← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 178

Sashe 140

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👁🥡👁 🅿5⃣9⃣. *G* anin da khaleepa yai momyn tasa sai faman kakkafewa take qarayi hakan ya sashi saurin duban dadyn nasa cikin wani sabon tashin hankali yake furta"dady...dadyyy mumu... mukaita asibitin mu kawai...yana mgnr ne tareda kinkimota cikin hannuwansa yai mata daukar jinjirai ya tallafota yafito dasauri yayinda dady mukhtar yafito cikin sauri yashiga motar yajasu zuwa asubitin, salati kawai ke fitowa a bakinsa dan hankalinsa yayi mugun tashi gskia, dandai yasan matar tasa batada jinnu amman dayace sune suka taso a jikinta yanda take wannan kanannad'a haka. suna isa aaibitin dasauri nurse ta turo gado wanda khaleepan yakirata tun suna hnya data zama ready daman. dan haka dakansa ya daura momyn nasa a gadon daukar marassa lpian yanufi emergency room din da ita yayinda dady mukhtar ya zauna saman wata kujera yama rasa abinda ke masa dadi kawai saiya tura tafukan hannuwansa cikin fuskarsa. yana nan zaune sama da awa 2 wato wuzin sha biyu saura na dare knn sannan khaleepa ya fito daga dakin daya shigar da momyn tasa jikinsa sai gumi yake faman tsattsafowa dan hatta farar rigar lolikitocin dake jikinsa saman kafadarsa ya ratayota. zama yai kusada da dadyn nasa tareda jingina bayansa a kujerar sannan ya saki wata qaqqarfan ajiyan zuciya tareda zare medical glass din idanunsa yasa hankicerf yashare gumin fuskarsa. dafa kafadan dadyn nasa dayai ne tareda furta"dady" hakan ne yasa dady mukhtar saurin janye taguminsa yajuyo yadubi khaleepan danshi kam kwata kwata ma baisan ya fito ba. cikin muryar karaya yace"yajikin maman naka danna soma fidda rai ma ganin shurun tayi yawa dan masallacin kun can naje har na dawo kuma najima banji motsinka ba" ya qarashe mgnr tareda shafe zufar goshinsa da bayan hannunsa dudda easi dun dake wajen kuwa. saida khaleepa yayi dan shuru na tsawon minti 3 sannan ya jinginar da kansa a kafadan dadyn nasa murya a kasalance yace "dady mummunan hawan jini ne ya shige Momy lokaci daya wanda yakusan zuwa qarshe sosai, badan Allah yataimaka ba dady zuwan namu asibitin nan kan lokaci dababu abunda zai hana momy kamuwa da cutar faralize, ciwon baren mutuwar jiki ya sameta,,dan da alama mgnr da mukai ne a gida ya bugeta sosai, amman yanzun Alhamdulilla dady komi ya dawo mata lpia lau tama samu sauqi zuwa gobe da safe zata iya komi da kanta dan barci take yanzun sakamakon injections danai mata dasauran abubuwan daya dace" sauke ajiyar zuciya dadyn yai tareda hamdalla na sauqin da ubabgiji Allah ya saukar musu dashi. cikin karewar zuci khaleepa yasake duban dadyn yanajin babu dadin abun da zai sake fitowa daga bakinsa dangane da wani ciwon na daban dake jikin momyn, dandai kawai babu yanda suka iya da qaddarar ubangiji ne. daqyar yabude baki yace "dady Momy na daukeda cutar ciwon sugar a jikinta a binciken danai, dan har ma yafara nisa sosai a jikinta,, dady..dady ina tsoron Momy taji wani ciwo a jikinta gudun matsala ta rashin warkewa ga cuta.... dakatar dashi dady mukhtar yai yace "komi kaga Allah ubangiji ya daurawa bawansa hakan yana nufin qaddarar sa ce ta rayuwa wanda daman a rubuce yake watom cikakken musulmi shine mai iya jure haqurin zaman qaddarar da mahallincinsa ya nufesa da ita domin gwada imaninsa, dan haka kada kasa damuwan hakan aranka Allah zaiyi maganin abun da iyakarsa tazo" wani sanyayyen numfashi