Sashe 136
Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
👁🥡👁 🅿5⃣8⃣. *S* aida ya kurb'i furarsa wacce ke gefensa cikin farin kofi sannan yasake duban su mama Zainab still murmushin sa na ga kan fuskarsa yace"dan haka wannan bawai wani abun damuwa bane dazaku tashi hankulan Ku akai" mama Zainab ta dubi kaka Jameela yayinda itama kaka Jameelan tajuyo dubanta ga mama Zainab sannan kuma lokaci daya atare lokaci dayan dai suka maida kallonsu ga baba yawale din kowacce zuciyarta na tunanin wacce mgn baba yawale ke yi haka na wannan mummunan abun daya samesu amman yake cewa su kwantar da hankali? kodai tsufa ne yake fada masa sabanin abinda suke fada masa yayinda hankalinsa na rudun tsufa yagaza fahimtar ma'anar babban mgnr da suka zo masa dashi ynzu. jisukai yace"kada kuyimn wata fassara Zainabu da mamanki dan cikin hankali na nike baku wannan amsar kudai kudan dakace ni harshi isma'il din ya dawo saimu ida tattauna mgnr tamu, zanje masallaci jan jam'e yanzun saina dawo" yayi mgnr tareda miqewa yana saka takalmansa roba masu rufi blue. "To" abinda sukace knn cikin qarfin hali, binsa sukai da kallo harya fita sannan ne kaka Jameela ta sauke ajiyar zuciya a fili "gskia kam dai din *da sauran kallo* a gabanmu, Allah kawo shi Ismail dindai lpia" cikin matuqar alhini mama Zainab ta janye tagumin ta itama ta kawo ajiyar zuciya tareda furta "Aminn mama" tana mgnr ne kawai tana kallon heenduh wacce ta miqe tadauki buta tashiga bayi. tana fitowa tai alwala suma suka miqe sukayi alwalar dan sallar la'asar din. sunjima dagamawa suka zauna jugum jugum bamai wa wani mgn. acan waje ko baba yawale koda suka fito masallaci nan ya zauna shida dady salis saman dakalin qofar gidan nasa suna fira. lokacin qarfe 5:22 na yammacin ranar. hamdala baba yawale yai a zuciyarsa na hango motar baba ismail dayai tana parking can gefen gidansa Inda yasaba ajiyeta. baba Ismail na futowa motar da jikkarsa a hannu yakuwa hango su baba yawale din mafarin knn yadoshi wajen yana murmushi faffada a fuskarsa. da sallama yaqarasa wajen suka amsa masa suma fuskokinsu cikin annushuwa. yana niyyar zama ne saman dakalin shima anan baba yawale yayi saurin dakatar dashi da fadin"a'a isma'ila kada kakai ma ga zaman nan muje ciki gida zamuyi wata muhimmiyar mgn dakai" duban baba yawale baba Ismail yayi yace"to baba bari nakai jikkar gida ko?" girgiza masa kai baba yawale yai yana kallonsa sannan yace "kada kadamu ay iyalan naka ma suna ciki" sosai kuma sai baba Ismail yaji jikinsa yayi d'an sanyi kuma yaqara tabbatazwa da eh lallai tabbas mgnr ba qarama bace kam inda har mata da 'yarsa na gidan baba yawale din kan batun. a sanyaye ya miqe tsaye shima ganin baba yawale din ya fara tashi shima. shima dady salis miqewa yayi ya dubesu sannan yace"toni zan wuce gida baba...baba yawale yai saurin katsesa da cewa ''a'a salisu ai dakai za'ashiga gidan kaima kaji batun inda dud dai an rigaya an zama daya babu zancen ayi wasa tare ci kuma yazo yazama banban, dan haka kumu shiga gidan dukanmu" har a ran dady salis yaji dadin rashin bambancin da baba yawale din bai nuna masa ba akan batun nasu na gida. dan haka binsa sukai suma suka shiga gidan cikin sallama. su mama Zainab suka amsa yayinda heenduh najin muryan baban nata tayi saurin qara cure jikinta waje daya gabanta na wata kalar azabben yankewa yana faduwa dasss