Sashe 97
Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
👁🥡👁 🅿4⃣5⃣. *S* osai taji zafin ya rage ta hanyar messeging din iskar bakin nasa da yake tura mata a bakinta, sunkusa minti shida sannan ya saki fuskar tata ya kamo hannunta suka koma suka zauna kan inda ta tashi. d'aukar cokalin yayi ya tsamo tsoka d'aya yakai cikin bakinsa yana taunawa a hankali, dan sosai yaji dad'in had'in girkin natah kuma yaji zafin ya rage yadawo dai dai ci yanzun, shiyasa ya saka hannu ya matsota kusa dashi ya dinga bata a baki shima yanaci saida suka koshi dukkansu sannan ya miqe tsaye d'aukeda wayarsa a hannun, ya zuba mata idanunsa itama binsa tai da kallo "zanje nai wanka kema kan na dawo saiki ida shiryawan" abinda yace kenan ya fita. sauke ajiyar zuciya tai bayan binsa da kallo datai harya bar gidan. runtse idanunta tai har tanajin kamar ta maidosa ya zauna dan sosai take jin farinciki na wannan moment din nasu. tana cikin gyara gidan ne dud jikinta a kasalance sakamakon yawon tunosa da take, jitai baba d'ahara na fadin"assalamu alaikum mutan gidan na kurkusa ne? d'agowa heenduh tai daga kwashe sharar tsakar gidan nasu data tattara ta tace"oyoyo baba d'aharas sannu da shigowa" zama baba d'ahara tai saman kujerar 'yar tsugunno dake jikin bangon tsakar gidan tareda fadinn "bismillahi Allah, yawa heenduh daman na shigo ne mu gaisa to kuma ga alamun ma zainabun batta nan ko?" dafe kai heenduh tai da hannunta tace "ayya na manta na shiga na fad'a miki mama taje zariya kakanta ne ya rasu yau" baba dahara tace "innalillahe Allah jiqansa amman Zainabu maimakon ta fada mun ai saimuje tare inda dud an zama daya dai ko?, tareda babanki ne suka tafi kenan? "a'a baba dahara aishi baba yana asibiti ne" "Wake ba lpia kuma?, cewar baba dahara din. waro idanuwa heenduh tai tace "Lalala kaddai bakisan habibinki bayya da lpia ba?" hararta baba dahara tai tace"ke banson shiririta da shaq'iyan cin nan naki waye habybyna kuma?" wata 'yar siririyar dariya heenduh tai sannan tace "ah habybynki man baba yawale mai ran qarfe" saurin bugun qirji baba dahara tai tareda dafesa tace "Innalillahe miya samesa? amman dai 'yar nan bakkida kara shine ya gagara kije ki fada mun? Tun yaushe ne suke asibtin ma?, O'hni dahara na shiga Tara mai tarainiya da yawa Allah sa basu kai ga kwana ba dan abun kunya ne agareni ace saisun kwana sannan zanje dubasu" "Kwantar da hankalinki baba dahara yau aka kaisa nima yanzun wanka kawai zanyi na koma asibitin kai musu abunci nida Yaya khaleepa, ki jira saimu tafi tare inda bakisan 6angaren da suken ba ko". baba dahara tace "eh kinkawo Shawara jekiyi wankan to kidaina wannan laqwaiqwaitan tafiyar nan taki dan Allah heenduh sauri." har heenduh ta fito tai sallar magrib sannan babu jimawa taji wayarta na ringing ta dauka ganin batasan number bane yasata ajiye wa. bayan wasu mintoci taji shigowar text message da hartayi burus sai kuma wata zuciyar tace a'a tadai duba taga miye saqon ya qunsa. "nakira baki daga ba, to Ki fito gani nan waje zamu wuce." sai lokacin ne ta fahimci waye ke mgnr doctor ne. shiru tai tana tunanin a ina ya samu number ta to? ganin takasa tunowa yasata tashi ta saqala gyalenta dokin wuyanta daman doguwar rigar atamfa ce a jikinta tai matuqar amsar zubin surata kuwa ta dauki jikkarta ta fito dakin. basket din abincin nasu ta dauka ta dubi