← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 175 OF 178

Sashe 175

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gani na tattara kayana da matata nabar garin muna kuka nida qanena,, to babu Inda na sauka sai garin kaduna, dan ji nai qwara nima nayi nisa da gida kona samu kwanciyar hnkali, cikin ikon Allah harna shigo nan anguwar neman matsakaicin gida wanda zan siya dan inada 'yan kud'i na na shanu na dana siyar da wasu daga cikin su a satin, anan ne Allah ya had'ani da mahaifinku kai mukhtar, shine yayimin hanyar samun gida anan layinku harna siya muka zauna cikinsa muna rayuwa nida matata, sosai muke zumunci da baffanku dan dud anguwar nan dama garin gaba daya banda amini kamarsa wanda na yarda dashi shima kuma ya yarda dani, mafarin knn dana fada masa shida inno taku abinda ya raboni da gida, lokacin ku kuna qanana baku fara mallakan kanku ba sosai, haqiqa sun tausayaman wanda tun daga lokacin mahaifunku yaqara jawoni jiki sosai ya zameman dan uwa shaqiqi, kuma gefe guda ga addua dayaketa mana kan Allah maido da hankalin mahaifina gareni. haka al'amurra sukaita faruwan hardai kawo rasuwan matata da kuma ta iyayenku data biyo baya har xuwa yanzun dai kuma ayau din nan danake muku wnn mgnr" baba yawale ya qarashe mgnr tareda goge wasu 'yan siraran qwalla. sunji tausayinsa sosai wanda babu wanda bai share qwalla ba a wajen. " hmnn duniya knn" abinda baba yawale yace knn yana qaqaro murmushi, snn yace "gobe insha Allah zanje garinmu wajen qanena muntari da sauran iyayena su ganni nima na gansu ko hankalina ya kwanta. cikin jimami dady mukhtar yadubi baba yawale yace" yanzun baba shikenan tafiya zakayi ka barmu bacin mun saba dakai muna ganinka a mazaunin uwa da uba namu munajin dad'i kuma? "yaqarshe mgnr yana hawaye. cikin mgnr kuka shima baba isma'il yake cewa" dan Allah baba mun roqeka kada kace zaka tafi ka barmu, inka barmu muma zamu bika ne"! "dady sales cikin karayar zuciya yace" kadubi koken mu baba ka haqura ka zauna cikinmu dan girman zumuncin dake tsakaninku dasu baffa kada kace zaka tafi ka barmu" murmushi baba yawale yayi yace "ku kwantar da hankalinku, dannaga dud hankulanku sun tashi danai muku mgnr tafiyar tawa, to baccin abunku ma ta yaya zan tafi na yarda amana? alhalin aminina baffanku daya danqan amana taku a hannuna sannan ace kuma na watsar na tafi na barku? toni ba haka nike nufi ba da mgnr tafiya na gida, nufina shine zanje naga 'yan uwa da abokan arziqi snn na dawo da fatan kun fahimci zancen nawa yayana? "yaqarashe mgnr yana 'yar dariya kalar tasu ta manya. kowa dake wajen saida ya sauke ajiyar zuciyar farin ciki dajin dadin abinda baba yawale d'in ya fad'a. cikin murmushin dariya heenduh ta taso daga Inda take zaune ta koma gefen baba yawale ta zauna tace "hmnn nasan ay daman mai ran qarfe bazai iya tafiya ya barmu ba, hmnn kaga su baba dahara har jiki ya mutu tsohon masoyi zai gudu,, d'an dukan wasa mama zainab ta kaiwa heenduh aiko tayi saurin riqe baba yawale suna dariya ita dashi, mama zainab tace" bakida aiki sai tsokana ko? cikin kunya baba dahara tace "rabu da ita zamu gauraya ne ai zainab" suma su dady mukhtar dariya sukai yayinda khaleepa murmushi kawai yayi yana cigaba da kallon heenduh ta qasa qasa wanda