dass. dukkansu zama sukai kan shimfidar baba yawale, sannan shimà baba yawale ya zauna yana kallon yanda heenduh dud tabi ta takura kanta, sosai ya fahimci bata nutsuwarta, dan haka yace mata cikin kalan wasan da sukeyi" amaryata kifa daina damuwa komi zai bayyana ne yanzun ay insha Allah, dan haka in kika kuma mana wani shesheqar kuka nan sainasa carbi nan nawa na dabaibaye miki baki dashi sainaga ta bud'esa ay kuka" yaqarashe mgnr cikin raha yayinda baba Ismail da dady salis suka musu dariya, ita kuwa har cikin ranta take furta cewa"shi wai baba yawale miyasa zai na mata hakan a wannan quncin taskun data tsinci kanta cikinsa? baisan wasa ma lokaci ne dashi ba... kwatsam taji saukar mgnr baba yawale nacewa"sama'ila da salisu kumu taya junanmu murna dan muna shirin samu qaruwa a cikin dangi ta kyautar d'a da Allah ubangiji buwayin sarki gagara misali yai mana akan 'yarmu heenduh" cikin baibai na rashin fahimta Su baba Ismail ke faman kallon heenduh da tunanin cikin a ruwa ne ake samunsa yanzun da baba yawale ke musu mgn akai? abinda sukaji baba yawale din na qara nanatawa shine yasa gaba daya jikinsu yin la'asar sanda kunnensu yasake juyo musu yana cewa"heenduh na dauke da juna biyu na wata biyu da satittika" amatuqar mugun zabure baba Ismail ya miqe tsaye a gigice yake fadin "ciccc...ciki kuma fa kace a jikin heenduh na baba?"! yana mgnr ne idanunsa sun kada sunyi jazur a wajen jikinsa naqara ciri. kamo hannunsa baba yawale yai na ganin halin dayake ciki uwa zai fadi sbd kyarma" "Kwantar da hankalinka sai kace bakaine dai ka aurar da 'yar taka ba kuma kasan hakan? to lokaci ne yazo ya nuna Kansa gashi jaririyar 'yar taka daka auras ta girma harta samu qaruwa tareda jinjirin mijin nan nata da aka aurawa to miye abun tada hankali daga cikin batun em?" wannan karan dagasu mama Zainab har baba Ismail din gaba daya daskarewa sukai da kallon baba yawale da tunanin kaddai fa ya bayyanawa yaran nan sirrin aurensu na jarinta har cikin nan yakaiga samuwa?, to in hakan ya kasance gaske kenan matakin da iyayen khaleepa suka furta musu zai hau Kansu muddin suka bayyanawa yaran gskia knn yakusan Hawa Kansu knn?????!!....katse musu tunani baba yawale ya sakeyi da cewa "heenduh dube ni nan" cikin firgita kuwa ta dago tana kallonsa danma ko iyayen nata ta kasa duba. "kiramun khaleepan ta cikin wayarki'' Abinda yace knn yana mai cigaba da lazuminsa a zuci da carbinsa a hannu. cikin rawar jiki ta bude jikkarta ta fiddo wayar ta duba number tasa da daman itace a sama sannan ta kira, tana fara ringing babu jimawa taji an katse wayar, batareda daukar second daya ba saigashi ya kirata.. dasauri tadaga Wayar hannunta na rawa wayar kmr zata qwace mata ma takeji dn ganin wani kallo da mama Zainab da baba Ismail me mata na tsantsagwaron mamaki. da rawar murya tace"ka...ka..kazo.. gidan baba yawale yanzun injisa" tana gama fadin hakan ta katse wayar batareda tama saurari amsar mi yake bata ba. dayake daman khaleepa fitowarsa knn daga gida bayan dawowarsa hospital yai wanka yaci abunci yafito knn cikeda azarbabin zuwa gidan baba Ismail din gun sugar din nasa sai kuma ga wannan kiran dole tasa ya cewa yunus yajirasa yana dawowa kaitsaye ya nufo gidan. cikin muryar sallamarsa ya shiga gidan bayan sun amsa anan ya zauna gefen heenduh qiri qiri ko kunyar iyayen baiji ba sai itace ma tadinga qoqarin