← Book details Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 145

Sashe 45

Dare Da Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wayata ce tayi ringing a aji, shine ya ƙwace mini wayar" tai maganar tana tsilli-tsilli da ido, saboda ƙaryar da tayi.

Salman dai kallonta kawai yayi, yace "to yanzu daga ina kike?".

"Cafeteria naje inci Abinci".

"To Yanzu kinci Abincin?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

"Wai meke damunki ne, gaba É—aya kamar a tsorace kike fa" yai maganar yana kallonta.

gaba ɗaya tunaninta da hankalinta yana kan yadda za tai ta karɓi wayarta, tare da jinjinawa ƙarfin hali irin na Adnan.
'yanzu idan da gaske yake ya tafi da wayata Kaduna ya zanyi?' wata zuciyar ta tambayeta, nan da nan wank irin gumi ya shiga tsastsafo mata, na tashin hankali da damuwa.

A haka suka nufi mota suka kama hanyar gida, Salman ya lura gaba ɗaya akwai abunda yake damunta, amma ganinaa yayi-yayi ta gaya masa taƙi, kawai sai ya ƙyaleta.

Tafe suke a mota, Baby na sake gwadawa Ihsan yadda za suyi da Sojan nan idan sunje Abuja, Ihsan tai shiru tana sauraren Baby kamar 'ya da uwa.
Baby  tace "Maza ki ɗakko waya, ki sanar masa gamu nan".
Jiki a sanyaye Ihsan ta ɗakko waya ta kira wata lamba, wadda tai saving da Yallaɓai.

Sai data kusa tsinkewa, sannan ya É—auka "Hello beb ya?"

Tai ajiyar zuciya tace "Ya kake? Ya aiki?"

Yace "Alhamdilillah, nayi missing É—inki sosai fa".

Ihsan tace "gamu nan zamu shigo garin Abuja".

With so much excitement yace "Wow, are you sure?".

Tace "Quiet sure"

Yace "Can't wait to see you Baby, sai kin zo, ki sauka a guest house É—ina, za'a samar maku da komai".

Tace 'Alright, sai mun zo".

"Ok bye".

Baby tace "hmm zaka ga tsiya, ko ka saki kuɗi ka ƙwaci kanka, ko muyi maka bariki irin ta yaran zamani".

Gaba ɗaya Abra jinta take kamar mara lafiya, saboda rashin wayarta, gashi gefe guda tana ta tunani unknown ɗinta, da yake turo mata saƙonni. Allah sarki ta san yanzu zai tayi mata Magana yaji ta shiru, ba ta reply.

Da magariba, Abbi ya dawo daga masallaci suna hira shi da Na'ima, gefe Salman yana duba wayarsa, Abbi yace "Hope dai karatu kake ba shirirta ba?"

Salman yace "eh Abbi, ina duba wani abu ne".

"Ai nasan hankalinka ne, kafi maida hankali a kan, shirita fiye da karatu".

Na'ima tace "Eh amma ai Abra ka yadda karatu take a waya, amma shi kace ba karatu yake ba" wani mugun kallo da yayi mata ne, ya sanya ta haÉ—iye Maganar ba shiri.

Abbi yace "Ni ban ma ganta ba gaba É—aya, me take yi a É—akine iya kaÉ—ai?"

Salman yace "I don't know what's wrong with her today, gaba É—aya kamar wani abu yana damunta".

"Kira mini ita".

Salman ya miƙe ya nufi ɗakinta, ko da ya shiga ya tarar tana zaune, ta zube littattafai a gabanta, amma tunani takeyi, ba karatun ba.

Yayi ajiyar zuciya sannan yace "Idan kin gama tunanin kizo Abbi yana kiranki".

Ta É—aga kai ta kalli Salman, wanda tuni ya juya zaia bar gurin.

Jiki a sanyaye ta miƙe ta biyo bayansa,  ta tarar da su gaba ɗaya a falo.

Ta ƙarasa gaban Abbi ta zauna yace "Gani Abbi".

