Sashe 167
Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
bugawa a mujalla daya wuce hjy furdausey haka yakeji a ransa, dankuwa ko sunanta yatsani yaji bare ya tuna da sunyi wata rayuwa ma a baya. koda khaleepa suka shigar da hjy furdausey emergency nan suka kwantar da'ita saman gado, wanda kusa da gadon nata harda wani crista shima yana kwance galabaice ba lpia.. tashin farko khaleepa daya fara buncike yaga dole sai an yankewa hjy furdausey qafafunta 2 da kuma hannuwanta dukknsu Snn zata samu nutsuwa sbd sugar din ta. Dan haka yana kuka ya sanar WA su dady sales, to babu yanda suka iya haka suka yita tausar khaleepa d'in dayayi hakan kodan nema mata sauqi kuwa dan ihun kukanta kadai da takeyi gamida yagar naman jikinta d'anye tanaci ya'isa ya qara tada musu hankali, dole tasa khaleepa yayi mata allurar barci tareda Sanyo kayan aiki ya dawo yafara aikin cire mata qafafunta yana kuka riris, saida yagama tsab wajen qarfe uku na dare sannan yasa bandage ya nad'e wuraran tsab sannan yayi saurin komawa wajen su dady sales ya zube jikinsu yana kuka sosai gwanin tausayi,, sosai suka dinga rarrashinsa wanda daga qarshe suna nan wajen akayi kiran sallar asuba, daqyar sukayo salla a cikin masallacin sai wajen bakwai na safiyar ranar ne Snn suka baro masallacin, suka shigo room d'in da hjy furdausey take kwance wanda suna shigowa tana farkowa,, ganin datai jikinta ya koma dungu kawai ta fashe da kukan nadama na abinda ta aikata a rayuwarta kan kace MI tuni idanunta sun kakkafe tana kyarma,, da gudu khaleepa yaje ya rirriqe ta yana kuka yake kiran "innalillahee.... momy ki tashi,,,, kitashi,,,,, kiyi haquri ki tashi indai kika tashi nai miki alqawalin zanje gaban dady na durqusa nayita roqonsa harsai ya yafe miki kinji,,,, haka khaleepa yaita sabbatu hatta su baba yawale da dady sales da 'yan uwan wannan kiristan dake jinyar sa basu San sanda hawayen tausayin khaleepa yadunga fito musu daga cikin qwayar udanuwan su ba,, daqyar dady sales ya tayar dashi daga wajen, wanda sosai baba yawale ya lura da hjy furdausey magagin mutuwa kawai takeyi, dasauri baba yawale d'in ya qara so daidai setin kunne ta yana laqafa mata kalmatusshahada, amman inaaaa tayi tayi tama bud'e bakin amman takasa kwata kwata, uwa an datse mata bakin kuwa haka takeji,, haka baba yawale yaita maimaita mata kalmatusshahada d'in nan amman tagaza kar6awa dudda ya fahimci tana son maimaitawan amman Allah bai bata ikon hakan ba,,, abin mamaki da al'ajabi ji sukai wannan kiristan dake kusada gadon hjy furdausey d'in shi kuma yana nanata kalmatusshahada d'in dayaji baba yawale nason hjy furdausey ta fad'a amman takasa,,, cikin mamaki baba yawale ya tambayi 'yan uwan kiristan mutumin nan wato mace guda daya namiji daya, baba yawale yace musu ko daman dan uwansu musulmi ne? nan take sukace masa a'a kawai dai sun sani yana yin wasu 'yan al'adu masu kama dana musulmai,wato na kullum safiya ta Allah yana bada sadaqar kud'i biyar goma ga qananun yara, snn in sallar su tazo wato kirsimate yana sawa a dafa abinci wanda babu nama a cikinsa ko tsoka daya, yasa adinga kaiwa gidajen musulman maqotansa, damuka tambayesa miyasa baisawa asaka nama a ciki dudda dai ga naman da yawa, sai yakance yayi haka ne gudun zargi, wato kada musulman ganin naman a cikin abinci yasa musu shakkun cin abincin gudun kada suyi tunanin ko naman alade kona kare ne ko kuma ma mushe ne a ciki,, koda suka gama gayawa baba yawale hakan sosai yayi mamaki, a ransa yake cewa "lallaikam gaskiyar hadisin dayazo Akan fad'ar cewa, zakaga mutum na aiki kalar na 'yan wuta baifi saura qiris ya rasu ba in Allah ya soshi da rahamarsa zaisa shi yayi aiki kad'an wanda zaisa ya shiga aljanna babu hijab wato ba shamaki, hakama mutum na aiki kalar na' 'yan aljanna zakaga saura qiris ya rasu zai aikata aiki kalar na 'yan wuta kuma y@ shiga wutar, wannan dud suna faruwan ne a cikin littafinka na kunfayakun, ya ubangiji Allah. Jin da sukai mutumin yana gama maimaita kalmatusshahada d'in yayi shiru idanunsa a sama yasa yan uwan fahimtar ya mutu tuni suka fara kuka suna kiran jesus jesus jesus,, sunjima suna kuka dudda sun kira saurin 'yan uwansu kuwa da cewa azo da mota a dauki gawan dan bakin binneta,, koda sukazo zasu dauki gawar baba yawale yayi qoqarin fahimtar dasu cewa yanzun fa d'an uwansu ba kiristan bane Inda harma Allah yabashi dama ya ambaci kalmatusshahada to susamo malamin adini yai masa salla, amman qiri qiri sukace baza suyiba Inda sunsan d'an uwansu kiristan ne, ahaka suka fita baba yawale yabisu da kallo snn ya dubi dady sales yace "Allah yasosa da rahman sa dan haka komi zasuyi masa bazai sauyasa daga musulincin daya karba ba ynxun snn ya mutun. dai dai lokacin ne sukaji wani nishi mai qarfin gaske hjy furdausey taja sannan ta nimmuqe dungurmin jikinta daga haka tace ga garinku nan...... ta cika knn. Allah sarki ay da gudu khaleepa yaje ya qanqame gawar tata yana kuka ma'ishi dan kwata yakasa mgn jijjigata kawai yake jikinsa na fidda gumi uwa yayi wanka,,, daqyar baba yawale ya janyesa shikuma dady sales yaja malullu6i ya rufe ta har kanta yana kallon ta da tunani a ransa yake cewa "ay shikenan to, iyakar taki ta duniyar knn furdausey, yanzun ina yawon neman asirin naki yake? babu? Allah shi kyauta ya shiryi masu hali kalar naku kodan gobenku tayi kyau. girgiza kai yayi shida baba yawale yayinda khaleepa ke dafe da bango har lokacin hawaye basubar fuskarsa ba, kallon gawar baba yawale yake a ransa yace ''hatimatussu'e mummunan makoma ta cikawa bada imani ba, wa' iyazu billah,, Allah ya tsaremu da 'ita,,. daqyar baba yawale yasa khaleepa yayi shuru har suka tallafo gawar tata shida dady sales suka sakata a mota suka tuqo ta har suka iso ciki anguwar tasu kuwa da misalin qarfe 10 na safiyar ranar ....