← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 145

Sashe 80

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya dage a kan Mama ba zata tafi yanzu ba, ƙanwar Mama da suka zo tare, wato Hajiya Bilki ta ce ita kam tafiya za ta yi, ta bar yara a gida.

Abra ta bawa Mama da Adnan guri dan su yi hira.

Mama ta kalli Adnan ta ce "My son, magana nake son mu yi"

Ya É—an yi jimm, yayi zaton ko Abra ta gayawa Mama wani abu, ya maze ya ce "To Hajiya".

"Duk da bai kamata in maka katsalandan a lamarin Aurenka ba, amma ni uwa ce, kuma 'ya mace ce, yarinyar nan Abra, ta rame da yawa, na yi imani da Allah idan iyayenta suka ganta haka ba zasu ji daÉ—i ba, dan ba a haka suka baka 'yar su ba.
Kai kuma kalli yadda ka yi wata uwar ƙiba, kai tsaf da kai, na yi magana da ita, amma ba ta ce mini komai ba, sai kuka tana cewa ita gida.
A É—an abin da na fuskanta, kana takura yarinyar nan Adnan".

"Mama takurawa kuma? Me nake mata? Ki tambayeta ni abin da nake mata".

Mama ta ce "Ƙaniyarka, ni zaka mayar ƙaramar yarinya, ai ka gane sarai me nake nufi" sai kuma ya kama sosa ƙeya yana ɗan basarwa.

"Ba ina nufin yi muku shishshigi bane, amma dan Allah a dinga ɗaga mata ƙafa, ramar ta yi yawa".

"To Hajiya" ya amsa cikin jin nauyi.

"Yawwa kirawo mini ita muyi sallama"

Adnan ya kira Abra dan suyi sallama da Mama, amma Abra ta fara kuka ta ce "Mama dan Allah zan biki".

"Abra kiyi haƙuri, na yi masa faɗa, ba yadda za'a yi da aurenki ki bar gidanki ki biyo ni".

"Haba Angel, ya kike haka kamar wata ƙaramar yarinya, me kike so in sai miki? Ku mu fita yawo yau" yayi Maganar yana rungumeta a jikinsa cike da kulawa.

Abar kuwa sororo tayi tana kallon Adnan, suka yiwa Mama sallama, har mota ta tafi.

Yana dawowa ya tarar da ita a falo, ta na ta gyarawa, ya zuba mata ido, tana É—agowa suka haÉ—a ido, sai da ta sha jinin jikinta.

"Shi ne ki ka kawa mahaifiyata ƙarata ko?".

Ta shiga girgiza kai ta ce "Wallahi ban kai mata ƙararaka ba".

"Idan ma ƙarar ta wa ki ka kai mata, ko sani, ba yadda za a yi in sanya kuɗi na in Auroki in kasa karɓar hakkina na Aure, ba dan iya fansa kawai na Aureki ba, na Aureki ne dan ina da buƙatar yin hakan ne. Kuma duk in da baiwa take a ubangidanta yana da iko a kanta, dan haka ba zan fasa ba sai dai ki mutu. Kuma Wallahi ki ka bari wani ya san irin zaman da nake da ke, sai kin gane shayi ruwa ne"

Abra tayi shiru, tana sake jinjina azabar rashin imani irin na Adnan.

Ba ta karaya ba, ta bishi ɗakinsa, ta tarar yana ƙoƙarin shiga wanka, ya kalleta ya ce "Uban me kika biyo ni ki mini".

"Baby alfarma nake nema".

"Ina jin ki".

Ta ƙaraso gabansa ta durƙusa a kan gwiwowinta ta haɗa hannayenta ta ce "Idan kana son ganin Annabin tsira, ka bani wayata, ko ka haɗani da Abbi na a waya, dan girman Allah".

"Annabin tsira insha Allah zan ganshi, wayarki kuma ta tafi kenan, dan ba zan baki waya ki dinga Magana da Wannan mayen naki ba, Suleiman yake ko wa?"

