← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 178

Sashe 102

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ba a kyakkyawar fuskarta da jikin taba?hmnn wannan mgnr taka sak zancen qanzon kurege ce wlh, kuma nadai fahimci bakka son shigar dani wajen sister din nan taka kuma wlh baka isaba bazan janye ba danni naga mata muraran" sosai khaleepa yake kallon doctor mus'ab da jajayen idanunsa da tsananin kishi yasa suka rikid'e masa lokaci daya, jikinsa har wani d'an rawa rawa yakejin yana masa, kamar zai masa kutofu na d'an banzan duka a yanda yake jinsan nan yakeji. damtse hannunsa yai da idanuwansa yana budesu kuwa dariyar da doctor mus'ab ke masa ta tsaya cak sakamakon sauyin halittar khaleepa dabai taba gani ba kamar yau, tuni yaji wani tsoro tsoro ya shigesa farat daya a dabarance ya matsa daga gaban khaleepa ya fara tafiya yana cewa ''kadaije kai tunani abokina dan nasan kasan niba mutumin banza bane bare ka hanani qanwar ka,na barka lpia ni" wani dogon tsoki khaleepa ya saki bayan ya ware hannunsa daya dunqule ya shiga motar yai mata key. jinsa yake dud ya jiqe da gumi ma, a.c na motar ya qaro bayan yasa hankicerf ya share zubar fuskarsa data wuyansa fadi yake a fili "please doctor mus'ab please kada ka bari na tsaneka kan wannan b...maganarsa ta katse jin wayarsa na qara ganin momynsa CE yasashi daidaita nutsuwarsa ya d'aga tunkan yace wani Abu yaji tace "hankalina ya tashi mai tsada na sa'ilin Dana duba na tabbatar ba'a gida ka kwana ba Allah sadai ba wani abun bane dannaji kamar ina fad'uwar gaba tun tashina da safen nan wlh?" Wani kalar d'an murmushin dole ya q'aq'alo Wanda iyakarsa geffan fuskarsa d'aya sannan yace"kada kidamu Momy kinsan ai kalar aikin namu babu yanda bai juyawa , to yanzun na koma dutyn dare can zandinga kwana asubiti kan wani lokaci, dan yanzun ma haka gani nan tafe d'aukar mana breakfast, kinsan nafison cin naki girkin Momy na shiyasa na yanke shawarar zandinga zuwa karbar breakfast nawa hadadde a gunki har nagama dutyn nawa na dare na dawo" yayi wannan dubarar ne kawai danya samu breakfast yanda Yakama ta bangaren sa da headache da kuma su Baba yawale yanda basai tasha wahalar girki ba kokuma shi yasha wahalar zuwa siya. jiyai tace"mai tsada na hakanma Shawara CE amman jia da daddare zarah kecemun taga kamar motarka kofar gidan matsiyatan can fa?". runtse idanunsa yai yana jin ciwon abunda momynsa kewasu baba Ismail sosai matuqa, kuma gashi wannan munafukar zarah harta gani taje ta zartar mata inko hakane dole yadaina shigowa da motarsa cikin anguwar nan tasu inda munafukai sun soma fiddo Kansu dan yana gudun nan gaba baisan kuma mi za'aje a CE mata ba, gwara kawai yadinga kai motar wajen ajiya anan bakin titi daya tashi kawai saiya dauka ya wuce babu Wanda yaji bare gani kuma. amman a fili sai yace"a'a Momy bani bane sudama basa nan sunyi tafiya". yanaji ta sauke ajiyar zuyciya sannan tace" yawwa to shikenan, yanzun zaka qaraso daukar kalacin ne?" "Eh Momy ganima nakusan qarasowa, amman Momy zakina hadawa da dan yawafa daga gobe dan harda abokan aikina fa zan dinga zuwa daukar mana". "to shiknn mai tsada na saika shigo bari nashiga kicen din dan da kam banyi niyyar Shiga ba". ''yawwa Momy na thanks soooow saina iso" nan ya sumb'aci wayar sannan yakashe yana murmushi tareda shafa sumar kansa yadaki styaring motar yace "yesss yes" ahaka yaci gaba da tuqin harya iso nan titin anguwar tasu yakai motar a place take motor park ya fito yazagaya ta baya ya bude gidan baba Ismail din ya shige tareda maido qofar ya rufe harda kuba. dasauri ya shiga dakin jin kakarin aman da takeyi, isketa yai nan a bakin katifan ta sauko a galabaice. a rud'e yake mata sannu bayan matseta dayai gam cikin jikinsa kamar zaiyi kuka. Sam takasa ko d'agowa ta dubesa kanya Ankara tuni har ta fara feso masa amai a gaba dayan jikinsa,, baiji qyama ba haka yaqara riqeta cikin jikinsa harsaida ta gama aman nan sannan yad"ago fuskarta ganin idanunta sunyi luu luuu ne tana shirin komawa ta zube masa yasashi saurin sake tarota cikin jikinsa ya gyara mata jikinta sannan ya mayar da ita bisa katifar ya hada wasu sabbin alluran ya jona drip a qusar bangon dakin sannan yasamata qarin ruwa ganin yanda dud jikinta yai mata yaushi alamun son ruwa yakeyi, gyara wajen yayo wani wankan ya canza Maya snn yadawo ya zauna gabanta gamida tagumi. kallonta kawai yake ganin yanda tayi wata 'yar rama lokaci d'aya, fuskarta taqara haske sosai kuma. ahankali yasa hannu yana gyara mata gashinta da iskan fanka ke kad'asa yana sama da kuma sake dawowa yana shafar jikinta kota 'ina...... barcin datakeyi ne yasashi sauke ajiyar zuciya, shima kansa a d'aura a saman qirjinta tareda shigewa cikin jikinta gabansa na wani kalar bugawa dammmm!!!! dammm!!! batareda yasan amsar hakanba, yadaiji a jikinsa wani mugun sonta ke fuzgar rayuwarsa Wanda haryaji baiqi sun dawwama a hakanba muddin ransa batareda ya sake morar wani 6angare na jikinta ba. " hakan kuwa shine haqiqanin so a rayuwa kaso mutum badon wani abu nasa ba daya mallaka a rayuwa na kyau ko kuma dukiya ko ilimi" abinda zuciyarsa tafad'a masa knn, sosai yaqara shigewa jikinta kamar mai tsoron wani zai qwace masa ita..... Ahankali yadago da fuskarsa yana kallonta har baisan sanda bakinsa ya su6uce yai mata sabon suna nan take yakirata da "lollipop d'ina" ba'a bayyane...
Chapter 102 · 0% Book details