← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 178

Sashe 51

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

majalissar su haruna mai cemist kuwa nan samarin wajen sukace"mun gaisheda heendu beuty haru na samu miqo miki gaisuwa" ko kulasu bataiba taja tsoki tareda fuzgo hannun sa'a sukai gaba. isa kabeer ne yace "kai abokina mutuniyar taka fa ta qara cika full wlh, gashi dreesing na matuqar kar6arta koya tasa abu sai ya haskata, face dinta ta qara wani masifar kyau fa billaheel azeem fiye da randa ma tazo nan da bbnta dreesing" haru yace "hmm kaidai bari abokina na gari ba kmr wannan d'an iskan ba, yayi mgnr yana hararar Hari's sannan yaci gaba da cewa "yanda kasan hawainiya kullum kyaunta qara rikid'ewa yake, kai insha Allah fa dl babyn nan rabona ce saidai baqinciki ya kashe ka Hari's wlh" cewar haruna. kecewa da dariya Hari's d'in ya dubi haru daya dinga bin heendu da kallo harta qule daga inda yake hango ta. Yace"har gobe wlh haru bazan daina baka shawarar ka rabu da heendu beuty ba dan yarinyar klr mnya ce fa masu nera d'ubge a hannu" matasan suka d'au ihu yayinda haru yace"mugu maq'etaci d'an baqinciki kawai" kan wannan dramar daine suka maida hankali a majalissar haruna mai chemist. lokacin dawowar heendu baiba amman kakarta jameela ta hirgad'osu gida sakamakon addabarta da sukai shikuwa mlm zayyanu dariya kawai yake musu yakance "ato bamai jinku jika da kaka nn bada jimawa ba za'a ga kun d'inke kuna qus qus ay" a hnya ne heendu tace "bazamu je gidn baba yawale ba ynda ake kiran sllr nan nasan yana cen limanci masallaci, sa'a tace aikuwa kema kin sani ai" da sauri heendu tace"wayyo nayi mantuwa sa'a " sa'a tace mntuwar mi? heendu tace"dazun musaddiq yamim kyautar waya na mntota gidan baba d'ahara zo muje,,nan kuwa suka isa gidn tana nn kuwa inda ta barta sa'a ana bud'e wayar tayi wani qarar farinciki tace"wawoooo wlh ipone ce kumsa babbar ma kuwa,kai naji dadi fa wlh qawata wayar nn tazo a sa'a zamuyi babu da ita gobe" shiyasa ma nakarba ai danmu qara bada kala ai a wajen kinsan mu bammason harkar qaranta a waje. tafawa sukai dariya nn sukaita santin wayar suna faman tattabata har suka baro gidan baba d'ahara bata gama salla ba dayake jam'in su baba yawale take bi anaji sosai ta loud speaker d'in. suna fotowa kowa ya nufi gidnsu, heendu tana shiga ta iske mama na salla itada maman salis dayake babban tabarmar nn ce tasu shimfide a tsakar gida sai suka daura sallaya akai. dayake tasan tana fashin salla shiyasa tai wucewarta d'aki ta fad'a bisa babban katifarta dake qasa bayan cillar da gyalenta datai can gefen katifar tata ta shige cikin bargonta tana lallatsa wayar cikin jin dad'i, acan waje mama zainab bayan sun gama sallar ne maman salis datafara mnyanta tace"ina wuninmu zainabu na shigo na iske anata salla ba'a gaisaba, shine nima nace bari kiga da zaman nan d znyi kn kigama salla gwara nima nayi " mama zainab tace "lpia lau Alhamdulillah mama, aikam dai qwamma dakikai sllr kinhuta inkinje gida, nan maman salis tace "dazun naje wajen maman taki Jameela saima take cemun mai gidan naki yasamu rauni mafarin knn nazo na masa ya jiki, to cikin ikon Allah ma sai muka had'u dashi ynzun bada jimawa harma yake cemun daga nan gida ya fito, to