← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 145

Sashe 144

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Am sorry yaya nayi laifi to" Adnan ya ce "Ba wani sorry kawai ka saka mini matata kuka, ka kiyaye ni fa" a wannan karan drya sosai Salman ya yi cikin farin cikin ganin Adnan da Abra suna zaune lafiya ya ce.
"To Yaya Adnan a yafe mini, amma kada a manta nima fa ba gwauro bane a to" a haka dai suka ƙarasa gidan.
Suna shiga Abra ta tafi da gudu ta rungome Mami tana hawayen farin ciki.

"Yau na shiga uku, wai ke kam komai na kuka ne, ɗaga ni to" Abra ta ƙanƙame Mami tana murmushi ta ce "Mami hawayen farin ciki ne fa"

"To nutsu kada ki samu asara yanzu" Abra ta ce "Asara kuma Mami tame?" Kai tsaye Mami ta ce "ina nufin kada kiyi ɓari irin na ƴar uwarki" Abra ta zauna kusa da Mami ta ce "Ayya Mami ai ni bani da ciki"

"ÆŠan duma ne, zai bayyanar kan shi ai da zarar lokaci ya yi" murmushi kawai Abra tayi.
Adnan ya zauna ya ce "Ina yini Mami?" Ta ce "Allahamdulillah, ya hanya" kansa a ƙasa alamar martabawa ya ce.
"Allahamdulillah!. Allah kuma ya mai da na aike" murmushi kawai tayi tana kallon Aishatul-humaira wacce ta ƙara wayo sosai ga wani kyau da Allah ya zuba mata, ta luff a jikin mahaifinta sai barci take.

"Mamana an zama Æ´an mata, ta fara tafiya ne?" Abra ta ce "Tab Æ´ar aiki muka samu Mami, wallahi komai ta samu fasa shi take, haka ta fasa wayar Abou-Aisha ta lalace ga surutu"

"Ah masha Allah, Allah ya raya mana ita" Salima ta fito tana musu Sannu da zuwa.
Bayan sun gaisheta, Mami taiwa Abra farin ciki kuɓutar Dr Bulama sosai tare da ƙara jajanta lamarin.
Daga nan ɓangaren su Salman suka nufa, dake bayan tafiyar Salman ɗin an sake gina sabon ɓangaren a gidan Abbi, kuma babu kowa ciki shi ne Salman da Afra na dawowa suka sauka a nan. Mami tabi bayansu da kallo gwanin sha'awa kana ta shiga kallon tilin kayan arziƙin da Adnan ɗin ya kawo musu.
A zaune suka samu Salman rungome da Afra sai kuka take taƙi haƙura tana ganin kamar gangancinta ya sanya ta rasa abin cikinta.
"Kai baka jin kunyarmu ko"?
"Ni kam Yaya zanji kunya ko kai? Ku rufe idanunku idan ba zaku iya ba" Adnan ya kwantar da Aishatul-humaira a cinyarsa yana ɗan jijjigata sai gani ya yi ta fara ɗaga kai da ƙafa kamar wacce akewa wasa.
"Babu abin da zamu gani wanda bamu san dashi ba, mun shige darasinku" Adnan ya faɗa yana zaunar da Little wacce take ƙoƙarin sakkowa zuwa wajan Salman domin tuni ta gane shi.
Abra ta koma kusa da Æ´ar uwarta tana dungure kan Salman.
Hira suka yi sosai kafin Abra ta janye Afra zuwa bedroom ta fara bata darasi mai zafin gaske.

"Little Kinga mun rasa mijinki ko? Don't worry soon za a samaki wani" ya zauna yana mata wasa ina ita hankalinta na kan wayar shi.
"Yaushe kuka dawo daga ƙasar wajan ne?" Salman ya ce "Cikin satin nan, muna tunanin ma hawa jirgi ya kawo ɓarin Allah dai ya barwa kan shi sani"
"Ayyah Allah ya kawo ni soon" hira suka ɗan taɓa duk da Adnan hankalinsa yana kan Abra baya son tai nesa da shi baki ɗaya.
Bayan sun yi sallah Mami ta aiko da lafiyayyan lunch mai tsari kala-kala.

