← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 145

Sashe 105

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miƙewa yayi ya fice ya bar mata falon gaba ɗaya.
Ƙwafa hajiya Saudat tayi, ta tashi ta koma sashinta.
Meenal ce ta tarar da Mummy a É—akinta. "Mummy kin gaya masa ya kuka yi da shi?".
"Ni na rasa me yake damunsa, gaba É—aya a takure yake, baya cin abinci ya daina zuwa wurin aiki, ko bacci ba ya iya yi"
"To meya same shi?"
"Ina na san masa, na tambaye shi yaƙi gaya mini".
"To ni dai da kika gaya masa zancen Usman me yace miki? Ya ce su zo É—in?".
"Ina ya saurareni ma, balle muyi maganar"
"Innalillahi, Mummy to jira za suyi har sai ya daina damuwar tukuna? Jira suke fa ya basu lokaci su zi".
"Zan cigaba da yi masa magana, gara a san abun yi".
"Yawwa Mummy, dan Allah ki cigaba da lallaɓa shi".
"Ina jinjina abin da yake damunsa haka, na ga baya wasa da duk abin da ya shafe ki, amma naga yana cikin damuwa sosai".
"To Allah ya yaye masa damuwar ta sa".
Meenal ta amsa da "Ameen".

Salman yana zaune a kan gadon Abra, yana tuna Abubuwa da suka shuɗe, na rayuwar da suka gudanar, tun daga ƙuruciya zuwa girmansu, halayyarta na shagwaɓa, a hankali ya lumshe idanunsa, yana tuna yadda ya dinga wasa da hankalinta a matsayin unkown ɗinta suna hira, lokaci ɗaya rabon Aishatul Humaira ya sanya Adnan ya kutso rayuwarsu, ya rabasu cikin gaggawa ashe rabon ajali ne ya sanya, da shigowar Adnan rayuwarta da Aurensu ba a ɗau lokaci mai tsawo ba.
Hawaye yake sosai, yana ƙanƙame filonta a ƙirjinsa, yana juyi a kan gadonta, kansa har wani irin sarawa yake yi, saboda kuka.

Sai da Abra ta kwana goma da rasuwa sannan aka sallami Adnan daga Asibiti, shima bisa sharuÉ—a da dokokin da likitoci suka shimfiÉ—a, saboda har yanzu baya hayyacinsa, da allurai sun sake shi, yake fara zabure-zabure da kuka shi wurin Abra zai je, a bashi matarsa su tafi. Idan ya É—an watstsake, sai ya dinga tuna cewar rabon da ya ga Abbansa a kansa, tun lokacin da aka kawo Abra Asibiti.
Hajiya Mama ce ke ta cigaba da rarrashinsa da bashi haƙuri, amma ya kasa yarda da cewar Abra ta mutu, lokuta da dama sai ya birkice yace mafarki yake yi.
Kafin su tafi gida, Mama ta ce Adnan suje ya ga 'yar sa, dan bai ganta ba tun da aka haifeta.

Tafiya yake tamkar wanda ya zare, jan ƙafarsa kawai yake yi, Mama na riƙe da hannunsa, wani Cousin ɗin Adnan Aminu na gefensa, jefa ƙafarsa kawai yake, yana kallon Asibitin.

Haka suka je suka nemi izinin shiga wurin da jaririyar take, Adnan ya zubawa jaririyar idanu, Abra ba ta ga abin da ta haifa ba, gashi a hankali kamanninta juyewa suke zuwa na Abra, likitoci suka tabbatar da an kusa cireta da ga kwalba, a É—orata a kan madara, ko kuma idan an samu mai shayar da ita a kafa masa dokokin kula da ita.

"Mama É—aukar mini ita a hoto" Adnan ya faÉ—a idanunsa na zub da hawaye.

Mama ta É—au hoton jaririyar, suka fito daga cikin wurin, zuwa cikin mota.

Tun da Aminu yake bai taɓa ganin abin da ya sanya Adnan kuka ba irin mutuwar Abra, dan mutum ne mai dakakkiyar zuciya, ba komai ne ma yake ba shi tausayi ba, balle a sa ran zai yi kuka.

Wayar Mama ya karɓa, yayi zooming ɗin fuskar Aishatul Humaira, wadda yake yiwa laƙabi da little Abra.

Babban abin takaici shi ne da ka kalli jaririyar ka san jinin Bulama ce, dan a hankali kammaninta suke juyewa irin na Abra, ya tuna lokacin da ya ɗauko Abra daga Asibitin Bulama, tana zubar da jini, saboda halin ko in kula da wasa da rayuwarta da aka yi a Asibitin. Sakin wayar Adnan yayi ya ƙanƙame Mama yana kiran sunan Abra.
Lamarin Adnan ya fara bawa Mama tsoro, amma tai shiru ta cigaba da yi masa Addu'a, har suka je gida yana kuka.
"Mama ku fara kai ni kabarin Abra dan Allah"
Mama ta ce "Adnan ni da ba dani aka kaita ba, ina na san kanarinta, muje gida Abbanka ya kai ka".
"Mama Abba ya san Abra ta mutu ta barni kuwa?".
Mama ta É—an yi jimm, dan ba ta san ta ina zata fara yi masa bayani ba, amma ta basar ta ce "Eh ya sani mana, da shi aka kai ta gidanta na gaskiya ma"
"Mama shi ne bai zo ya ganni ko sau É—aya ba, shine bai bari na ganta ba yaje ya binne ta? Dan ba matarsa ba ce, shi lokacin da matarsa ta mutu haka aka yi masa? Ai shikenan idan na tashi daga baccin na san zan ganta a kusa da ni, ai tare muka kwanta jiya da daddare, har Abincin dare ta yi mana. Idan kuma muna Dubai ne sai inje gidan Abincin Hilal in sayo mana gasashen nama".