khaleepa ya sauke yace"to dady kuma zan duba magungunan daya kamata tadinga sha dan raguwar ciwon a jikinta cikin ikon Allah ma zai iya barinta in akai dace" "Allah sa to haka ake fata ay" "Ameeen dady muje nakaika gida inyaso saina dawo dan daman zan kwana wani aikin kuma anan asibitin zan dinga kewaya momyn kozata farka ta buqaci wani abun" girgiza kai dady mukhtar yai yace "hakanma yayi to, amman kabar motar a hannunka danko munyi waya da dadynka salis yana hanya ma yanzun zaka gansa inyazo kaga saimu wucen kaiba saika fito b...katsewa mgnr dady mukhtar tai sakamon kiran dady salis din dayagani yashigo Wayar tasa, nan danan Kuwa yai saurin dagawa da fadin"assalamu alaikum ka'iso ne hospital din salis?" daga can dady salis yace"eh mukhtar bansan bangaren da kuke bane ka fito gani nn moto park na asibitin" dady mukhtar yace"OK gani nn fitowa to ynzun" "OK saika fito" Cewar dady salis din suka ajiye wayar atare. tareda khaleepan suka fito anan dady salis yai musu yamai jiki dady mukhtar ya amsa da fadin"ay mai jiki kam alhamdulilla dasauqi dan tama samu barci zuwa gobe da safe zan dawo insha Allah, zamu tafine yanzun dan khaleepan shi yanada duty ne na dare. "To shiknn saimu wucen goben dasafe madawo tare" cewar dady salis. haka khaleepa yajuya yakoma asibitin bayan sunyi sallama da su dadyn sun wuce suma. office dinsa yanufa yana tafiya yana sake trying number heenduh still tana rufe ake ce masa, tsokin haushi kawai yai tareda jefa Wayar aljihunsa ya'ida nufa office din nasa dan fara shirin ayyukan dazaiyi. tun da dady mukhtar yayo sallar asuba ya dawo yazo nan falo saman kujera ya had'a tagumi danjinsa yake yau tun tashinsa uwa wani sabon mutum dabn wanda aka daukewa kaya masu tsananin nauyi saman kansa, sosai yake jinsa kamar wanda ya farka daga wani dad'ad'd'en nannauyen shekararren mafarki marar dadi. dan sosai hotunan abubuwan dayaita yiwa iyayensa musamman ma dan uwansa qaninsa Ismail yanda yabanzatar dasu yazamana ma babu wata kyakkyawan alaqa atsakaninsu face ta zallar rashin mutunci dayaita danqara musu... babu zato yaji hawaye na zuraro masa a fuska wanda rabon da hawaye su sauka fuskarsa zai iya cewa tun na yarinta danko su baffa dasuka rasu bazai iya tunawa yayi kuka koko baiba. afili yake cewa da qarfi "miya faru dakai ne mukhtar ka zamowa dan uwanka gurnanin zaki? miyasa kagaza cigaba da qaunarsa da tarairayarsa gamida basa dukkan jin dadi na dukkan rayuwa kamar yanda ka faro masa daga farko miyasa?! Miyasa?! Miyasa?! akan mi hakan yaita faruwa waye silar faruwan hakan kuma tsakaninku mukhtar?'' tambayar dayaita yiwa kansa knn yagaza samo amsar Kuma,, sosai yaqara runtse idanunsa sanda ya tuna mummunan fad'an bata kashin dasikai da qanen nasa akan mallakin gidansu su dukansu na iyayensu amman ya qwace?? dakuma sanda yasa aka koresa a makarantar dayake teaching bacin yasan teaching shine burin qanen nasa a rayuwa? yanaji yana gani kuma qanensa yake kwana da yunwa dudda dumbin dukiyarsa kuma? saidai ya 6uge da seda cefane a bakin hanya yana samu yana cigar da iyalensa wanda ahakan ma baqinciki yake masa kuma dai? kuka sosai dady mukhtar yakeyi har ya sauko nn qasan carpert din yanayi sakamakon sauran kalar mummunan wulaqancin da kwanyarsa taita tunowa yaiwa qanen nasa naqin qari miyasa hkn? gakuma babban tashin hankalinsa yanda iyayensa har suka rasu da baqincikin sa arai batareda ya nemi gafararsu ba? kuka sosai yaitayi babu qaqqautawa