Fitowa tayi daga kitchen zata shige bedroom É—in Afra ya yi saurin jawota jikinsa yana kissing wuyanta.
Ta marairaice fuska tana kallon shi, ya manna lips É—in shi akan nata tare da yin kissing kaÉ—an ya ce "kin barni kamar maraya, Allah zan faÉ—awa Hajiya Mama"
Ta shafi gemun shi tare da wuyan shi ta ce "Please mana, yau ɗaya ka barni muci abinci da Afra kaji" ya langwaɓe tare da riƙe ƙugunta da kyau yana mannawa da nashi murya bata fita sosai ya ce.
"Ki gama yanzu,ina son mu gaisa da ƙanin Little" ta rungome shi sosai shi kuma ya fara ƙoƙarin kissing bakinta..
Ƙafar shi yaji an riƙe ana miƙewa tsaye tare da bubbuga ƙofar.
"Oh my God, jeki madam tunda little tazo ba za ai abin arziƙi ba, yarinyar nan kinawa babanki baƙin ciki yasin" ya faɗa yana miƙa hannu tare da ɗaukan ta, shi bai ma san yaya akai ta zo wajan ba.
Dry sosai Abra tayi tana shafa kan Little.

Da daddare Salman ya yi musu jagora zuwa gidan Ammi sosai taji daɗi, kamar ta ƙwace Little amma taƙi ta maƙale a jikin Salman sai ka rantse shi ne ya haifeta shi kam dry kawai yake, daga nan suka je gidan Uncle Shurem sun daɗe sosai, ko wanne gida sai Adnan ya ajjiye abin arziƙi.
Ganin Salman ya É—auki hanya daban ya sanya Abra faÉ—in "Faris ina zamu?" Ya ce "Gidansu Mami angel"
Jin Salman ya ce angel ya sanya Adnan taɓe baki, yaci ace ya saba amma a kullum Salman ya faɗi haka sai yaji kishin Abra, yana dannewa ne kawai sbd yasan kawo yanzu babu komai a zuciyar Salman ɗin.
Salman kuma ba zai taɓa iya cewa Abra kai tsaye ba, bakinsa ya saba da angel babban dalili kuma Abra is his first love, yana ganin girma ƙimar sunanta ainun, ba zai taɓa iya manta abubuwa da suka faru ba, da yawan lokaci yana tuna first kiss ɗin shi da ƴar mace kuma Abra ce sai ya yi saurin yin Asstagafirullah. Shi ya sa a kullum ba a son namiji ya ɗinga zaƙewa yana aikata abu ga mace, sbd rashin samun tabbaci kasancewar ta mata wajanka, idan bata zana matarka ba a kullum ka ganta sai abin ya faɗo maka.

Bayan sun gaisa Anuty Suwaiba ta ce
"Abra nayi miki abubuwa da yawa, don Allah ki yafe mini ina cikin jarrabar rayuwa, tun bayan aure na da rabuwar da mukai, har yanzu wani namiji bai taɓa cewa yana so na, don Allah ki haƙuri ki yafe ko zan samu sassauci da rahamar Ubangiji"
Abra ta ce "na yafe miki har abada" haka Uncle Faisal, wanda ya auri mace bai san halinta ba, sai gashi ashe maza take bi har sukai auren bata dai na ba.
Shima ta ce ta yafe masa babu komai, haka babar Mami. Daga nan shopping mall Salman ya shige ya dinga jidarwa Aishatul-humaira kaya kamar hauka, Adnan zai magana Abra ta ce ya rabu dashi ai yana da kuÉ—in kuma shima babanta ne, bisa dole Adnan ya yi shiru.

