← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 178

Sashe 4

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

~Shekaru 23 da suka gabata~. *** Muku mukun sanyin da akeyi ne a jihar kaduna wanda ya sauko tun bayan gama sallar asubahi hakan yasa da yawa daga cikin masu salla a cikin babban masallacin anguwar tasu mlm Abdullahi sukayi zamansu a masallaci suna cigaba da lazumi har saida gari ya yi sha sannan suka fara komawa gidajen su. Mlm Abdullahi na tafe shida 'ya'yansa maza samari 2, babban shine mukhtar dan kimanin shekara 30 sai qaramin ismail nada shekara 28, har suka isa gida suma suka wuce ciki, saida baba Abdullah ya gama musabaha da maqocinsa baba yawale da mlm zayyanu mai almajirai sannan shima yabi bayan samarin y'ay'an nasa nasa yashiga cikin gidan. ya taras da matarsa wanda yaran y'ay'an ke kiranta inno, a gaban murhu take duqe tana kwashe d'umamen tuwon nasu a wata roba mai murfi,, har qasa ta zuqunna ta gaishesa ya amsa a fara'ance, shikam ba qaramin alfahari yake da hafsato ba a matsayin mata ta gari garesa ba tun zamanin aurensu kuwa, shidai kam Alhamdulilla ala kulli halin yana matuqar farinciki da ahalin nasa sosai,, "sannu da aiki hafsatou" cewar mlm Abdullah daya duqa ya d'auki robar tuwon da nufin kai musu cikin d'aki dan wajen kwata2 batta zaunuwa saboda sanyi,, da sauri inno hapsatou ta ce ''a'a mlm kabari basai na qarashe samun ladan ba in nakai mana abincin d'aka ba?" tayi maganar a kunyace alamun fulanan takar tana kurkusa kenan,, murmushi mlm Abdullahi yayi yace "inason in ragewa uwargida na aiki ai nima ko? to dan haka nike roqon ta data haqura ta barni nakai mana abincin nn d'aki sai nasamu ladar temaka wa nima ko ba haka ba?" cikin murmushi inno hafsatou ta janye hannunta daga kan robar tuwon tace "haka,, to shiknn mlm aini banqi ace dud aikin da nike cikin gidan nan ba'a raba mana ladar ni da kai da yaranmu ba, kaga sai kowa ya q'ara samu akan nasa ladan ba" murmushi matashin dattijon yayi d'an kimanin shekaru 66 ita kuma inna hapsatou nada shekarun ta 55 sannan mlm Abdallah ya sake cewan "hmn hakane madalla da mata ta gari irinki hafsatou, muje to" a tare suka shiga d'akin nasu suka zauna. dudda sanyin da ake surarawa amman kuma d'akin nasu akwai gumi sakamakon rushin garwashin da inno hafsatou ta girke musu a d'akin tuni dakin ya d'auki daddaden gumi kuwa. saida mukhtar ya sake gaida iyayen nasa sannan isma'il shima ya gaishesu cike da biyayya iriyar tasu wacce iyayen nasu suka d'urar dasu tun farko. a tare suke cin abunci da iyayen nasu kullum karin safe, yanzun ma tare sukeci bayan sun gama ne mukhatar yaje dakinsu ya shirya cikin kayan aikinsu ganin baiga qanen nasa isma'il ba ya shigo shiryawan shima dan wucewa school dayake sun saba tare suke fita saisu rabu bakin titi shi mukhtar saiya wuce wajen sana'ar sa shikuma Ismail saiya hau school bus ya tafi shima, ganin shiru shiru ismail din bai shigo dakin nasu ba hakan ne yasa mukhtar fitowa dan ya kirasa ya shirya su wucen, saidai abin mamaki yana fitowa nan tsakar gida ya hango qanen nasa ismail zaune kan wani bokitin qarfe ko sanyin nan baya ji yayi tagumi kansa saqe cikin jikinsa. cikin mamaki mukhtar ya isa wajen nasa sai