← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 161 OF 178

Sashe 161

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

* 👁🥡👁 🅿6⃣7⃣. *A* hankali cikin dubara khaleepa ya zame heenduh daga jikinsa suka zauna nan saman carpet d'in, suma su dady mukhtar d'in suka qaraso suna shirin zama saiga baba yawale shima yashigo gidan da sallama hannun sa riqe da carbunsa, kusan tare mmn sales da momyn amnat suka shigo gidan suma anan suma suka zauna dukkansu suna sake gaishe da baba yawale d'in. sake futowa mama zainab tasakeyi jin mgnr baba dahara tana rarrashin heenduh dacewa tabar kukan haka nan komi yazo qarshe ay insha Allah Inda tadawo gida lpia. zama mama zainab tayi dud aka nutsu wajen, saida baba yawale y bude taron wajen da addua gamida salatin annabi sannan fa baba isma'il yakoro musu bayanin komi ya faru har kawo futarsa dayai yanzu yakirawo su. shiru kowa yayi a wajen banda sallallamin baba dahara da tashin shessheqar kukan heenduh bakajin komi a wajen. cikin d'ashewar murya wacce taci kuka ta qoshi heenduh ta bude bakinta da qyar tace"kuyafemun dan girman Allah wlh na tuba bazan qara ba, kuma wlh ni gidan sa'a kawai naje bawani waje ba, ko sa'a din ma aka kirawo aka tambayeta zata shaida muku hakan ne.... kwab'e mata baki mama zainab tayi tace "sakarar banza da wofi yimana shuru mikuma zaki fada mana wanda zamu yarda dake yanzu ay babu shi,, kuka ta qara saki tanayi tana dafe kai gwanin tausayi wanda khaleepa baisan sanda ya fara zubda mata hawaye ba na tsakanin tausayin ta dake bin ko ina a cikin saqon jikinsa. sosai su dady mukhtar suka tausayawa heenduh matuqa, sunsan komi ya faru da mutum qaddarar sane dudda itama heenduh d'in nada laifi amman Inda ta gane kuranta tazo tana neman ahi na tuba ai sai a haqura komi ya wuce Inda ubangiji Allah ma ana masa laifi ya yafe bare mutum abin halittarsa. baba yawale yadubi heenduh sannan ya dubi su baba isma'il kawai ya girgiza kai yace " komi dai ya rigaya daya faru, sai ayi haquri kuma, ya dubi heenduh yace" kinfi kowa laifi hendatu miyasa zakije wani waje ba tareda sanin kowa ba? kinbi kin tadawa kowa hankali sannan kuma kinqi bugowa a waya ki fadi inda kika je har saida Allah ya kawo wannan yarinya sa'a datu ta fada gskia a hakan da kikayi kin kyauta knn? " girgiza kai tayi cikin share hawaye tace" ban kyauta ba amman kuyafemun narantse da Allah mairan qarfe bazan sake maimaita hakan ba" baba yawale ya maida dubansa ga mama zainab da baba isma'il yace "zainabu da isma'il indai kun daukeni da gske a matsayin mahaifi to ku yafewa heenduh dan qaddara nakan kowa kuma kun hukuntata yanzu iya hukuntawa wanda nasan koda wasa bazata qara fara gigin sake aikata hakan ba, dagowa baba isma'il d'in yayi fuskarsa a sake dan shima runtse idanuwa kawai yayi ya kauda ido akan heendun tasa yayi mata hukunci da daidai abinda ta aikata kuwa, dan haka yace "nina yafe mata komi ya wuce baba, daman munyi mata hakane danta gane iyaye ba abin wasa bane, bakomai ynxun komi ya wuce Allah baku zama lpia kuma, Allah shi muku albarka" cikin murmushi dady mukhtar da dady sales sukai tareda cewa "aminn qanenmu,, dady mukhtar yasake cewa " naji dadin sake fahimtar juna da akayi haka a sauqaqe