← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 178

Sashe 22

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👁🥡👁
🅿1⃣4⃣
saida mukhtar yaci abincin nan kuwa sosai, jin cikinsa na barazanar fashewa dan cikarsa shiyasa ya d'agawa abincin nan qafa fa.
koda ya gama cin abincin kai tsaye gidansu yaje ya kirawo Ismail dasu baffa harda baba yawale sukazo sukaga gidan sukaita sa alheri sannan suka juya, ismail ne kawai yai saura bai tafi ba inda suke tsaye cikin garden din gidan(lambu) suna q'ara yawatawa shida mukhtar din.
ismail yace "wlh yaya gidan nan yayi mun masifar kyau baka jiba, hmmmm Allah kuwa yaya kamar gidan turawa fa, gskia maq'eran gidannan sun baje iya fasahar su kam" mukhtar yayi murmushi sannan yace"wlh qanena in kana son gidan nan zan iya barar maka shi sai nasa ni a gina mun daga baya, danni komi nawa naku ne a rayuwa" da sauri ismail ya zaro idanunsa tareda kama baki cikin mamaki yace"wlh yaya bazan kar6a ba kamaji na rantse"
tuni ismail yayi hanyar gate din gidan da niyar ficewa dan har ga Allah ransa baison haka da mukhtar ke masa, ace ko yaya ya nuna abu yana burgesa indai mallakin yayan nasa ne saiya nemi barar masa shi? wannan ai abun yayi yawa danshi har kunya ma yakeji dudda kuwa yana yayansa, shiyasa kullum son junansu da shaquwa take qara ratsa dukkan zuciyoyinsu gaba daya so zalla bamai algush ba kuwa a ciki.
da sauri mukhtar ya bisa ya riqo hannunsa cikin damuwa yace "miyasa zaka tafi ka barni qanena?!, mukhtar yana gama fadin hakan kuwa take yaji gabansa yayi wani kalar mummunan faduwa kansa kamar yana jujjuya masa da sauri ya dafe kan tareda zuqunnawa wajen yana fadin
"ya salamullahe!,,, innalillahe'wainna'ilaihurraji'un,,, a zabure Ismail ya zube gabansa ya ruqo hannunsa daka saman kan nasa a rude yake cewa "subhanalla subhanalla
"yaya na?
yaya na miya faru dakai ne haka fad'a mun dan Allah, yana maganar muryasa na kyarma, mukhtar kuwa da kansa ya daina juya masa zuwa yanzun,yana dawowa hayyacinsa yaga Ismail zaune a gabansa riqe da hannuwansa da sauri kuwa ya fizge hannunsa daga na ismail din ya miqe tsaye danji dayai bai ma son ganin Ismail a lokacin yafi buqatar yaje ya kwanta ya huta dan har yanzun yanajin ciwo a tsakar kansa, jikinsa ma gaba daya yaji ya saki ya sauya masa kamar ba nasa bama.
ismail shima miqewa yayi yace "yaya fad'a mun mike faruwa dakai dan Allah?"
yayi maganar yana qoqarin sake ruqo hannun mukhtar din, jikin mukhtar na rawa ya goce hannunsa ya dubi ismail fuskarsa a sauye yace"kaje gida qanena kaina namun ciwo zanje nasha magani na d'an kwanta"
"to yaya sannun Ubangiji Allah ya baka lpia,,,, tunkan ma ya ida maganar mukhtar ya wuce baice masa komi ba yana shiga kuwa ya maido qofar tasu ya rufe da qarfi, haka Ismail yabi yayan nasa da kallon tausayi shi kansa yasan gajiya ne kawai ke d'awainiya da yayan nasa, haka dai badan yaso ba yatafi.
wasa wasa kwana uku ras a jere saida firdauseey ta ida ciyar da mukhtar abincin sihirin nan sannan taje ta jefasa a kwaminsu na toilet tareda floshin dinsa yayi qasa.
yanzun haka mukhtar ne zaune shida firdauseey bayan dawowarsa daga office sai faman manne masa take tana masa fira.
zuwa can tace "alhaji na yadace fa ace mamana itama an gina mata gidan zamani haka wanda zata dawo ciki ta zauna ko?'"