"Dan Allah, ka taimaka magana nake son yi da Abbi na dan Allah" wayar Adnan ce ta fara ringing, ya ɗauka ya duba, yayi murmushin mugunta ya ce "Gaskiya wannan baban naki na riƙo yana ji da ke, dama shine babanki mahaifi, da kin ji daɗi".

Ya gyara tsayuwarsa ya É—aga wayar, suka gaisa da Adnan.

Abbi ya ce "Adnan anya kuwa lafiya, yarinyar nan mahaifiyarta da kkanninta duk sun isheni ba'a samunta a waya, ni jikina yana bani kamar ba ta cikin farinciki, a weekend zan zo in ganta, kai kan ka wayarka ba ta shiga".

"Abbi Abra tana lafiya ƙalau fa, ga ta ma a kusa dani".

"Bani ita maza".

Ya miƙawa Abra wayar jiki na rawa ta karɓa "Hello Abbi na".

"Na'am Babyna, yaya akayi bana samun ki, kina lafiya kuwa?".

"Abbi, Abbina" tayi Maganar tana kuka.

"Ina jinki Abrana, mai yasa kike kuka? Meyafaru ni jikina gaba É—aya ya gama bani babu lafiya" Abbi yayi Maganar a rikice.

"Abbi wai da gaske ba kai ne babana ba?"

Ras!!! Gaban Abbi ya faÉ—i, dan yaji maganar ta ta a bazata.

"Waye ya gaya miki wannan banzar Maganar?".

"Abbi dan Allah ka gaya mini, ba kai ka haifeni ba ko? Wai tsinto ni ka yi ka riƙeni".

"Abra waye ya gaya miki wannan maganar? Naima ce ko?" Abbi yayi Maganar cikin wata irin razananniyar tsawa.

Abra kasa magana ta yi, sai kuka.

Adnan ya fizge wayarsa ya ce "Abbi kaji dalilin da ya sanya na ƙwace wayarta, na kuma hanata wayata ku yi magana, ta isheni da koke koke, ban san a ina ta ji wannan maganar ba.

Ai Abbi bai ba shi amsa ba, ya katse kiran.

Adnan yayi murmushi ya ce "Ina fatan ko wannan rikicewar da Abbin naki yayi, ya isa ya tabbatar miki da ba shine ya haifeki ba, saboda kin gano sirrin da ya ɓoye duk ya rikice, tabbas yana miki so irin na 'ya da uba".

Abra ta ɗora hannunta a ka ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku, waye babana? Dan girman Allah ka gaya mini wanene ya haifeni, suwaye iyayena" ta riƙe hannun Adnan tana Magana cikin kuka.

Shi ba halin da take ciki ne ya dame shi ba, sai yadda ƙamshin turarenta da yadda kwalliyarta suka yi turning ɗinsa on ne suka dame shi, kamar kullum yayi abun da Allah ya nufe shi da yi, duk da halin da Abra take ciki na damuwa da tashin hankali.

"Kaji tsoron Allah, ko tausayin halin da nake ciki baka ji? Buƙatarka ce kawai a gabanka" tai maganar tana kuka.

"Halin da kike ciki ke ya dama ba ni ba, dan haka damuwarki ba zata hana ni jin daÉ—in rayuwata ba.

Mami ta rasa sukuni balle mafita, gaba ɗaya gidan yayi mata faɗi, tana zaune tana ta jujjuya takardar da Salman ya bari, ta kira Anty Suwaiba ko zata samu mafita, bayan ta gama korawa Anty Suwaiba bayani, Anty Suwaiba ta jinjina kai ta ce "Taɓɗijan, shi Salman wannan wane irin hali ne? Daga wannan sai wannan, ki sanar da mahaifinsa kawai".

"Anty Suwaiba ta yaya zan sanar da mahaifinsa, bayan bai san na gayawa Salman É—in cewar bani na haifi Abra ba?".

Anty Suwaiba ta ce "kin ga wannan maganar ba ta waya bace, kinga bana gida amma insha Allah wajen jibi zan shigo gidan naki".