komi ya wuce ai insha Allah,, dady sales ya karbe da fadin cewa "hakane, aci gaba da haquri dai dan haquri shine ka isa gaci Allah iyakar qarshen taqaddamar knn Allah kiyaye gaba kuma" da aminn suka amsa, cikin fara'a baba dahara tace "uwargida ta gudu tabar ango a rude to ina kaga a gaishesu? dud tasa yabi ya rame ko? hmnn kinci arziqi ban aure miki shi bama ay na tausaya miki shi Inda kin gaji kin bada kai kin sare" duka wajen akayi dariya harda mama zainab da baba isma'il kuwa, dankuwa hatta gogan naku doctor saida ya dan murmusa dan shima yaji dadin yanda su mama zainab suka sauko daga fushun nasu kan heenduh. yayinda heenduh kuwa wani farin ciki ne taji ya mamaye mata zuciyar ta najin baban ta ya haqura ya yafe mata gashi harda ma sa mata albarka,, jitai mama itama mama zainab tace "baba yawale bakomai ka'isa garemu ai fiye da komi ma na duniyar nan, dan haka nima d'in nayafe mata saboda kai, amman da sharadin karan kaina ban amunce mata ba dako kwana daya ne wannan shashashan yarinyar ta qara mun a gida ba, ta tashi tabi mijinta can gidan sa, kuma ki bude wadannan kunnuwan naki marassa ji kijini, to fa muddin naji kinyi wani abun wanda zai batawa abokiyan zaman ki rai ko kuma shi khaleepa d'in to Allah kuwa zamu sake gauraya dake ne dan ranki sai yafi nayau 6aci sakaryar yarinya kawai wacce batasan annabi ya faku ba" murmushi mamn meenat tai tace "ah adaiyi haquri komuda mama ne da baba dahara mu rakata dakin nata, mama zainab tace" wlh kuwa mmn menatu kinji na rantse babu wanda zai rakata,kuma ko wannan dukan danai mata ita tajawa kanta, banso ma na tsaya mata iya haka ba Inda naga alaman rawar kanta bai buyuyuwa da nasiha kad'ai, Inda ko an mata nasihar bata dauka dole sai an had'a da tab'a mata lpian jikanta snn za'a daidaita da'ita yarinyar kawai" baba yawale yace "kinada iko sosai akan heenduh zainabu dan haka komi kika yanke yayi Allah sa shine mafi a'ala akan tafiyar ta dakin nata yanzun kuma hakan amin,, kama hab'a baba dahara tayi tace "o'oni heenduh kinjawa kanki kinga mamanki ta hana mu rakaki bare na koya miki kwalliyan zamani kina cancarewa,, dariya mgnr baba dahara ta basu dan kuwa sunsan wasa ne kawai baba dahara d'in ke mata dan haka nan take su baba yawale suka dungayiwa heenduh da khaleepa nasiha kan sabuwar rayuwa da zasu fara, sosai nasihan ta dinga ratsa heenduh har batasan wani kukan ya sake kutto mata ba kuwa ta cigaba da yinsa.. daga qarshe suka umarcesa daya dauki matarsa su tafi Allah basu zaman lpia..... haka su mmn meenat da mmn sales da baba dahara suka rakosu har mota babu wasu kaya dauka dauka wanda ya danganci heenduh Inda daman tun ran safiyan juma'an data gabata aka rigaya aka kai mata kayan nata... dazasu tafi nanma saida baba yawale ya rufe taro da addue dan cika sunnar manzo kan hadusin dayazo yayi mgn da cewa turr da majalisin da'aka zaunasa tundaga farkonsa har qarshensa sannan aka tashi ba'a ambaci Allah ko manzon saba ciki, tofa anyi alla wadai da zaman nan. suna shafa addua'n ko a haka heenduh tana kuka su mmn meenat suka fito da'ita daga cikin gidan suka saka ta mota khaleepa yashiga motar shima yaja suka tafi sai bye bye su mmn sales suke musu har suka qule sannan kuma su