cikin fara'a batareda shayin komi ba yace "kin kawo shawara Matata,, to amman awane anguwa ne kike ganin yadace ace za'ai mata ginin ne ta zauna?"
saida tad'an muskuta tareda qara kwanciya sosai a jikinsa tana wani shafa fuskarsa yayinda shi kuma ke shafa cikinta wanda haihuwa yau ko gobe.
jiyayi tace"hmn ay alhajina inma ka tada su baffanka daga gidansu ka gyara mata can ai abun zaifi kusa nikega da ace kuma tai mana nisa in zata zo kuma zata sha wuya, kaga qwamma ace sudinne sukai maka nisan wato su baffa. babu musu mukhtar yace "lallai kumafa wannan gskia ne, yanzun abunda za'ayi zanje nasan yanda zanyi kan maganar gidan su baffan da tashin nasu kuma" farinciki aran firdauseey kamar zai kasheta kuwa, a zuciyarta kuwa tuni tabawa boka marakusa number daya daga cikin hatsabiban bokayen dudduniya dan gaba daya taga hankalin mukhtar yabarsa inba haka ba harya zai yarda yana'a cikin hayyacin sa ya tashi iyayensa daga gidansu, gidan daba mallakinsa ba shi 1?
ta6 lallaikam dole ta sara masa kuwa, cikin murmushi tace "nagode alhajina sosai" 6ata fuska yayi yace "haba matata miye kuma na godia dukiya ta fa dani kanki mallakin kine"
danta tsokanesa tace "amman kuma banji kace komi ba tun dawowarka gameda ginin da zakasa aiwa qanen namu ismail fa?"
gani tayi take yanke fara'ar dake fuskarsa ta gushe gaba dayanta sakamakon ambatar Sunan isma'il da tai"
fuska a daure yace "nafasa bazan yi masa ba, shima ay yana aikinsa na gobnati inyanada buqata ya tara kud'insa shima yaje ya gyara gidan nasa dan nama fad'a masa hakan shima.
kaini su baffa mafa kansu nayi dana sanin biya musu mecca da nayi sai naji da kudin na karba na kejerar tasu dana ida shurye shuryen bude gidan mai na da na fara ginawa" firdauseey tace "gskia kam dai asara anyita nima banji dadin faruwan hakan ba alhajina sai dai kuma a kiyaye na gaba dan kuwa dai wannan yarigaya daya faru"
q'utawa mukhtar yayi yace "hmn ai anyi na farko anyi na qarshe dan q'wadala ta bazan qara 6atarwa kan su ba, barima naje na dawo nasan abunda zan musu na rage asara."
(kai jama'a! kuji fa?)
yana gama fad'an hakan kuwa ya miqe ya fice daga falon.
wani iriyan dariya firdauseey tayi har saida dan cikinta ya wuntsula kuwa,
a fili tace "hmnnnn wnda rai ke a jikinsa nada sauran kallo, billaheel azeem su baffa wannan somin ta6i ne kuka soma gani ma daga garemu".
tana gama fad'an hakan ta jawo wayarta takira uwar tata ta sheda mata ai mukhtar yazama nasu harta bata labarin ginin da za'a fara mata itama, karkaso kaji yanda meron tsimbe ta kwarara wani uban ihun farinciki.
Mukhtar kuwa yana fita gidansu ya shiga kai tsaye ya fad'a ko sallama babu, anan ya iske baffa da inno suna zaune tsakar gida suna fira kwalin dabinon ajwad ne a gabansu suke ci.
tsaya musu yayi aka "sannunku su baffa" abunda yace knn ya kama qarfen barandar gidan nasu ya riqe, baffa ya dubesa sosai yace "ah mukhtar ya bazaka zauna ba kai tsaye haka akanmu?, fuskarsa kijin kijin ya dubi baffan yace "eh baffa hakanma yayi dama zuwa nai nace muku zansa a fidda kayanku zuwa gidan isma'il za'a dan d'ora muku wani sabon gyaran ginin ne na sama in yaso aka gama sai ku dawo.
Inno tace "aa mukhtar barmu haka dan iya haka ma ya ishemu wannan gida dai zaman duniya bana q'iyama ba ai yayi"