lokacin ne ma ya lura da yanda tsigar jikin isma'il d'in ke tashi ta wajen damatsan dukkan hannayen sa wanda mukhtar yasan ba komi bane ya jaza masa hakan face sanyin dake ratsa sa a wajen, matsawa kusa dashi mukhtar din yayi sannan ya dafa sa yace ''q'anina yaban ganka ba kazo ka shirya zuwa school kada kayi late naji jia kuma kace around 8:30 kunada exam ko?, kuma gashi kazo ka zauna waje ga sanyi anayi bakka gudun mura ne ta kama ka? sai lokacin ismail ya iya d'agowa da fuskarsa wacce hawaye ke bi dan tsabar damuwa, cikin mamaki mukhtar yake kallonsa sosai, zuq'unnawa yayi bayan ya kamo hannuwan ismail din fuskarsa cike da damuwa, dan kuwa cikinsu babu wanda keson yaga damuwar dan uwansa mafarin knn a matuqar d'imuwance yake qara ruqo hannuwansa yace ''dan uwa na qanena mike damunka? kasan bazan juri ganin damuwarka da kuma zubar hawayenka ba a rayuwa ba dai ko? sanin kanka ne sai inda q'arfi na ya q'are akan hakan dan naga na faranta ma qanena dan uwa na guda day'a tal hm? , dan haka maza ka gayamun mike damuwar ka? q'irqro wani kalataccen murmushi ismail yayi bayan ya dauke fuskarsa daga jikinsa yayi saurin goge hawayen nasa dan baiyi tsammanin zuwan dan uwan nasa ba wajen ba lokacin, yace "laaa yaya mukhtar yaushe kazo nan ban sani ba?, ni babu abinda mafa ke damuna fa kada ma ka damu kanka d'an uwa na" yaqarashe yin maganar tasa tareda qara son 6oye damuwar tasa can qasan ransa. kallonsa mukhtar din yake cigaba da yi sai kuma ya girgiza kai yace "no q'anena kada kaimun qarya nasan bakayi mun ita, dan nasan halinka na kuma san in kana damuwa kokuma kana murna dan haka ka fad'a mun, Saddar da kansa qasa yayi yana tunanin ta yaya zai fad'awa yayan nasa wannan iyayen kudin handout din da zai siyo kimanin 5000k (dubu biyar)? alhalin yasan ba wata riqaqqen sana'a yake ba, bayaga ta kanikanci kuma ba koda yaushe suke samu ba inda wajen nasu ba wani fice yai ba, kuma dudda shima yaya mukhtar d'in wannan year din yagama karatunsa a A. B. U. Zaria shima da qyar da zufar goshi da kuma temakon baffansu ta hnyar saida saida day'a daga cikin guda 2n gonakinsa da yayi har yasamu yayi degree d'inshi gashi kuma ya gaman aiki yayi wuyar samu dole yaje ya roqa ya samu aikin kanikancin a can bayan tasha,, kuma duka duka aikin nasa ko wata day'a baiyi da fara sa ba, gudan gonar da ta ragewa babansu itace dud in lokacin noma yayi suke zuwa da baffan nasu suke girbewa amfanin gonar kuma in aka samu baffan yakan rabawa dangi da abokan arziqi kingin kuma a kawo gida aci, kuma tunda yayan nasa mukhtar ya fara aikin shike siyo musu kayan cefanen da za'a saffara abuncin gidan aci kullum, sannan ga kuma kud'in ruwa da kuma sauran buqatu na rayuwa,, topa tayaya zai fad'a masa damuwarsa ya tayar masa da hankali inda yasan ba halin hakan garesa ba?, jin mukhtar ya sake dafasa a karo na biyu muryarsa hatta fara canzawa sbd bacin rai yace "wlh q'anena in baka fad'a mun damuwar kaba zanyi fushi dakai har na tsawon minti day'a fa danma kaji" yana fad'in hakan kuwa ismail baisan sanda dariya ta subuce masa ba dudda halin damuwar da yake ciki kuwa, dan yasan wannan wani salon sune na wasa tun suna q'ananan yara in day'a na cikin damuwa zai furta wa d'ayan hakan