Sashe 146
Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
knn ko? wacce bata mantuwa da yafiwa bare kuma daukan fansa? Hmnn muje zuwa tayaro kyau take bata qarko ay yayinda yaro baisan wuta ba inba takata yaiba yajita a jikinsa ba. wata mugunyar dariya tasaki ita d'ai a wajen uwa wata mahaukaciya sabuwan kamu, aranta tace "hmm auran nagani kuma banga zaman saba ay, tsinannu mayu kawai" haka taita tuqawa tana qarawa harsanda taji motsin saukowar dady mukhtar daga saman benen zuwa falo. yana qarasowa kuwa kuwa yana zama saiga khaleepa yashigo falon d sallama hannunsa riqeda jikkar laptop dinsa idanunsa sayeda medical farin glass dinsa gwanin fin kyau yama qarayi yau. sosai yake a gajiye dan aikin dayai yau asubiti ya wahalshe sa sosai ga tentions dinda heenduh ta aza masa na rasa gane kashe masa waya datai yau, burinsa kawai yai wanka yaje gidan danshi gudunsa ma kada kobata lpia bata dai fada masa bane ko batason takura danyasan halin 'yar kayansa shiyasa takashe Wayar tatan may be ma. saida yaje jikin momyn da dadyn nasa sukai kalar gaisuwarsu sanan yamiqe yana yamutsa fuska yace"wlh dady Momy nagaji sosai yau a hospital, wanka kawai nike sonyi konaji Strong nawa yadawo ..cikin murmushu dady mukhtar yace "sannu my son jeka kayo wankan daman akwai mgnr dazumiyi dakai" "to dady" Momyn tace "yawwa maitsada na afito lpia to" dasauri yahaura Sama kuwa zuwa side nasa. duban ta dady mukhtar yaice "kinsan dud bidurin mgnr auran nan da ake baida labari amman yanzun zaijisa nasan zaiji dad'i''. Cikin murmushi tace"qwamma yasani kam kozai fara shirye shuryen daya kamata shima a matsayinsa na ango kam" tayi mgnr cikin girgiza qafa. minti 20 tsakani saigashi ya sauko falon cikin shigarsa ta jar t-shet da farin jeans sosai sukai masa kyau kayan musamman dasuka kama jikinsa saiyai gwanin kyau da burgewa sosai,ga damtsensa cike hakama gashin hannunsa har zuwa wajen yatsunsa kwankwance suke baqaqe yas yas, sajen fuskarsa da girarsa gamida cikakkun gassan idanunsa madaidaita shiya qara bayyana sirrin kyan fuskar tasa dan kallo d'aya zakai masa kai zaton baqon balarabe ne ingarma fari Sol a gabanka. tundaga nesa iyayen suke kallonsa dayaba tsarin kyan halitta ta d'an nasu. harkusa da dady mukhtar ya zauna ya kallesa yace "iam ready dady na wace mgn zamuyi?" Yayi mgnr tareda kallon momynsa Uwa gareta zaisamu amsar. saida dady mukhtar yai gyaran murya tareda gyara zamansa sannan yace"mgnr dai nasan daman dai kasan da zamanta tuni tunknma Nina sanda ita" duban dadyn yai yace"mgnr CE ta 6acemun amman tunamun dad dan gskia I forget it" dady mukhtar yace"OK ba wata mgn bace illa ta auran Ku da zarah wacce kuka gama tsarawa kaida momynka yun asa'ilin da bannan, sannan kaida bakinka inbaka mantaba mukai waya Kn mgnr kuma ka jaddadamun amincewarka ga zarah, inban mntaba lokacin harna roqi ku dagan qafa kaida momynka kamin na dawo dannaga kamar momyn taka taso ayi bikin tun lokacin, saida na alqawanta mata dazarar na dawo za'akai mgnr gaban manya to shine yanzun cikin ikon Allah da yardarsa da kuma cika alqawalin danaiwa momynka yau munje nema maka auran zarah nida babanka Ismail da d'ayan baban naka salis kuma Alhamdulilla mahaifanta sun amshemu hannu bibbiyu dan haka nan take muka tsaida ranar daurin auren naku nanda sati biyu masu isuwa wato jumaa' ta sama kamar yanda aka tsara ranar za'akai itama heendun tokaga saisu tare ranar gaba daya, shiyasa nasanar maka da zancen kokaima Kanada wani shiri karan kanka da abokanka na hidiman bikin dazakuyi, tokaji dalilin Kiran naka danai nace zamuyi mgn" tunda khaleepa yagama jin saukar wannan hargitsattsan mgnr gaba daya tunaninsa yabar kansa yayinda jikinsa gumi yadinga tsattsafowa kota'ina banda heenduh babu wacce ke karakaina a tunaninsa, dawane duba zai kalli heenduh ne? bacin yagama fallasa mata qin zarah da rashin damuwa dayakeyi kanta bare yaji koda burbushin sonta ne a ransa? Knn zatai masa kallon maqaryaci mayaudari mai fuska biyu knn? alhalin har aransa ba haka bane?? abinda