janyewa daga garesa cikin basarwa yadunga janyo tafin qafarta alamun ta tsaya a hakan. saida yagaidasu snn baba yawale yace "Nasa akiraka ne daman dan nai maka wata tambaya khaleepa" sai lokacin ya lura da fyskokin su baba Ismail a jugumgumce, hakan yasa ya sake nutsuwa sosai tareda furta "to" "To alhamdulilla,,,cewar baba yawale din yana mai ajiye carbinsa gefe daya sannan yaci gaba da cewa "shin mlm khaleepa daman kasan kuwa matar ka heenduh na dauke da cikinka ko kuwa? daga farko ya firgita dajin wannan bazatacciyar tambaya daga baba yawale,, sai kuma yayi tunanin to miye? daman shifa jiran zuwan wannan ranar yake fata dan yagaji da boye boyen nan na aurensu gwara abasa matarsa dud wacce za'ayi inyaso sai ayi. dan haka cikin dakewa gamida Sosa qasan Kansa alamun kunyarsu baba Ismail sannan yace"eh baba najima dasani kamar yanda itama tasani" murmushin baba yawale ne yasake fadaduwa a saman fuskarsa sannan yace"masha Allah,, kukuma bari kuji yanda lamarin yafaro wanda har yaran Ku sukasan da aurensu da kuke boyewa wanda bakowa ne yafara fallasa hakan ba face kanwa mamar khalepan inkun fahimceni...nan take baba yawale yafada musu tun asalin farkon yanda su khaleepa suka ji mgnr daga bakin Hjy furdauseey sanda take fadawa qawarta harkawo zuwan da su khaleepan sukai wajensa da mgnr shi kuma ya sake tabbatar musu da haka batun shike har kuma zuwa damar dayabasu ta kasantuwa mata da miji adud sanda suka so hakan domin halalin juna suke sud'in tuni.. yaqarashe mgnr da cewa"to miye abin tashin hankali anan inda cikin nan da ubansa gashi kusa?" yayi mgnr yana mai sake sakin murmushi. daga mama Zainab har baba Ismail har kawo kaka Jameela wata sanyayyen ajiyar zuciya suka saki dan koba komi hankulansu ya kwanta dajin matsayin sahihancin Inda cikin jikin heenduh yasamu usuli kuma zarginsu yasauka a kanta na tunanunsu ko cikin waje ne dan basu taba tunanun cewa baba yawale din zai fadawa su heenduh matsayin junansu a garesu ba, hatta dady salis shima saida yai mamakin wannan auren jarinta haka da'akai musu dan baita saniba shima inba yanzun ba, kuma sosai yaji dadin hakan a ransa. cikin sake sauke ajiyar baba Ismail yadubi baba yawale yace"amman baba baka gudun abinda iyayen shi khaleepa zasuyi kmr ynda sukace muddin muka bayyana gskian lamarin nan?" "abinda Nike tunani nima knn wlh a zuciyata dan nasan halin Yaya fursauseey sosai ta dauki zafi kan haka, dady salis yace "zafi kamar yaya?'' atsanake baba Ismail da baba yawale suka bayyana musu abinda mukhtar yace shida maidakinsa kan batun Indai suka furta sa. tsoki dady salis yayi tareda cewa ''wannan kuma ba hujja bane...nan baba yawale shima ya katsesa da cewa"abunda nagani knn nima haryasa nakaiga bayyanawa yaran gskia dan lokacin dazasu santa kuma yayi, kuma wlh ko d'ar bazanji tsoron hukuncin da mukhtar zai yi Kn hkn ba" shiru baba Ismail yai zuwa can kuma wurin yai tsit sai muryar khaleepa dasuka tsinkayo yana cewa''insha Allah dady bazaice komi akaiba dan daman nayanke shawarar daya dawo zan fada masa komi da kaina. "Hakan yayi khaleepa gwarzon namiji haka akeso yazama ay ba tsoro" cewar baba yawale da dady salis. saida suka qara tattaunawa sosai kan batun sannan sukaiwa baba yawale sallama sika fito. kaka Jameela tawuce gida hakanan taji farinciki samuwan cikin heenduh dantanaji kamar cikin shine silan gyaruwan zumuncin