sam ita bama ta lura da kallon nasa ba hankalinta naga su baba yawale. dady mukhtar yace "muma saimu fara shiri daga yau dan gobe in Allah ya kaimu lpia muraka baba zuwa garin ku muma mu gaisheda dangi." dady sales har hada baki suke shida baba isma'il wajen cewa "hakama yayi" sosai baba yawale yaji dadin hakan kuwa. sunjima suna zaune a wajen sannan daga bisani baba yawale ya wuce gida khaleepa yabisa a baya, da yake can yake kwana saida safe ya dawo gidan baba isma'il d'in. sosai yaso ya keb'ance da heenduhn tasa amman ina babu dama sbd har lokacin tana tareda iyayen nasu, yana lura sadda zai fita suka hada Ido har gwalo tai masa dan itama ta ankara da ma'anar kallon da yake mata zuwa yanzun, girgiza kai yayi tareda sakin wani boyayyen murmushi alamun zasu had'u kenan, dariya tai tareda qara zama a gefen jikin baba dahara ta lumshe idanunta danta fara Jin barci sama2, batasan miyasa takejin kwatankwacin abubuwan da ta dinga jiba a jikinta lokacin da take dauke da cikin baby baby neylar ba, bambancin d'aya ne amai da batayi, saidai tarin kwadayi daya qara tarar mata, gashi nan da nan taji yunwa, dan komin dare inta farka saita nemi abinci taci snn take samun nutsuwa, dan jiya ma da kular abinci ta kwanta gefenta da nufin in yunwar dare ta katsota taci basai ta fita ba cikin daren ba. saida su dady mukhtar suka jima snn suka tafi gida shida dady sales, dan kan lokacin har mama zainab da heenduh sun jima ma da komawa cikin gida, itama baba dahara harta tafi. washe gari kuwa suka shirya cikin motocinsu, wato dady mukhtar da dady sales gamida baba isma'il sai baba yawale suna cikin mota d'aya wacce dady sales ke tuqawa asaman hanyarsu ta tafiya garin su baba yawalen, saikuma d'ayar motar khaleepa ke driving dinta, da yake motar mai fadin bayan nance shiyasa ta amshesu ba takurar komi, yayinda heenduh ke gefensa sai kuma acan baya mama zainab ce da baba dahara sai kuma mmn meenat da'ita menat d'in kanta, heenduh kuwa kad'an kad'an ta juyo ta tsokani baba dahara da mata tsiyar cewa wai zataje gaisheda dangin miji.... yayinda baby meenat keta qyalqyata musu dariyar, baba dahara kuwa a haka taita biye musu, suna fira suna raha. khaleepa ko sai d'an danne qafar heenduh yake alamun tai shiru ammn cakwaiwaiwar taki kulasa, a haka har suka iso rugar. sosai baba yawale yaga rugar tasu ta qara canzawa da girma sosai, dan hatta yawan bukkokinsu sun qara qaruwa, haka sukaita wuce shanu da awakai baba yawale yana nuna wa dady mukhtar hanya har suka iso qofar fadar baba ard'o wato mahaifin baba yawale. suna fitowa kuwa daga motor suka doshi wajen da jama'ar dake fadanci a wajen suke zazzaune, karab baba yawale kuwa suka hada ido da d'an uwansa qanensa muntari a karagar mahaifin nasu anmasa nad'i ga alama shine shugaban yankin yanzun, shima muntari ya shaida yayan nasa dud tsawon shekarun da aka dauka kuwa basu mance kamannin juna ba, Allah sarki nan da nan suka rungume junansu suna kukan farin ciki wanda sauran jama'a ma sukaita mamakin yanda yawale ya dawo, dan harsun fidda rai dashi kamsu tuni, nan da nan wani babban bafadan muntari yayi cikin gida da gudu babu jumawa sai gashi sun fito riqeda hannun ard'o wanda ya tsufa sosai tukub tukub harda makanta a idanunsa bai