← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 145

Sashe 49

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"I'm toking to you my friend." Ya faÉ—a cikin tsawa.

Zabura ta yi ta ce. "Mun zo ganin wani mutumi ne?" Ya ce. "Wane wanin? Daga Kadunan kuke yanzu?"

"A'a, muna zaune a school hostel ne, daga can muka zo nan."

Jinjina kai ya yi cikin nazartar ta ya ce. "Okay, cigaba da bayani, gurinwa kuka zo?"

Cikin rawar murya ta ce. "Wani tsohon Soja ne, ita ƙawar tamu da aka kashe muka rako nan Abuja, don ta gana da shi akan wani abu." Tattara hankalinsa gabaɗaya D.P.O ya yi a kanta ya ce. "Wanne abu ne wannan da kuka taho tun daga Kaduna har Abuja saboda kawai su yi magana a kansa?"

Baby tana hawaye ta ba shi labarin duk abun da ya faru tsakanin Ihsan da General Ibrahim, ganin ba ta da mafita, kuma tana son ta kuɓuta daga zargin su da ake yi. D.P.O ya ce. "Kin tabbata abun da kike faɗa mini gaskiya ne?"

"Wallahi gaskiya ne ranka ya daÉ—e, kuma dalilin da ya sa ma ba mu fita tare da ita ba saboda zai zo su haÉ—u a lokacin." D.P.O ya ce. "Kuna da tabbas É—in ya zo sun haÉ—un bayan kun fita? Kuma menene shaidar ku akan abun da kika faÉ—a." A raunane Baby ta ce. "Eh, lokacin da ya zo ta kira mu ta sanar mana zuwansa cikin murna, dan muna tunanin ya zo ya ba ta kuÉ—in da muka nema ne daga hannunsa, shaidar kuma akwai short video na tattaunawarsu ita da shi akan cikin jikinta a cikin wayoyinmu, wanda muka yi masa barazanar da shi."

Numfashi D.P.O ya sauke tare da shafa kansa ya ce. "Ya sunan shi Sojan?"

"General Ibrahim A.M"

"What? General Ibrahim A.M? Are You sure?" Ya tambaya cikin shock.

GyaÉ—a masa kai ta yi cikin tabbatarwa.

Girgiza kai ya yi ya ce "Oh My God!"

Duban jami'in da ya kai Janna cell ya yi ya ce. "Officer."

"Yes sir." Ya faɗa tare da ƙamewa.

"Ka shigar da wannan ciki ka fito É—ayar."

A ruɗe Baby ya ce. "Yallaɓai dan Allah ka sallame ni tunda na faɗa maka gaskiyar abin da ya faru, wallahi ba mu muka kashe ta ba, ba mu.."

"Shut up, tashi mu je." Officer ya buga mata tsawa da faɗin haka. Kuka ta fashe da shi tare da miƙewa ta yi gaba.

Exactly abun da Baby ta faɗa shi Janna ta faɗawa D.O.P, bayan ta gama yi masa jawabin ya bayar da umarni aka kawo masa wayoyinsu da aka karɓa, ya cewa Janna ta ɗauki tata ta cire key ta nuna masa videon tattaunawar Ihsan da General Ibrahim. Da wannan damar Janna ta yi amfani ta ɗora videon a social media in seconds, sannan ta miƙawa D.P.O wayar.

Bayan ya gama kalla ya dubi wani police dake tsaye a gabansa ya ce. "Inspector, a cigaba da tsare yaran nan har zuwa lokacin da za mu gama bincike, sannan a je a taho da General Ibrahim A.M, yarinyar da aka kashe kuma a san yanda za a yi iyayenta su samu labari, and lastly aje a zo mini da Manager na hotel É—in da abun da ya faru a ciki yanzu, a kuma bincika CC TV camera domin a tabbatar da General Ibrahim ya je hotel É—in a yau ko akasin haka."

"Done Sir." Inspector ya faÉ—a tare da sara masa.

Bayan ya fita D.O.P ya dubi Janna dake ta kuka ta ce. "Wannan ya isa ya zama izna a gare ku da masu hali irin naku, yara ƙanana da ku iyayenku sun tura ku karatu amma kuna irin wannan rayuwar, yanzu wa gari ya waya? A misali idan General ɗin ne ya kashe ta hakan ya isa ku gane ba ku da wata daraja da ƙima a idanun irin waɗannan Mazan da kuke bi, ba su ɗauke ku a bakin komai ba, sun mayar da ku kamar ledar pure water saboda yawan da kuka yi a gari. Ya kashe ta ne saboda ya tsira da mutuncinsa kar abun da yake aikatawa ya fito fili, kuma a lokacin da ya kashe tan yana fita idan ya haɗu da wata ɗaukarta zai yi ya je ya sheƙa ayarsa da ita hankali kwance, ita kuma wannan ya gama da ita, da ita da Dabba duk matsayinsu ɗaya a gurinsa. Ina baki misali ne kawai ba wai ina faɗa dan ya aikata ba, dafatan kin fahimta?"

Janna da kanta ke ƙasa tana hawaye ta gyaɗa masa kai. Girgiza kai ya yi cikin takaici ya ce. "Allah ya shirya." Sannan ya bayar da umarnin a mayar da ita ciki.

General Ibrahim A.M ne zaune a gaban kujerar gaban table ɗin D.O.P, cikin shiga ta kamala, ba zaka taɓa cewa shi yake aikata baɗala da Ƴaƴan cikinsa a bayan fage ba. Bayan sun gaisa cikin ƙwarewar aiki D.P.O ya ce. "General, muna son za mu yi maka wasu ƴan tambayoyi ne a kan kisan wata yarinya da aka yi mai suna Ihsan Sadam Malali a Aminci Hotel." 