kamar yaron goye wanda hakan yasa masa jin saukar masasara mai kyarma ta kamasa gawani ciwon kai,,,daqyar yatashi yaje yasha magani ya dawo ya kwanta nan qasan tiles dudda sanyinsa kuwa dake damun jikinsa sakamakon masassarar daya saukar masa amman shi sam hakan bai damesa ba danji yake to miye amfanin kwanciyarsa waje mai laushi alhalin qanensa gudan jininsa nacan yana saka haqarqarinsa cikin gurarun daki dababu ko arziqin suminti a cikinsa sakamom zaizayewa dayai. (dan shi a tunaninsa har yanzun isma'il na cikin zafin talaucin daya sanshi dashi a baya shiyasa yake tunanin hakan) haka yaita sambatu yana cewa''wayyo Allah na nacuci kaina da kaina ni mukhtar.... haka yaita yi gwanin tausayi kamin yasamu barci ya daukesa, wanda baisamu maganin yasakesa ba saida misalin qarfe tara na safia. tashi yai zaune yai zuru, saigashi cikin ikon Allah ciwon kuma yasauka saidai kuma har lokacin babu tunanin komi aransa daya wuce yaga yasaka qanen nasa a idanunsa yanemi gafararsa ko Allah yasa nutsuwar kwanciyar hankalinsa datai qaura daga jikinsa tadawo masa. tunanowa yai da asuba daya fito daga masallaci har sau wajen uku yana zuwa qofar gidan Ismail din amman saiyaga baiga gidan ba saima wani tsantsararren gida mai dutsi daga waje sabon gini a gidan dayasan na Ismail dinne kuma a da, sosai yaita mamaki a ransa lokacin na tunanin kodai Ismail siyarda gidan yai yabar anguwan? tunanin hakan dayai kuwa baqaramin fad'ar masa da gaba yaiba na tsoron cewa Allah sadai ba garin suka bari ba inda baisan Inda zasu koma ba bare yasaka komar nemansa shi da iyalin nasa. ahaka yamiqe cikin kasalar jiki yayo wanka ya shirya ya fito cikin shigarsa ta kamala kaida ganinsa kaga babban mutum wanda tsaban hutu da nera suka gama bin jikinsa suka shanye, anan ya dauki makullin motarsa ya fita gidan cikin motarsa kai tsaye qofan gate din gidan dady salis yatsaya inbai mantaba kamar yanda yashiga gidan a daren jia byn sunje sun dawo daga gaido maman salis din dan haka yakega kmr nan ne qofar gate din gidan salis din. amman dan kawar da taraddadin sa yasa ya fuddo wayarsa yakira number dady salis din yashaida masa gashi qofar gidansa yazo. babu jimawa saiga dady salis din kuwa ya fito cikin fara'a yaqaraso inda dady mukhtar din yafito yake jinginr a jikin mortar tasa, suka kama hannun juna sukai musabuha sannan cikin murmushi dady salis yace"ay saika shigo ciki kayi breakfast ko dan nasan tunanin madam bazai barka cin wani abun ba sosai danni nazata ma sammakon fitowa zakai ay muje asubitin dantun dazun nashirya ma ni" wani dan guntun murmushi dady mukhtar yai yace"kamin nan inason kagayan ina qanena yakoma ne dannata zuwa gidan banganin gidan saima wani sabon gini awajen" wani sanyayyen ruwan farinciki ne dady salis din yaji a ransa na murnar jin abunda mukhtar ke fada yau da bakinsa, nason ganin qanen nasa abin mamaki, lallai kam mai roqon Allah baitaba tabewa a rayuwarsa komin tsawon lokaci kuwa haka batun shike. amman afili saiyai shirin waina mukhtar din dan haka ya tsuke fuska kadan sannan yace "ni sanda ma na dawo garin nan nima ban iskesu ba dan jinai jama'a na cewa anwayi gari ne aka nemesu aka rasa har zamn yanzun kuwa babu labarinsu da'aka sakeji....habawa ay tunkan dady salis ya'ida zancen nasa dady mukhtar ya cimamiyo kwalarsa a gigice jiki na rawa idanunsa na yoyon ruwan hawaye murya na rawa yace"kaddai kacemun qanena yayi duniyarsa yabarni salis?
Chapter 140 · 0% Book details