"Daughter na, meke damunki ne? Duk muna nan a zaune, amma kin keɓe kanki a ɗaki, gashi fuskarki ta nuna, kina cikin damuwa".

Abra tace "Abbi bakomai, na gaji ne kawai"

Abbi yace "Anya kuwa? Ki gaya mini gaskiya".

Salman yace "Wayarta akai seizing a Makaranta"

Abbi yace "Subhanallah, how comes?"

Salman yace "Wai ringing tayi a aji, shine aka ƙwace, shine take ta wannan ƙuncin".

Abbi yace "Ki dena damuwa, in basu baki ba a canza miki wata".

Na'ima da tun É—azu ba tace komai ba tace "Wane irin a canza mata wata, ka sani ko ana musu karatu tana wasa da waya ne?".

"No ba haka 'yata take ba, koma mene zanga abunyi, a canza wata idan be baki ba, amma ki dena damuwa kinji?"

Tace "to Abbi".

Salman ne ya miƙe ya nufi hanyar kitchen, ganin Kamar Salman yana fushi da ita, yasa ta miƙe itama ta nufi kitchen ɗin".

"Ina zaki?" Na'ima tayi maganar tana zazzarewa Abra ido.

Abra tace "Mami banci Abinci ba, zanje in zuba ne".

Ba dan ta so ba, tai shiru saboda Abbi yana gurin.

Da sauri Abra ta ƙarasa cikin kitchen, ta tarar da Salman a tsaye yayi shiru, da alama ma ba wani abu ya shiga yi a kitchen ɗin ba.

Yana ganin ta shiga, shi kuma ya nufi hanyar fita, da sauri tace "Faris"

Ya waigo ya kallta ba tare da yayi magana ba.

"Fushi ka ke dani?".

"Me ki kai mini da zan fushi dake?".

'ga alamu nan a fuskar ka, me nayi maka? Kuma ina shigowa ka juya zaka fita".

"To ya kike so inyi, ina ta binki ki gaa mini me ke damunki amma kin ƙi".
Abra tace "Haba Bloody na, rashin wayata ne kawai duk ya dameni, You know am so much attached to my Phone, am sorry"

Ta yi maganar tana murmushi tare da jan dogon hancinsa, ji yayi yana neman shiga wani hali, kasancewar kusacinsu da Abra yayi yawa, gashi sai ƙamshin turare take yi.

Cikin shagwaɓa ta ce "to kace mini ka haƙura mana".

Lumshe ido yayi, yana kallon yadda take cigaba da shagwaɓa.

"Talk mana".

"Ta yi maganar tana girgiza shi".

"Tom na haƙura" ya faɗa a taƙaice.

Ta girgiza masa kai tace "See how you frown your face, gaskiya ba kaa haƙura ba"

"Na haƙura Angel, let me go and rest please"

"Wai to ya na ga duk ka wani canza ne?"

Yace "Stress ne kawai na school, see you later" yayi maganar yana kashe mata ido É—aya, ya fice daga kitchen É—in.

Murmushi tayi a hankali ta furta "Faris sarkin rigima, am imagining ma life without you, you are so much caring bro, Allah ya biya ka" ta ƙarasa Maganar da ajiyar zuciya.

"Kai yanzu Adnan, fisabilillahi daga cewa zakaje wani Assigment a Kano ka dawo, sai kaje ka yi zamanka, kullum kana gaka nan gaka nan, mahaifinka duk ya damu".

"Am sorry Hajiya, ni kaina ban yi zaton aikin zai ja mini dogon lokaci haka ba, amma Alhamdilillah an yi Nasara a aikin ai".

"To barka, haka ake so dama, amma aikin na ku ne sai a hankali, yau mutum yana nan gobe yana can, ga ƙasar nan babu cikakken tsaro sam".

Yace "Hakane Hajiya, dama aikin É—amara kasada ne, amma gara a rasa rai É—aya idan har zai silar rayuka da yawa su samu kwanciyar hankali".

Hajiya tace "A'a Adnan, ai duk rai rai ne, mai shi yana son abunsa, Allah dai ya tsare mana ku".