'To shikenan, Allah ya kaimu"

Mami na gama wayar, taji jiniyar motocin sojoji, alamun Major ya sauka a gari.

Mamaki ne ya kamata, ta fito falo, kamar an wurgo shi haka ya shigo a birkice.

Mami ta ce "Yallaɓai lafiya kuwa? Yana ganka a gida yau ba ko sanarwa?". Wani mugun kallo ya yiwa Mami ya wuce part ɗin sa.

Binsa ta yi cikin mamaki "Yallaɓai dan Allah ka gaya mini meke faruwa?" Ko kallon in da take bai yi ba, ya cigaba da abin da yake gabansa.

Da yaga zata dame shi, ya buga masa wata razananniyar tsawa, wadda ba shiri ta bar masa É—akin, tana mamakin meke faruwa.

Kusan awanni biyu da dawowar Major, ya sami Na'ima a É—akinta yana binta da wani mugun kallo ya ce "Na'ima, ubanwa ye ya sanya ki gayawa Abra cewar ba mune muka haifeta ba?"

Dafe ƙirji tayi tana faɗin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ita Abran ce ta ce maka ni na gaya mata?".

"Shut up! Sai ta gayamini cewar ke ce? Ta kirani tana kuka cewar wai ba mu muka haifeta ba, shiyasa mijinta ya ƙwace wayoyinta saboda kar ta kira ta ɗaga mini hankali? Waye ya sa ki gayawa Abra am talking to you".

"Wallahi ni ban gaya mata ba, bani bace ba"

"Ashe har kin manta sharaÉ—in dana sa miki akan, daga ranar da wani ya san bamu muka haifeta ba, ta dalilinki a bakin Aurenki ba? Ashe zaman haramci muke yi, ki tattara ki bar mini gida na sake ki, saki É—aya".

"Na shiga uku, baka sakeni tun da ƙuriciyata ba sai yanzu, da girmana har na kai 'ya ɗaki".

"Ƙarya ki ke yi, munafuka"

"Ni kake kira munafuka, a kan laifin da ba......

"Shut up! Kar ki bari in dawo É—akin nan in tarar ba ki tafi ba.

Har ya juya zai fita ya hangi takarda a ƙasan madubi, da irin signing ɗin Salman.

Littafin kuɗi ne,biya ₦300 via  0116886423 Sulaiman Na'ima s union Bank... Idan katin waya ne zaka Turo 500 shaidar biya 08081012143
[10/14, 1:45 PM] Abk: Ɗauke idonsa ya yi daga kan takardar ya juya da niyyar fita amma sai ya ji zuciyarsa na son sanin me takardar ta ƙunsa, ko don yana cikin kewar ɗan nasa ne? A hankali ya juyo ba tare da ya kalli inda Na'ima take ba, wadda ke gunjin kuka kamar za ta shiɗe. Sunkuyawa ya yi tare da kai hannu zai ɗauka, kamar an cillo kibiya daga cikin baka haka ya ga Na'ima ta yi tsalle ta dira a gabansa, da mamaki yake kallon ta bai ce komai ba. Cikin bugawar zuciya Na'ima ta matsar da takardar gefe cikin pretending irin ba ta san ta yi hakan ba. Wani mugun kallo ya watsa mata ya miƙe ya ɗauki takardar ya fara karantawa a zuci.

"Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, na shiga uku!" Naima ta faÉ—i haka a fili cikin tsananin ruÉ—ewa da rawar jiki.

Kallo mai kama da na tsana Abbi yake jifan ta da shi, cikin matuƙar takaici da ɓacin rai ya ce. "Me takardar nan take nufi Na'ima?" Kasa magana ta yi sai rawar baki take tana haɗa hannayenta alamar roƙo.

"I'm asking you Na'ima me kika aikata? Wacce irin soyayya Salman yake nufin yana yi wa Abra?" Ya yi maganar cikin ƙaraji da tsawa, wanda hakan ya ƙara firgita ta."

Cikin rawar murya ta ce. "Don Allah My Man ka saurare ni, wallahi ban aikata abin da kake zargi na da shi ba."
Chapter 80 · 0% Book details