baba dahara tace"mu tafi gashi can waje yazo" haka ta kulle gidan suka isa bakin motar ganin yunus a gaban motar yasata bude baya itada baba dahara suka zauna. aladafce khaleepa da yunus suka gaisar da baba dahara din sannan suka dau hanya batareda khaleepa yacewa heenduh komi ba dan wani qululun haushin shigardatai ta fito yakeji saikace budurwa, uwa zata night club ba hospital ba?shifa Allah ma yasani kishinsa zafi ne dashi. Wata zuciyar tace masa"ai matsayin budurwar ce inda baka rabata da abinda yasa take tutiyar budurcin nata ba bare ta hankaltu garage wasu abubuwan inkai sa'a. qutawa yai yace "hmn yau zanyi abun ne" jiyai cikin tsokanar ta yunus ya juya yacewa heenduh "aunty headache babu mgn ne komun fara gaba ne ban sani ba?, "aunty???" abinda khaleepa ya maimaita kenan a ransa sannan yayi wani dan taqaitaccen murmushi wanda iyakarsa lebbensa baihau fuskarsa ba, Qasa qasa yace "zadai ta zama auntyn nan da wasu 'yan awowi gaba. heenduh kuwa a yangance tace "ban lura dakai neba" dariya yunus yai yace"nikam dai ban yarda da cewan ba'a ganni ba saidai nasan mulkin naku ne ya motsa sarauniya heenduh" dauke kai tai abinta bata qara cewa komi ba sai shi da baba dahara da suketa labarin yanayin zafi da aka fara kuma yanzun. sai satar kallon doctor din takeyi a madubin motar caraff kuwa ya kamata tana kallonsa da sauri ta maida fuskarta cikin cinyoyinta saboda kunyar dataji na ya kamata tana satar kallonsa. shiko murmushi kawai yayi tareda bada signal ya karkata zuwa cikin asibitin nasu. yai parking suka fito dukkansu. tundaga nan ma'aikatan asibiti maza sukaita gaishesa da barka da shigowa yallabai. ahaka har suka isa dakin da su baba yawale suke. saidai sun sami baba yawale na barci sakamakon alluran da akai masa cikin drip din. nan su baba dahara sukaiwa baba Ismail yamai jiki ya amsa masu a fara'ance sanna sukai masa gaisuwa shima. shiko khaleepa na tsaye dafe da qarfen gadon baba yawale din ya harde qafafunsa a juna hannuwansa zube cikin aljihunsa 2, matsawa yai a hankali ya cire drip din dan saurin ankara dayai ruwan har sun qare jini ya fara dawowa a cikin robar drip din. cikin sauri sister maryam da daman itace tasa masa qarin ruwan a umarnin doctor mu'sab danya tafi gida shi tun d'azun, ta iso wajen tana fadin"sorry doctor bari na ida gyarawa" bai kulata ba har saida ya ida jona masa wata ledan ruwan bayan ya zare waccen sannan ya juyo fuska a mtqr daddaure ya zuba mata idanunsa kaifafa yasake maida hannuwansa cikin aljihunan sa cikin 6acin rai yace "kinsan kan aikin ki kuwa da matsayinsa?"! zatayi masa mgn knn ya ce cikin tsawa "shut up your lazy mouth, it's enough it's enough banson jin komi daga bakinki kingane? so worning for you! worning! worning! muddin kika qara mana wannan makamancin shirmen aikin ga dukkan kowane ma kalar patient namu bawai wannan kadai ba zamu dauki mataki ga dukkan kowaye bama ke daya ba a cikin ku OK?" cikin rawar jiki tace"Sir..sorry sir baza'a kuma ba doctor" tsoki yaja kawai tareda cewa "fice mun anan dan banson ganin mashirmanci a wajen aiki kusa dani, ki kuma kiramun sister laure". dasauri ta fice kuwa tareda amsa masa. sosai heenduh taji dad'in yanda taga sam 'yan matan sistocin basu gabansa saima wani tsoronsa data gani muraran a idanunsu, lura datai sister maryam din yar iyayi ce da tusa kai ba qwarjini