baffa ya amshe da cewa "gskia ne, dan haka mukhtar kaje mun gode AllAh shiyi albarka mungode hakanma" dai dai mukhtar zaiyi magana saiga isma'il ya shigo gidan yana ganin yayan nasa sai jikinsa ya qara sanyi dan tunawa da abinda ya faru jia, abunda ya faru kuwa jia ne lokacin mukhtar ya dawo office da marecen ranar yana qoqarin tura hancin motarsa gate din gidan nasa dan har ma maigadi ya bude masa wawakeken gate din, to shikuma ismail shima dai dai lokacin d'an aca6a ya saukesa daga mashin dawowarsa kenan ma daga makaranta dayake gyaran makarantar ake musu shiyasa aka maidata ta marece kafin a gama su koma ta safen.
da sauri ya bawa d'an mashin din kudinsa ya qarasa gefen motar mukhtar din yace "waitt yaya, yana maganar ne yana gyara jikkar sa da litittifansa na koyarwa ke a ciki.
dakatawa mukhtar din yayi Amman sam ko kallon isma'il d'in ma baiba still hanunsa na bisa styarin na motar dukkansu.
Isma'il yace "yaya harka dawo sannunka da dawowa, ya kuma qarfin jikin, kan mukhtar yace wani abu saiga alhaji tanimu yazo wucewa cikin motarsa shima, alhaji tanimu shine mai filin nan na kusa da gidan isma'il wanda mukhtar ya nema a kwanaki akace yaje mecca, dan haka parking yayi kusada motar alhaji mukhtar din daga cikin motar yace "alhaji mukhtar barka da ganinka, sai nan fa alhaji mukhtar yasaki fuskarsa yace "yawwa dai alhaji tanimu ya iyali da harkoki"
"Alhambdulilla haj mukhtar, dama naji ance kana nema nane, haj mukhtar yace "eh a kwanaki ba, akwanaki ne na nemeka dan inason siyen filinka ne, haj muntari yace ok wanne filin kenan nawa daga ciki? haj mukhtar yace nanan anguwar amman yanzun ma na fasa ay"
yana fadin haka kuwa Ismail din ya dubesa da sauri saidai baice komi ba ya maida kansa qasa sakamakon hada idanuwa da sukayi yayan nasa ya hangi wasu abubuwan marassa fasaltuwa a qwayar idanun nasa,
haj tanimu yace "shikenan to babu damuwa" nan sukayi musabaha sunadaga cikin motocin nasu sannan haj tanimu din ya wuce.
a sanyaye isma'il d'in yace "yaya naji kace ka fasa siyen filin kuma? baccin nina fad'a wa haj tanimu din kana nemnsa kuma gashi kagansa kuma kace a'a?
cikin isa da taqama gamida gadara mukhtar yadubi Ismail yace "eh na fasa, dukiyar kace koko dukiya ta??! dan haka kai tsaye nace bazanyi ba, kaima ai kana aikin kuma kana samun kud'i to kayi da knka, kai bari ma kaji kasan da sanin cewa daga rana mai kamar tayau dinnan kada ka qara tunanin zaka mori qwandala daga cikin arziq'ina, dan bazai yiyuba kudasu baffa da sauran jamaar anguwa kun maidani Baitul mali gidan tatsar kudi ba, dan haka kaji ma ka q'ara ji" yana gama fad'a masa haka ya bad'e isma'il da qurar wajen ya shige gidansa mai gadi kuma ya tura gate d'in gidan ya rufe...
da kallo kawai isma'il ya bisa yana tunanin kuwa anya wannan yayansa ne koko dai wani mai kama dashi ne?!...

by
*Xexen Fasaha*.
[1/17, 3:10 PM] Xainab Documen: 👁👁
🥡🥡
👁👁
*DA SAURAN KALLO !!!*

Story and writing
by
Xayyneb 💤💤

Fasaha online writers f. o.w.

*🌳imparting valuable knowledge and entartaiment is our concern*🌳.

~dedicated to my mom Sadeeq hawwas~

-https://www.facebook.com/Fasaha-Online-Writes-751775151851852/?referrer=whatsapp.
Chapter 22 · 0% Book details