangiji ya kawo satin bikin Abra Khamal Khamis da Sp Adnan Aliyu Matawalle. Shiri ake da ga ko wanne ɓangare, abinka da masu kuɗi sai ka rasa wanne ɓangare ne ya fi ji da bikin. Gefen Abra abin ba sauƙi ta rame sosai Kullum cikin kuka ta ke, gaba ɗaya ta tashi hankalinta akan Salman, wanda ya sa Ammi ta ɗauke ta zuwa can gidanta a can ake mata gyara jiki. Sp Adnan ango Kullum yana tare da amaryarsa a waya yana yin iya bakin ƙoƙarinsa wajan ganin ya faranta mata, gefe guda kuma har lokacin Abbi bai dawo ba, Khairy sai shige da fice suke domin sun haɗa plain na dinner a ɓoye ita da Usman da su Fayyad.

The day.
Yau ya kama ranar juma'a wanda ya yi dadai da ranar da za'a fara biki wato Kamu. Tun safe aka fara zuba decorations a harabar gidan Abbi sai ka É—auka babban hall aka kama sbd tsarin wajan. Har yamma babu amarya babu labarinta, Hankali ta she Mami ta kira Khairy ta ce.

"Ummulkhairy ina Abra?"
Khairy da ke gidan kwalliya ta ce. "Mami ina gidan kwalliya Abra ma tana gidan da za'ai mata kwalliya"

"Ok call her immediately"
Katse kiran ta yi, khairy ta kira number Abra a kashe hakan ya sa ta kira number mai make up É—in tana É—auka ta ce.
"Hello don Allah Abra fa?" Mai make up É—in ta ce "Tun 3 aka gama mata kwalliya na ce ta jira ta ce zata da ganta yanzu wajan 5 ake nema na yamma tayi kusan 2hours da tafiya"

A fili Khairy ta ce. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un kanan dai ta gudu kamar yadda ta ce.....

Littafin kuɗi ne,biya ₦300 via 0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank... Idan katin waya ne zaka Turo 500 shaidar biya 08081012143
[10/10, 4:17 PM] Abk: Jiki na rawa, Khairy ta kira Mami tana salati tana salallami, Mami ta É—aga wayar ta ce "Ya aka yi? Ta na ina ne, mutane sun fara taruwa fa?".

Khairy murya na rawa ta ce "Mami na kira mai kwalliyar ta ce mini tun uku, aka gama kwalliyar, kuma ta tafi".

Mami ta ce "Ta tafi taje ina?"

"Mami Wallahi ban sani ba, ba guri É—aya muka je kwalliyar da ita ba, ni gurin da naje daban".

Mami ta ajiye waya tana faÉ—in "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, yarinyar nan gidan ubanwa ta tafi ne? Ace an gama kwalliya tun uku amma har haÉ—u da rabi ba ta iso gida ba, ga mutane sun fara taruwa".

Anty suwaiba ta ce"Allah yasa ba guduwa ta yi ba".

Mami ta zare ido ta ce "Ta gudu ta je gidan uban wa? Lallai ma yarinyar nan".

Abu kamar wasa, ba Abra babu dalilinta, tun ana maganar ƙasa_ƙasa, har mutane suka fara jin halin da ake ciki.

Abokan aikin Adnan ne, suke ta shiri cikin shigarsu ta police, domin dai za'a yi parrate na ban girma ga Adnan da amarayarsa.
Usman ne ya kalli Adnan da ke ta haÉ—e rai ya ce "Wai haÉ—e ran me kake ne?".

Adnan ya ce "Am jealous ne, duk wannan garadan sai kun je kun kalle mini mata".

Aminu ya ce "Kai dalla ware, ai kaima gardin ne, sai kace a kanka aka fara Aure, ko da yake tsiyar mutum ya zama tuzuru kenan, duk sai ya fara behaving abnormal".

"Meye banbancina da kai? Har gara ma ni yanzu zan shige daga ciki, kai kana waje".

"Nima ina hanya ne" Usman yayi Maganar yana murmushi.

Daga haka suka kammala shirinsu, suka fara haramar tafiya gidansu Abra.

Granny ce ta shiga sashin Na'ima tana faɗin "Ke Na'ima, wai wace Maganar banza nake ji ne? Wai kamar Ana Abra ta ɓata, gidan ubanwa ki kai ta?"

"Haba granny, Ina kuwa zan Kai ta, daga zuwa kwalliya ba ta dawo ba".

"Ƙarya ki keyi, ana Magana kina wani ƙifta ido kamar ta Allah, ki fito da yarinyar nan duk in da ki ka kaita, kan in samo madoki in shemeki a gurin nan".

Ammi ce ta ce "Granny ki yi haƙuri, ya za'ayi ta aikata haka ga 'yar ta, Yanzu dai muyi ta addu'a, kuma a kira shi angon a sanar masa dan a san abun yi".

Granny ta ce "Wai ke Yaushe zaki gane kan makircin wannan yarinyar ne? Ai duk abun da akace tayi babu mamaki, yau duk abun da za'ayi sai an nemo mini jikata. Amm ke nace ina tabarau na ne? in ƙarewa wannan mara Kunyar kallo, in kalli idanunta sosai, dan ni idan na kalli idon mara gaskiya ina gane shi".

Ammi ta ce "Glass É—inki yana in da ki ka yi salla, amma dan Allah ki dena wannan maganganun, bari a san abunyi, ko a tura wasu gurin mai kwalliyar".

Na'ima kuwa iya ƙuluwa ta ƙulu, ji take kamar ta rufe Granny da duka, shegiyar tsohuwa hayyataciya, sai tsawon rai kamar dabino, ta ƙi mutuwa kuma kullum cikin rikici take, tsawon shekarun da Na'ima tayi tare da Khamal Granny ba ta ƙaunarta sam.