yasa taji ma dadin wanketa dayai. satar kallonsa ta dingayi cikin murmushi. baba dahara kuwa sai cewa take "mutane sai haquri ai babban likita." yunus Yace"sai ana musu hakan ai baba zasuna kula da aikinsu yanda ya kamata." "Allah kyauta to" cewar baba dahara din" sukace aminn.. daidai nan sister Laure ta qaraso tace"doctor gani nazo za'ai maka wanu abun ne?" dud cikin sistoci mata khaleepa sunfi shiri da sister Laure dan macece mai kirki da kulawa da patient sam battada wulaqanta patient gata tasan darajar aurenta akan sauran matan masu aure da 'yan mata dazakaga sunata faman shisshigewa sauran mazan likitocin asibitin. dan haka d'an sakin fuska yayi yace "yawwa sister Laure zakina kular mun da wannan patient din nawa da aka sawa drip please grandpha nane fatan zaki kular mun dashi yanda ya kamata?" murmushi tai tace"insha Allah doctor bama shi kad'ai ba ai dud sauran patient din section nan haqqinmu ne kuladasu" sosai yaji dadin hakan yace "hakane muje laboratory room kitayani na dubo file din matar nan da aka mata gwajin *operation* na ciki naga ya sakamakon ya bada" sister Laure tace "hakane doctor dan gskia matar nan na wahala tanaban tausayi qwamma ayi mata aikin nan a fidda cutar nan kota huta" "small dad ina zuwa" cewar Doctor khaleepa din sannan suka wuce yunus na zaune kusada gadon baba yawale yana dan Mirza masa tafukan hannunsa. sadda ya dawo har baba yawale ya farka yadanci abuncin yanda ya kamata haryana tsokanar heenduh da cewa"Matas ta iya girki ashe banyi zab'en tumun dare ba". dariya sukayi dukkansu yayinda heenduh tace "ay ga matar dana za6a maka nan baba dahara saina koya mata tadinga yi maka inkunyi aure" cikin dan murmushi na majinyaci ya dubi baba dahara yace"kinji abunda jikarki tace zaki aure tsoho kamata? rufe fuskarta baba dahara tai wai ita kunya ta sanya gyalenta a baki tace "nima ai tsohohwar ce ba damuwa zan iya" daga heenduh har baba Ismail da yunus dariya suke musu ganin yanda tsoffin suka qyasa da juna abun ba qaramun burgesu yaiba. dud wannan dramar khaleepa na jingine bakin kofa yana murmushi shima abun ya burgesa, ganin yanda heenduh keta qyalqyata dariya yabasa sha'awa harya shagala da kallon zallar tsantsar kyaunta bai Ankara ba sai yaji baba Ismail yace"ah khaleepa Ashe kadawo ka tsaya nan?qaraso man" cikin kunya ya sosa qeyarsa tareda qarasowa ciki ganin dayai small dad yakamasa yana kallon 'yarsa muraran. duban agogon hannunsa yai ya dubi baba Ismail din yace "small dad zan tafi Allah qara sauqi baffa" da amin suka amsa sannan baba Ismail ya dubi heenduh da baba dahara yace "inda gashi zai koma gida sakuje tare" miqewa baba dahara tai tana gyara mayafin kanta tace"harma dare ya fara bamu ankara ba" cikin tsokana heenduh tace"hohoho baba daharas ai daman bazakisan dare yayi ba inda kina gaban masoyin naki...da gudu tabar dakin ganin datai baba dahara din na shirin Sakar mata ranqwashi akanta,,, dariya baba Ismail sukayi yayinda baba dahara tace "kujimin ja'irar yarinya ta maisheni qawar kakarta sak" dariya khaleepa kesonyi amman saiya kanne. har waje wannan karonma baba Ismail ya rakosu cikin qasa qasa yaiwa heenduh mgnr kalacinsu na safe sannan suka Shiga motar suka tafi. wannan karon shida yunus ne suke dan mgn dan baba dahara shiru tai cikeda jimamin baro baba yawale datai jitake inama itake jinyarsa