shine nai masa ya qafan kuma Alhamdulilla naga qafar ma ta samu lpia mafarin knn nace inda na shigo aibana wuce ba, Shine na shigo danmu gaisa" cikin fara'a mama zainab tace "amman mungode sosai mama" mamn salis tace "bari to natashi natafi inda mun gaisa kn akira sllr isha'e kuma q'wamma mu koma gida muyita acan" cikin murmushi mama zainab tace "hakane, amman mama wai ina yaya salis ne rabon dana gnsa tunkan bikin aurenmu fa shekaru da yawa" maman salis tace "Allah sarki ai tunda q'anena ya d'aukesa aiki inda ya samo masa tofa can yariqesa hannunsa dud yawan shekarun nan kuwa harma ya aura masa yarsa yanzun haka yaransa biyu babban shine musbahu mai shekara 21 sai qaramar mace ce aminatu yar kimanin shekaru 16 amman dayake aikin nasu kwata kwata ba hutu ba koda yaushe yake zuwa nn ba, dan zuwnsa na farko kwansa biyu lokacin da mukhtar suka tafi mecca to aikin nasu kuma danaga ana samun matsala in zakai tafia shine nace yayi zmnsa ni inna samu lokaci zan dinga zuwa dubasa inda yana mana aiken kayan buqatu na rayuwa kuma yace suna waya da mukhtar kullum, to yanzun dai zancen nan ma da nike miki ana shirin yi masa transper ne zuwa nan garin cikin 'yan watannin nan" cikin fara'a mama zainab tasake cewa"za'a dawo knn yaya salis Masha AllAh, AllAh shi taimaka kuma mama, "aminn" cewar maman salis sannan ta qara cewa"ina saran insha Allah in salis ya dawo zaiyi qoqarin ganin ya shawo kan alhj mukhtar naku daga baqin qullin da matarsa tai masa, dan abun yai yawa" cikin sanyin jiki kuma mama zainab tace "'to shiknn mama AllAh shi shi yarda haka akeso ay" maman salis na fita heendu ta fito ta kwantar da kanta a cinyar mama zainab tareda cewa"mama kinga musaddiq ya min kyautar waya d'azun " mama tace"kingode kam, amman tun d'azun ina kika shige ne tun marece badai kuna tareda shi ba? mama zainab tai mata tambayar tana mai tsattsareta da idanunta. da sauri heendu tace "mama a'a wlh bamma tare dashi, baima jimaba ya tafi mu kuma nida sa'a muka shiga gidan baba d'ahara mukai mata yini sannan daga nn kuma mukaje wajen kaka jmcy" sauke ajiyar zuciya mama zainab tai tace "barkanki nazata kuna tare dashi ne har tsawon wnn lokaci ay dasai ranki ya 6aci, sannan kuma ban hanaki cewa mamata jamcy ba? dariya heendu ta qyalqyace da ita sannan tace "afuwan mama na" ture kanta mama zainab tai daga cinyar ta tana shirin magana saiga baba d'ahara ta shigo gidan da sallama. mama zainab ta amsa heendu kuwa da gudu taje ta rungume baba d'ahara kamar gaske take cewa "oyoyo baba d'ahara ta Oyoyo oyoyonki" baba d'ahara tace"nikam 'yar nan sakeni kada ki kada ni q'asa" cikin murmushi mama zainab tace "Gskiar ki baba d'ahara" heendu kuwa aka tsinano lips wai tayi fushi an dizga ta mafarin knn tai komawar ta d'aki bayan ta faki idon mama zainab taiwa baba d'ahara signal kan tayi tayi mgnr data kawota. dan haka bayan sun qara gaisawa nan baba d'ahara taiwa mama zainab bayanin bikin da zataje dasu heenduh gobe, mama zainab tace"baba d'ahara ai basai ma kin zo da knki kin gayamun ba ke mai iko ce akan heendu dan haka babu komi wlh Allah basu zaman lpia amaren" baba d'ahara tace "to to amin amin zainabu ngd da girmamanin nan da kike " mama zainab tace "babu komi ai baba d'ahara zaman taren knn