gani sosai. yana fitowa sai laluben hanya yake yana cewa "ina yawale d'in nawa yake? kazo gareni yawale na najika a jikina, konaji dadi nayi farin ciki wanda na juma ban yisa ba tun bayan tafiyarka..." da sauri baba yawale ya riqe baffa ard'o d'in nasa yana hawayen farin ciki dan ganin cewa baban nasa ya dawo hayyacinsa, cewa yake baffa gani nan baffa, dasauri baffa ard'o ya qara ruqosa sunata kukan murna, haka jama'ar gari sukaita zuwa yiwa ard'o barka da dawowar dansa babba. saida suka shiga cikin gida aka musu masauki suka hutu aka damo musu fura suka fara sha, ard'o yabada umarnin a yanka kaji 20 a soya musu, sannan a soya musu qwai shima 30, kankace MI har an gama musu wannan hidiman, dud abin nan da ake kuwa baffa ard'o na riqe da hannun baba yawale, yayinda muntari qanen baba yawale ke gefen baban nasu, ma'ana sunsaka ard'o din tsaka, su kuma su dady mukhtar an shimfuda musu babban tabarma suna zazzaune akai kowa nashan furarsa wacce taji nono na usuli, har wani qamshin dadi furar ke futarwa, ga qanqara da'aka dama musu da'ita, shiyasa koda aka kawo musu soyayyen qwai d'in da kajikan nan ba wani cinsu sukai sosai ba, sai bayan an gama komi ne an nutsu baffa ard'o yaita neman afuwan d'an nasa baba yawale akan abinda ya faru batareda hankalin saba, baba yawale shima ya nuna komi ya wuce harma yana tambayar ina goggo shatu d'in, anan ne muntari yake cewa ai tun bayan tafiyar sa bada jimawa ba cikin ikon Allah shima d'an ta rabeey datake d'aurewa qugu yana wulaqan ta kowa yaso a cikin garin ya shiga harkar dabanci, wanda daya giga ya fada daji yana tare mutane yana musu k'wacen dukiya, wanda in sun qi basa kuma ya kashe su, to ana haka ya samu daidai shi, ya tari wani hatsabibin bokan mutum mlm ne, anan yayi maganinsa ta hanyar sakar masa da wani mummunan asiri wanda babu arziqi rabeey ya dawo gida jinya, magani babu wanda ba'ayi masa ba amman ina sauqi sai wajen Allah, wanda ko kwana 50 bai haura da dawowa ba ya rasu, koda yarasu babu wanda yayi masa kuka sai uwarsa goggo shatu, dan mutanen gari ma murna suka wuni yi sbd wanda ke addabarsu ya mutu, amman dud wannan isharar da goggo shatu ta gani bata saduda ta daina makirci ba, todayake Allah maijin qan bawansa ne sai gashi baffa da kansa ya ganowa idonsa sanda goggo shatu take zuba masa maganin a abuncin, a ranar kuwa ne asirin dataiwa baffa ya karye, daga nanne baffan yace taje gida ya saketa, haka ta fad'i a wajen tana neman yafiya wanda Sam baffa qin kulata yayi, saima cewa yayi sai yayi shari'a da ita akan saita gano masa d'ansa, daqyar mutane suka shawo kansa ya fasa kai qarar tata cikin kotun birni, sai gashi ba'a qulla shekara ba da rabuwarsu goggo shatu ta kamu da cutar kuturta wanda kowa nata ya guje ta, yanzun haka kullum tana can bakin hayin shanu tana bara" shiru muntari yayi snn ya d'aura da cewa "tsawon shekarun nan baffa yaqi qara wani auran danya rantse akan bazai qara aure ba, mata tsoro suke basa, haka ya dinga rayuwa kullum cikin kuka dare da rana yana adduan Allah maido masa d'ansa, wanda kukan ne yasa baffa makancewa baya gani sosai, tsawon shekara 30 knn da faruwan hakan, sosai su dady mukhtar suka tausayawa baffa ard'o, lallai in bakai sa'ar mace ta
Chapter 175 · 0% Book details