Damm zuciyar General Ibrahim ta buga, amma da yake cikakken ɗan duniya ne kuma ya san ta kan harkar bincike sai ya ce. "D.P.O ni kuma? Wacce yarinya ce wannan? Me ya sa kuka gayyato ni akan kisan ta? Ba na jin ko a cikin familynmu akwai mai sunan da ka ambata balle na yi tunanin ko ina da wata dangantaka ta jini da ita, Ihsan ka ce ko wa?" Cikin nazartar shi D.P.O ya ce. "Bari ka ga hotonta, na san idan ka gani may be ka shaida ta." Bai jira cewar shi ba ya ɗauki wayarsa ya latsa sannan ya nuna wa General Ibrahim pics ɗin fuskar Ihsan da ya cika screen ɗin wayar. Ƙarɓa ya yi ya duba, cikin ɓoye razanin da zuciyarsa take ciki ya ce. "Gaskiya ban san wannan yarinyar ba D.P.O."

"Ko?" D.P.O ya faɗa tare da karɓar wayarsa.

"Ina jin mistake kuka yi ba ni za ku kira ba."

"Kai kuwa za mu kira, saboda bincikenmu ya tabbatar mana da a guest house ɗinka yarinyar ta sauka ita ƙawayenta shekaran jiya."

Cikin maziya General Ibrahim ya ce. "Eh hakan zai iya yiyuwa, saboda akwai abokaina da dama da suke saukar baƙinsu a gidan ba tare da na sani ba, because mun zama ɗaya na yarje musu hakan. Cikin gyaɗa kai D.P.O ya ce. "General please kar ka wahalar da mu ka wahalar da kanka, ka amsa kawai ka san yarinyar nan, in yi maka tambayoyin da zan yi maka, that is all."

"A'a fa, ban san ta ba zan amsa na san ta ne? Da kuka kira ni in zo akan abun da ban sani ba na yi muku musu? Na taso na zo duk da ina gaba da ku a matsayi da miƙami, amma saboda ina girmama kaki da mahukunta ya sa na zo cikin salama ba tare da jayayya ba." General ya faɗa cikin harzuƙa.

"Akan aikina nake General, kuma sanin kanka ne babu ruwan doka da wani muƙami ko matsayi, idan abu ya biyo ta kan mutum ko waye shi dole a tuhume shi, but ba wannan ne a gabanmu ba yanzu, let me show you something." D.P.O ya faɗi haka tare da ƙara ɗaukar wayarsa a karo na biyu.

A ɗarare ta shiga gida zuciyarta cike da tsoron Na'ima, kasancewar Major ba ya gari. Allah ya taimake ta Na'ima ba ta main Parlor tana ɗakinta, ajiyar zuciya ta sauke ta shige ɗakinta. A bakin gado ta zauna tare da ƙurawa wayarta ido, sai dai a zahiri ba wayar take kallo ba, tunanin wanda ya ba ta wayar da kasancewar da suka yi tare na wasu mintuna take tunawa. Har yanzu zuciyarta ba ta daina bugawa ba, ta tsorata sosai da farko, dan wannan ne karo na farko da ta taɓa daɗewa tare da wani Namiji bayan relatives ɗinta. Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke tare da kai wayarta kan hancinta ta shaƙi ƙamshinsa, tun a jikin i.d card ɗinta ta ji tana son ƙamshin, sometimes idan za ta kwanta bacci sai ta ɗauko ta shinshina. Mr unknown ne ya faɗo mata a rai, da sauri ta latsa wayar ta cire password tare da cire ta daga Flight mode ɗin take, kamar jira ake messages suka dinga shigowa. Hannunta har rawa yake wajen dannawa ta buɗe ta karanta. Messages ɗinsa ya kai 15 ta gani, duk na yanda yake tsananin son ta ne da missing ɗinta da ya yi, a ƙarshe kuma sai ya roƙe ta akan ta taimaka ta yi masa reply koda da "Okay" ne, dan ya ji daɗi a cikin ransa. Murmushi ta yi ta tura masa da.

"Hey, How are you."

Message É—in yana tafiya kira ya shigo cikin wayar da sabuwar Number, kallon special Numbern ta tsaya tana yi, sai da ta kusa katsewa sannan ta yi pick.

"Assalamu alaikum." Wata murya mai cike kamala da daÉ—in sauti ta doki kunnenta.

Sai da gabanta ya faÉ—i jin muryar wanda ba ta za ta ba, lumshe ido ta yi a hankali tare da gyara zama ta amsa masa cikin sassanyar muryarta.

"Na kasa cigaba da driving a dalilin kyakkyawar fuskar matata dake ta mun gizo gami da tunaninta da ya addabi zuciyata, shi ya sa na kira ki don na samu nutsuwa, i hope kin shiga gida lafiya?" Ya yi maganar cikin wani irin salo da ya ratsa zuciya gami da ko'ina a jikinta. Shiru ta yi ta rasa me za ta ce, jin al'amarin take wani mai girma a kanta.

"Ba na son ina magana ana ji na a yi shiru" Ya faÉ—i haka a É—an kausashe kamar ba shi ya gama magana cikin kulawa yanzu ba.

Turo baki ta yi kamar yana gabanta ta ce. "I'm sorry, ban san me zan ce ba ne." Murmushi ya yi mai sauti ya ce. "Just say I love you My husband." Waro ido ta yi ba ta ce komai ba. Ya ce. "I'm waiting for you Madam." Nan ma shiru ta yi sai sauke numfashi kawai take yi. Murmushi ya ƙara yi ya ce. "Okay bye, thank you, take care of yourself." Bai jira amsar ta ba ya kashe wayar.
Chapter 49 · 0% Book details