to zakiga nan take sunyi dariya dan sunsan koda dai dai da second d'aya ne bazasu iya fushi da junan suba bare har minti day'a kuma hakan sabon sune tun zamanin childhood nasu knn. murmushin jin dad'i mukhtar yayi ganin q'anin nasa ismail ya saki ransa har yy dariya sannan yasake cewa "to gayamun qanena miye damuwar ka dai yanzun? cikin kararriyar murya ismail yace"wlh yaya kudin handout ne sukaimin tsaye na rasa yanda zanyi nida da sanaar da zanyi da naje nayi wlh na siyo su, to amman yaya lokaci ya rigaya daya qure min tunda saura kwana biyu knn lectures din zai yi mana exam dasu kai tsaye, kuma gashi yace dud wanda bai siyoba bazai zauna masa class exam ba kuma babban tashin hankalin yaya shine lecture din dake daukarmu topic din inglesh da math kuma yaya Allah kuwa baida mutunci nasan zayana iya bawa dud wanda bai siyo books dunnan ba carry over a exam dinsa to shine narasa ynda zanyi damuwa taimun yawa kuma gashi muna jarabawar qarshe ne ta fita makaranta" mukhtar zaiyi mgn knn sukaji muryar baffan nasu a bayansu na cewa "ah mukhtar Ismail mikuke har yanzun baku tafi ba, ni da naji shiru ma nazata kun tafi ay,, ismail zaiyi mgn mukhtar yayi saurin cewa "eh baffa yanzun zamu fita yayi maganar yana mai yiwa Ismail din alama da ido alamum kada yace komi kawai yaje ya shirya,sam mukhtar baisan iysyen nasu susan da mgnr kudin dan basu ke garesu ba saima suma su saka damuwar hakan a ransu, shi har mmki yake yanda ake cewa free education amman saika je school din kaga ba haka ba dan tafi karfin talaka maras galihu. hakan kuwa akayi saida yaje ya shiryo suka wuce baffan nasu ya bisu da addu'an adawo lpia sannan ya d'auki buta ya fara alwala danyin sallar walha. suna tafiya har suka kai titi mukhtar ya fiddo wayarsa yace ''qanina bani sunayen handout din man" zuba masa idanuwa ismail din yayi sannan yace "yaya nasan bakada kudi ka barsa ni kawai zan haqura da zana jarabawar" yayi maganar kamar zaiyi kuka, girgiza kansa mukhtar yayi yace "kada ka damu qanina inabin salis abokin aikina wasu 'yan kud'i nasan zasu isa na siya maka books din. Insha Allah " da sauri ismail ya rungume yayan nasa baisan sanda hawayen farinciki suke zuraro masa ba fad'i kawai yakeyi " ngd d'an uwa na gari yayana Allah shi qara bud'i nasan in AllAh yai maka arziqi zamuji dad'i yayana kamar yanda kake cewa, murmushi sukai dukkansu kansu rabu saida ismail yakai bakinsa kan kunnen yayan nasa yace "d'an uwa ns Allah yabaka fiddausi,, cikin murmushi mukhtar ya dan kai masa dukan wasa yana fad'in kaiko kan dubamin waya na ko? da gudu gudu ismail ya shige school bus din nasu data tsaya a wajen datake daukar students din yana dariya tareda d'agawa yayan nasa hannu shima mukhtar d'aga masa hannun yake cikin fara'a sannan ya wuce wajen aikinsu yana tafe yana tunanin qaryar dayai ma qanen nasa ns cewar Yana bin salis abokinsa kud'i,, shi kansa yasan babu yanda zaayi ta bari burin qanen nasa nason ganin ya zama malamin makaranta ya kasa cika muddin yana a raye kuwa. dam yasan burin qanen sane ya zama teacher tun yana qaraminsa yake riqe da wannan burin shikuma yai masa alqawalin tallafa masa harya kai ga gaci muddin ana rayuwa,, to yanzun baccin
Chapter 4 · 0% Book details