A ɓangaren Salman aka bawa Adnan da Abra wajan kwana Mami kuma ta ɗauke Little. Cikin dare Adnan ya ɗauke Abra zuwa bedroom ɗinsa, a ranar bata samu barci ba sai da sukai sallar asuba, sosai Adnan ya tara mata gajiya ga yanayin cikin dake jikinta wanda kawo yanzu ta san da zaman shi.
Washegari motocin Major Khamal Khamis suka sauka a gidan,yana shigowa yaci karo da Little da sauri ya ɗauke ta yana faɗin "Matar zuwan yaushe" ta dinga tsalle a jikinsa, Mami ta rungume shi ta baya tana cewa "Wlcm Man" ya jawota gaba yana riƙe hannunta.
Sosai Abbi yai farin ciki ya ƙara sakawa ko wanne albarka, a nan yake cewa ya kusa ritaya daga aiki ya dawo gida baki ɗaya hakan ya yi wa su Mami daɗi.
Adnan ya kwashi iyalan shi zuwa gidan abokinsa Fayyad sun jima suna hira..
Washegari gari jirgi ya É—aga dasu zuwa Kaduna.

Rayuwa kenan, komai ya yi farko yana da ƙarshe a hankali Ubangiji yake tafiyar da komai cikin iko da buwayar shi, sauyi da ci-gaba yana ta zuwarwa Adnan da matsayinsa ya juye daga kan S.p ya dawo Inspector General of Police. Zaman gida ya yi masa wahala sosai. Da nacin su Abra da kuma addu'a haɗi da magiyar da Dr Bulama yake Ummi ta amince suka mai da hankalinsu, amma ta kwashe komai nata, Adnan ya buɗe sabon asibiti babba ya mallakawa Dr Bulama.

Da gudu manyan motoci ke shigowa cikin Bulama's twins privet hospital. Jijiya na tashi kota ina, wasu manyan jami'an tsaron suka buɗewa Adnan ƙofa ya sako da ƙafarsa zuwa ƙasa cikin sauri kuma ya fito sanye da blue ɗin uniform wanda suka amshi jikinsa. _Ag ISP Adnan Aliyu Matawalle Inspector General of Police_.
Ya juyawa da sauri zuwa cikin hospital ɗin yana ɗagawa sauran hannu alamar su tsaya, kai tsaye emergency ya nufa, yana zuwa ya samu Hajiya Mama tsaye da Ummi wacce bata jima da zuwa ƙasar ba, Abdullah na zaune shi da matar shi Soumayyerh a gigice Adnan ya ce.
"Mama where's my wife? Tana ina?" Da hannu ta nuna masa labour ya nufi shiga Mama ta hana shi bai tsaya ba yai shigarwar shi ciki, yana shiga idanunsa ya sauka akan Abra wacce take cikin halin ciwon naƙuda su duka sun tsorata domin cikin kusan watan shi goma sha ɗaya, da sauri ya rungume ta yana shafa kanta.
"Sorry Beb, sorry sweetheart sorry" shi ne kawai abin da yake faɗa, kuka sosai ta saka tana riƙe Adnan zufa na yanko mata, iya wahala tasha Adnan ya yi zaman dirshan a gadon lokacin da Abra ta fasa ihu daidai lokacin data haihuwa shima ya saki kuka yana riƙeta sosai a jikinsa ganin ko motsi ta kasa, tausayinta ya kama shi sosai.
Likitoci suka zare babyn wane yake ƙato dashi tubarkallah, aka shirya shi cikin wasu kayan sanyi masu laushi sbd weather garin. Itama Abra aka gyara ta tare da mayar da ita ɗakin hutawa. Adnan ya rungome Abra da baby boy ɗin, jaririn uban shi ya yo baƙi ne sosai sai jajayen laɓɓa da yake dasu sai motsi yake yana kai hannu baki, a hankali Adnan ya lumshe idanun tare da faɗin.
"Allah ya raya mana Abdullah bin Adnan Aliyu Matawalle" Abra tai farin ciki sosai soyayyar Abdullah ta wanzu a zuciyarta musamman ganin kamar shi da Adnan.
Akai taron suna lafiya kayan da Abra ta samu ɓata baki ne, rasa inda zata saka kanta tayi kukan farin ciki tayi babu adadi.
Chapter 144 · 0% Book details