Aminu ya ce "Anya Hajiya Adnan ba za a kai shi wurin likitocin ƙwaƙwalwa ba, kar fa abin ya zarce".

Mama ta ce "Bari muje gidan tukuna, idan bai ware ba sai a san abun yi".

Har suka je gida, Adnan surutai yake yi, yayi zancen hankali idan aka jima kuma, ya fara shirme da surutai.

Haka suka isa gida, suna shiga cikin babban falon gidan suka tarar da Abba a zaune, yana duba system ɗin sa, Adnan na ganin Abba ya nufi wurin Abba, ya zube a kan gwiwowinsa ya riƙe ƙafar Abba yana faɗin "Abba, wai da gaske i loose my Abra, Abba ka sa aka binneta ban ganta ba, Abba ka nuna mini kabarinta in ganta kafin in tashi daga baccin" hankaɗe Adnan Abba yayi, ya zame ƙafarsa, ya kalli Adnan cikin tsananin takaici ya ce "Am disappointed on you Adnan, ban san a inda ka kwaso baƙin hali ba, ashe zamanka da yarinyar nan zalintar ta ka dinga yi? Na gode Allah da ba wani ne ya gaya mini ba, da bakinka Allah ya sa ka dinga faɗa, ba wani ne ya gaya mini ba balle in ce ƙarya ne, to kanka ka yiwa, kuma komai aka yi maka a rayuwar nan idan ka barwa Allah, ya gani zai saka maka, amma ina ruwan baiwar Allah da bata san laifin da aka yi maka ba, kai laifi nawa kake wa Ubangiji ya yafe maka? Ka samu yarinya 'yar mutunci mai haƙuri amma ka zalunceta, to ka sani har abada ba zaka taɓa samun yarinya mai haƙuri da kirki kamar Abra ba, Allah yayi mata rahama amma na yi dana sanin shigewa gaba wurin nemawa mutumin banza irinka Aure".

Jiki a sanyeye Mama ta ce "Dan Allah Yallaɓai kayi haƙuri, ka tausaywa halin da yake ciki, likita ya kafa masa dokoki kar ya rasa hankalinsa".

"I don't care, komai ya same shi shiya janyowa kansa, bai shafeni ba, na jinjinawa haƙurin yarinyar duk wannan zaman naku bata tona maka asiri ba, kaji kunya Adnan, kuma ka tattara ka bar mini gida ka koma gidanka kar ka sa in gaya maka wata muguwar Maganar" ƙurawa Abba Idanu Adnan yayi, ko ƙyaftawa ba yayi, kamar mai shirin aiwatar da wani abu.

Bulama kuwa lambar maƙwabcin su Abra, ta jikin File ɗin Asibitinsu ya kira, yai sa'a mutumin ya ɗaga, suka yi arranging zasu haɗu da Bulama.

Bayan haɗuwar ta su ne, Bulama ya sanar masa cewa yana son ya gaya masa alaƙarsa da matar da suka kai Asibiti ranar.

"Matar maƙwabcina ce".

"Yanzu ina maƙwabcin naka yake?".

"Ai matar tasa ta rasu, shi kuma yana Asibiti babu lafiya".

Wata irin mummunar faÉ—uwar gaba ce ta ziyarci Bulama, wani irin gumi ya shiga tsatstsafowa a goshinsa, wata irin nadama da tashin hankali suka mamaye shi.

A saɓule ya ce "Ko zaka kwatanta mini Asibitin da yake?". Nan ya kwatanta masa Asibitin nan dai da yabi Adnan amma ya ɓace masa. Ya gaya masa har room ɗin, Bulama yayi masa godiya ya tafi.

Adnan fa sai abin da ya ƙaru, gaba ɗaya ya ƙara birkicewa, dan an haɗasu da likitan ƙwaƙwalwa, saboda kar a rasa hankalinsa, Mama kuma nata rarrashin Abba a kan, ya sassauta fushin da yake da Adnan, kar abun yayi masa yawa. Ba ya cin komai sai ruwa sai kuka, wasu lokutan idan ya birkice sai dai ayi ta masa allurar bacci.

Abbi da Mami tare da Salman, suka zo garin Kaduna domin karɓar jaririyar Abra, dan lokacin cirota daga kwalba yayi, Mami ta dage a kan cewar ita za'a bawa Little Abra ta riƙe.

Abban Adnan ya koma wurin aikinsa, Adnan kuwa ba shi da lafiya da cikakken hankalin da za'a tambayi ra'ayinsa a kan riƙon Aisha.

Tare da Hajiya Mama suka tafi Asibitin, suna nan tsaye suna ƙoƙarin shiga, Bulama ya fito daga cikin Asibitin, neman Adnan amma ya tarar an sallame shi.
Salman ne yabi Bulama da ido, ko ƙyaftawa ba yayi amma ya kasa Magana.

Na kuÉ—i ne a biya mu kan a karanta dan Allah
07063065680
[11/3, 6:09 PM] Abk: Har Bulama ya fice daga asibitin Salman bai daina kallon shi ba. Ajiyar zuciya ya sauke ya bi bayan su Abbi da suka wuce cikin kasala, kamar mutumin da Angel ɗinsa ta ɓaci, banbanci su kawai shi Namiji ne ita mace. Bai ɗauki hakan a matsayin wani abu ba, saboda yadda Abra take masa gizo akan duk abin da zai ɗora idonsa a kai sai ya ga fuskar Abra tana yi masa murmushi. Wasu hawaye masu ɗumi ne suka zubo akan kuncinsa. Cikin raunin murya ya furta. "Allah ya ji ƙan ki Yayata ya gafarta miki."
Chapter 105 · 0% Book details