Gida ya rikice ana neman Abra, ita kuma Granny ta rikice tana neman tabarau, ta ɗora da masifar cewa bayan sace Abra da Na'ima tayi, ta kuma sace mata glashinta, saboda baƙin hali.

Anty Suwaiba ta ce "Wai ke Na'ima ba wani mataki da zaki É—auka a kan wannan sokuwar tsohuwar, shegen surutun tsiya kamar an jefeta a ka?".

"To ni ya zan yi da ita? Wannan kaidinta ya fi yadda kike tunani, yanzun nan za ta ƙullawa mutum sharri.

ÆŠakin Salman Granny ta nufa, tana cigaba da zage Na'ima, Ammi ta ce "Granny me zaki yi a nan kuma?".

"Tabarau na nake nema".

"To mai ze kai glass É—inki nan kuma? Na ga tunda muka zo baki je nan ba".

"A'a, ance idan raƙuminka ya ɓata ka neme shi har kura tandu, yo na sani ko wannan algungumar ta yi garkuwa shi ta kai ta ɓoye" ta ƙarasa Maganar, tana nufar ɗakin Salman.

Sai dai tana shiga ɗakin, ta ƙwala uban ihun da ya janyo hankalin 'yan biki.

"Gata nan ku zo gata!" Ta yi maganar cikin ihu.

Su Ammi na zuwa, suka tarar da Abra a zaune, fuskarta sharkaf hawaye.

Ashe tun bai fi uku da rabi ta dawo gida ba, ta shiga ta ƙofar baya, tabi ta kitchen ta shige ɗakin Salman abunta, kuma ta kashe wayoyinta.

Ammi ta ce "Abra, dama kina nan ki ka ɗagawa mutane hankali? Kuma kalli duk kin fara ɓata kwalliyar".

Cikin kuka Abra ta ce "Ammi Faris É—ina, zan yi Aure baya nan, dan Allah Ammi kice musu na fasa Auren nan a dawo mini da Faris É—ina".

N'a'ima a fusace ta ce "wannan wane irin sakarci ne haka Abra? Mun tara mutane kina neman ki bamu Kunya? Kawai kin É—agawa mutane hankali".

"Mami ni bana son Auren nan na fasa, dan girman Allah Ku dawo mini da ɗan uwana" tayi maganar tana ƙoƙarin cire ɗaurin kanta, ga numfashinta da ya fara sama.

Ammi ta girgiza wa Na'ima kai, alamar ta dena yiwa Abra faÉ—a.

Granny ta ce "Ji min 'ya da wauta, ke yanzu sai ki fasa Auren, aikuwa da kin yiwa kanki kutunguilar tsiya, hmm jiya ba yau ba tsohuwa ta tuna kwanan turaka, yarinya karki cuci kanki" Granny ta yi maganar tana watsa guntun goronta a baki, ta bar É—akin, murmushi Ammi ta yi, Granny ba ruwanta haka take sakin 'yan maganganunta idan ta raya mata".

Ammi ta maida hankalinta kan Abra, ta din ga yi mata Nasiha tana rarrashinta, ƙarshe sai da aka kira Abbi video call, shima yayi ta rarrashinta, Sannan ta haƙura.
Aka samo wata mai kwalliyar ta gyara mata kwalliyar da ta fara ɓatawa da hawaye.
Na'ima ma haÉ—awa tayi cikin wani rantsatsten leshi fari da golden, tun daga wuyanta zuwa yatsunta gwal ne.

Hakan yayi daidai da ƙarasowar Adnan da da abokansa, haka zalika mota mota na 'yan uwan Adnan ɗin suka hallara a ƙatuwar harabar gidan Major Khamal Khamis, wadda akai matuƙar ƙawatawa.

Mami ce da kanta ta kamo hannun Abra ta fito da ita daga cikin gida, duk da kanta a sunkuye yake, ta rufe jikinta da mayafi, amma hakan be hana Adnan tsinkayen farar fatarta da ta sha gyara ba.
Nan masu police band suka sauke gangunan su, suka fara bugawa domin gabatar da parrate na ban girma ga Ango sha guɗa Sp Adnan Aliyu Matawalle, da matarsa gimbiya Abra Khamal Khamis, abun na masu ɗamara ne, dan haka parrate ɗin ya ƙayatar matuƙa, tare da crossing sword da aka gabatar duk dan murna ga amarya da ango.
A ka zo ɓangaren kamu, a kama amarya ta buɗe fuskarta, ƙanwar Hajiyar Adnan, ta ce sun biya dubu ɗari biyar a buɗe musu fuskar Amarya.
Nan wasu suka shiga tafi, yayin da Mami ta ce "ita dubu ɗari biyar yayi kaɗan". Ammi ce tsawatar dan kar ayi halin ƙaranta.
Nan aka shiga gudanar da shagali, bayan Abra ta buÉ—e fuskarta, wanda ba su santa ba, suka dinga jinjina kyawunta, wasu kuma suna gulmar ya za tayi da Adnan, dan da kaÉ—an ta wuce cikinsa.

"Sweetheart,yau ranar farinciki ce, amma ya naga kamar za kiyi kuka?" Adnan ya faÉ—a a saitin kunnenta.

"Wani farinciki bai taɓa riskata, Faris baya kusa da ni ba, sai a wannan lokacin, wannan ne karo na farko, ban taɓa tunanin Faris ba zai kasance da ni ba, Ranar Aurena akan high table, ana mana hotuna da ni da shi da angona ba, sai dai....." Hawaye ne suka fara saukowa da ga idanunta.
Chapter 67 · 0% Book details