ay"babu jimawa baba d'ahara ta koma gida. acan d'aki kuwa heendu juye juye kawai take bisa katifarta tana dariya q'asa q'asa tareda cewa"sai yanzun na qara tabbatar da cewa kina masifar qaunar baba yawale na baba d'ahara ta" lumshe idanu tai jin ynda cikinta ke kuka gashi kuma kwad'on tuwon ruwa taga anyi a gidan nasu, baccin dai batason sake fita gudun kada maman tata ta tambayeta ina zata dataje gidan babanta mukhtar ta samo koda goran yhugurt ne kuwa, dole dai ta haqura taci tuwon ruwan sannan ta kwanta barci wayarta na gefenta a ranta take cewa "yaudai mun rabu da wannan gwaramar wayar tawa munyi new designer ". ahaka barci ya kwasheta. washe gari da misalin biyar na marece heenduh ta shirya cikin doguwar rigar ta da hijab dinta taiwa mama sallamar tatafi dan baba d'ahara na jiransu alhalin baba d'ahara tun safe tai tafiyarta gidan bikinsu. nan mama tai musu adawo lpia Allah tsare. dan haka kai tsaye heendu tana fitowa daga gidan nasu gidansu sa'a ta nufa ta iske ba kowa sai Sa'ar, dan haka d'akin sa'a suka shige heendu tace "ina mama sa'a tje?" sa'a tace "taje anguwa anmn lpia lau inda nai mata bayanin zamuje anguwa da baba d'ahara dan haka ta d'auki d'ayan mabud'in gdn tabar mun wannan anan" heendu tace yana ganki da wannan zumbuleliyar hijab haka sa'a har qasa cikin gida? badai baki shirya ba kuma dan Allah dai? saida sa'a ta rufo gdn nasu sannan ta dawo tace "qawata komi saida kula ai yaza'ai nasanya iriyar wannan d'amammun kayan na zauna haka gida ai bazai yuyuba duba fa kiga? tayi maganar tareda cire hijab din jikinta, saiga kwalliyar sa'a ta inglesh wears ta fito dudda kayan basu kamata sosai ba amman kunyarsu takeji, tsoki heendu tai tareda cewa"ke wlh banza ce qawata yanzun wannan kayan da kika sanya miye wani abun qumuniya a ciki, sa'a tace "ke ai kin saba bakkyajin komi niko wlh tsoro gareni"harararta heenduh tai tace "kuma kinyi kyaun gske fa qawata bari nima dai nasa kayan nan naga yaza sumin ne, ina kayan suke ne nawa? sa'a tace "shiga q'uryan d'aki suna nan bisa gado" haka ko heendu ta wuce ta sanyo kayan ta fito ta tsaya gaban dogon glass mirrow na maman sa'a tana juye juye yayinda sa'a tayi mutuwar zaune wajen tana kallon yanda kayan sukai masifar mata kyau amman kuma batun d'ameta da sukai babu mgn dan dama roba ne kayan. gadai wando har qasa pencil amman yabi jikinta lam6as sannan haka ma rigar ta fiddo mata shape din hips dinta da laq'umammen cikinta shafaffe sai daga sama mamanta sunyi masifar cika gidan bra din rigar, sai dai kuma stones din da suketa qyalli gaban rigar inda breast d'inta suke cike fam dam kamar zasu fito waje tsabar matseta da rigar tai baqaramin qawata rigar sukai ba. gabaki daya jikinta babu inda bayya rawa yanda ta kama kitson kanta ta maidoshi gefen wuyanta ba qaramin kyawu ta qara ba, ga fuskar dama tasha kwalliya sai qyalli take, sa'a sam kasa mgn tai sai daqyar tasamu tace"wlh qawata kamar nai miki kuka dan tsabar kyaun da kikai, ni saina raina ma kaina kinsa na daina jin kunyar kayan ma danasa dan nawa musulmai ne akan naki arna" ta6e lips dinta taiwa heendu tai tace "aini banjin komi gameda gayu qawata" sa'a tace "amman ba haka zamu fita ba ko? Heendu kuwa ta zaro fararen idanun ta
Chapter 51 · 0% Book details