"Ameen, uwata ta kaina, baki mini Addu'a ba yau".

Ta yi murmushi ta ce "Addu'a kullum cikinta muke ai, yanzu haka ma ai na yi maka".

Yayi murmushi yace "Allah ya ja kwanan Hajiya Mama"

"Ina, ai mu mun kai gangara, fatan ƙarshe mai kyau muke, ku muke yiwa Addu'a, Allah ya raya mana ku".

Ja yayi kamar ta zuba masa wuta abunda ta faɗa, life without his Mum, haka kurum ya ji jikinsa yayi sanyi, miƙewa ya yi daga in da yake zaune yace "Sai da safe"

"To Allah ya tashe mu Lafiya, kar ka manta kayi Addu'a"

Bai amsa ba, kuma bai waigo ba ya wuce É—akinsa.

Ya shiga banÉ—aki ya watsa ruwa, ya fito yayi shirin kwanciya bacci, gefen pillow É—in sa ya kalla, wayar Abra ce da aka ishe shi da ringing ya sakata a silent.

Ya danna wayar, kusan 25missed calls, wanda duk daga Bloody sai Faris.
Sliding ɗin screen ɗin wayar yayi, saiga hoton Abra akan screen lock ɗin wayar, kanta babu ɗan kwali, ta saki gashin kanta, da ya rufe mata gefen fuska, ta turo laɓɓanta gaba, wanda suka kasance pink.
Shiru yayi ya zubawa hoton nata ido, kamar mai nazartar wani abu, daga bisani yayi wata nannauyar ajiyar zuciya, ya kashe wayar gaba É—aya ya ajiye, ya kwanta.

Duk da zuciyar Ihsan cike take da fargaba, amma haka ta ɓoye tsoronta, ta dake dan karta ɓata musu shiri, ta dube shi tace "Nifa Yallaɓai babban dalilin zuwana nan shine, ciki ne a jikina har watanni huɗu dan haka nazo ka bank kuɗi inje in cire shi, ka san dai babu da wanda na taɓa mu'amala sai kai.

Haɗe rai yayi yace "Na sani ko bayan na buɗe hanyar, kin cigaba da leƙe-leƙenki, kuma wace irin sokuwa ce ke, da zaki bari ciki ya shiga jikinki har Wannan lokacin?"

"Kar ka sake ce mini sokuwa, kawai ka bani kuÉ—i inje in zubar, kar Asirina ya tonu".

Gajeren tsaki yayi Yace "Naji, zan baki 20k kije a cire shi".

Wani banzan kallo ta yi masa tace "sai kace cikin jikin Akuya? Dubu É—ari aka ce zan ajiye, sannan a cire cikin ya zanyi da wata 20k".

"Kina da hankali kuwa, a wannan marrar ne zan baki har 100K?".

"A Arziƙin da Allah yayi maka mecece 100K? Ko nice a bar banza?"

"Kinga zan bani 50K, daga haka ba zan ƙara ba".

"Gaskiya ba zan karɓi 50K ba, a ina zan samu sauran?".

Yace "Wannan ya rage naki kuma" wani irin baƙin ciki ya turnuƙe mata zuciya da tarin nadama da dana sani, ba yadda ta iya, haka ya tura mata 50K.
Ba kunya kuma bayan ya tura mata ya fara lalubarta, abun mamaki sam ba ta masa musu ba, suka gama sheƙe ayarsu, Sannan ta kintsa jikinta, ta koma masaukin su.

Baby ta dinga jinjina mata, domin kuwa duk abunda suka yi, ta naÉ—o tsaf a video ba tare da ya san tayi haka ba.

Nan Baby ta sake shirya mata abunda zata yi masa, dan wanda ya yiwa Janna, sai da ya ajiye mata dubu ɗari biyu da hamsin, dan haka suma sai sun wanki wannan Yallaɓai.

Dan haka suka tsara message tare da videon nan nasa, suka tura masa!.
Chapter 45 · 0% Book details