mmn sales suka dawo suka samu mama zainab nan zaune Inda suka barta,nan suka ci gaba da qara tattaunawa kan batun, yayinda tuni daman baba yawale yawuce shi gida abinsa ransa qar farin ciki naganin cewan yau Allah ya cika masa burinsa da ransa yaga tarewar zaman auran heenduh da khaleepa koba komi ya cika alqawalin daya daukarwa kansa na bayyanuwar gskia kan auran jariran yaran, manya kuma a yanzun, duniya knn komi lokacin sa yake ci, a haka yashiga gidan nasa ya kullo. su kuma su dady mukhtar suna can zaune cikin sit room d'in baba isma'il suna cin abuncinsu kamar yanda suka saba, zuqatansu fall farin ciki fira kawai suke hankali kwance, sai bayan sun gama ne suka fito itama baba dahara harta yi musu bankwana ta wuce gida zuciyarta cikeda tunano baba yawale kuwa dan zaman da sukai yau tareda shi baqaramin tsaya mata yayi a rai ba, dan haka tana murmushi itama harta shige gidanta ta rufo sa da yake jikokin nan nata sun gama hutunsu sun koma. dady sales suka shiga motarsa shida mmnsa da mmn meenat suka wuce gida saida suka fara ajiye mmn sannan sukai bankwana suka wuce gida suma can bayan layin su maman knn.. baba isma'il kuwa har qofar gida yaraka yayan nasa snn sukai bankwana shi ya dawo ciki shi kuma dady mukhtar din ya wuce kowa zuqatansu fall farin ciki a wannan dare tunbuna ma mama zainab din da baba isma'il kwanan farin ciki sukai a daren. khaleepa kuwa tunda aka kawo zarah gidan bai tako qafarsa ba cikinsa ba dan ya fada Mata itama a waya tafiyar tasa Abuja kmr yanda ya fadawa su dady mukhtar da momynsa kuwa sa'ilun da yake cikin tasku kwana biyu da suka wuce, to sai fa yau a rana ta uku da tarewar zarah a gidan yaduro a cikinsa. dakansa yakai heenduh har dakinta tanata kuka kuwa wanda shi harya sare wa rarrashinta kuwa, a haka ya qyaleta snn yasake saukowa qasan falon yasake ganin babu dai kowa dai a cikinsa kamar yanda suka wutosa yanzun, banda qarar esi kota'ina a falon bakkajin motsin komi, dakinsa shima ya wuce yashiga wanka ya fito ya saka jallabiya ya shinfuda sallaya yafara salla. zarah kuwa tun shugowarsu cikin harabar gidan take tsaye ta saman window d'in tana kallon su,kallon ta ta maida ga heenduh ganin yadda ta qara mata haske da kyau gamida cika tamfar ta manyan yan mata yasata jin wani sabon tsanarta maras algus ya lunku cikin zuciyarta, ranta ya bata babu shakka kuwa tare da ita yayi tafiyar a Abuja Inda gashi sun dawo gida tare. amman a fili murmushi tai sanda ta tuno kalar tarkon d zasu datsa mata muddin mlm lamma ya dawo kuwa to tabbas tata ta qare saitaga qaryar feleqe da iskanci gamida mannewa miji uwa gum. ganin sun yo cikin falon gidan wato ta daina ganin su hakan ne yasata komawa bakin gado tana zama kuwa saiga kiran hjy furdausey ya shigo wayar tata, tsoki tai tareda furta "mtssss tsohuwar banza nifa yanzun bakida wani amfani da zaki mun a rayuwa Inda har kin sake kin mallaka min danki dai, tsoki ta qara ja tareda katse wayar kai tsaye ta kirawo mamanta hjy hadeeza, kamar jira take uwar ta dauka nan ko ta fara cewa" momy nifa iskancin nacin da kiran wannan tsohuwar guzumar qawarki da take isana dashi kulluyaumum walailatun yafa fara isana, haba mace sai nacin son
Chapter 161 · 0% Book details