mashi yafi d'aga masa hankali yasan heenduh da tsananin kishi musamman yanda basu shiri da zaran shiya san hakan, zai iya rantsewa kan wannan mgnr tsab heenduh zata iya masa bore tareda juya masa baya dudda sonda sukewa junansu kuwa, inda gashi cikin mgnr dady ga alama su heenduh sunsan da mgnr auran sboda gashi harda babanta a zuwan nema masa auren zarah ma, to tayaya zata fahimta babu wata mace a dukkan rayiwarsa harga Allah bayan ita? Ita ya fara so ita kuma zaici gaba da so har qarshen rayuwarsa. dafe kansa yai sakamon bugasa dayaji ana masa Uwa ana doka masa guduma akan kuwa tsaban yanda kwanyarsa taketa hango masa yanda zasu kwashe da heenduh dan jikinsa na basa za'a samu babban matsala kuwa ta sanadiyyan auran zarah kuwa da aka qaqaba masa ta qarfi dayaji, Sam bazai iya musawa iyayensa ba bare gardama danbai sababa dan haka samuyai ya miqe yana qoqarin barin falon knn yaji dady mukhtar yace "yaka tashi bakace komiba kuma?" Hjy furdausey tace"a to Nima dai da abunda zance knn ay" baijin zai iya juyowa dan ba shakka da zarar sun kallesa zasu harbo tsananin tashin hankalin daya mamaye zuciyarsa dan haka daqyar ya hada kalman "to dady Allah kaimu lkcn lpia" yana gama fadin hakan kuwa ya fice dawani mugun sauri daga falon. kaitsaye gidansu yunus yanufa yawuce dakinsa aiko ya iske yunus din yana waya ga alama shidama yarinyar sane..wani wawan ball khaleepa yayida wani qaton jug na glass cikeda ruwa Wanda ke ajiye tsakan dakin saiga cup dinkuwa yatashi yabugi bangon dakin yadawo qasa yayi tatsa tatsa dashi wanda ruwan da suka faso sune har jikin yunus suka fallatsa amman khaleepa ko'a jikinsa saima zaman sa da yayi can gefe yahada kaida gwiwa yayi shiru sai zufa yake. babu arziqi yunus sukai sallama da budurwar tasa ganin yanda abokin nasa ya shigo gigice dasauri ya'isa garesa ya zuqunna tareda tabosa da cewa"friend doctor lpia kuwa?" d'agowa khaleepa yayi wanda hakan kuwa baqaramin qara tadawa Yunus hankali yaiba sakamakon ganin yanda idanun khaleepan sukai jaaaaazur dan tsabar tention daya bawa kansa. "haba dan Allah nace kafadan mike faruwa newai kabi ka tashi hankalinka haka?" cikin mgn wacce murya tagama sanyi babu qarfi a cikinta khaleepa yakalli yunus yace"bansan taya zamu qareba yunus da ita, yunus inaji a jikina wannan mgnr bawai qarama bace gareta dan tanada kishi a kaina yunus,, yunus sonta yamun kamun bazata batareda na shiryawa hakanba, munso junanmu muna kan son junanmu yunus, sanda mike farincikin daman mallakan juna batareda wani shakku ba ko boye boye na tarayyarmu gudun fallasuwan sirrin ga iyayenmu, amman lokaci d'aya yunus wani baqon al'amari ya ratso mana wanda narasa ta yanda zan bullo mata da batun tagane babu niyyata acikin lamarin face *biyayyan iyaye*" yaqarshe mgnr tareda sakin wani zazzafan numfashi. gaba daya yunus yagaza gane inda zancen abokin nasa ya dosa kwata kwata..dan haka yasake dubnsa yace"kafahimtar dani danni bangane kan zancen ba, kuma atarayya tadakai bansan ma kafara soyayya da mace ba ayanda nasan halinka kan rashin maida hankali gasu matan ma gaba daya, dan hana rantsuwa zan iya cewa headche dinka CE kawai ma kake kulawa inkaso shima tab'a 'yar tsaman tsakaninku da'ita" shiru yunus yai yana kallon khaleepan kawai tareda sauraran amsarsa kmr ynda ya buqata yawarware masa manufar sanin inda zancen sa yasa gaba saida khaleepa yasake sakin wani numfashin sannan yafara korowa yunus tarihin aurensu shida heenduh ta hangar baba yawale dayai musu qarun haske kan batun dakuma rayuwar dasukai harta kaisu ga samun cikin dasuke raino da tattali har kawo mgnr auran Zara kuma yanzun. yana kawowa nan yasauke ajiyan zuciya yace"to yunus gashi su dady sunkarbo auran zarah kuma kasan bazan taba iya musawa ba tayaya knn zan kalli lollipop ?" sakin baki kawai yunus yai yana kallonsa cikeda mamakin auransa dawai heenduh headache? danhaka yace"amman wlh abokina kai masifan maidani garwa ko? Wato Ashe kasan heenduh takace kaki fadan in san madam dunmu CE saima kabi kadinga lalube yarinya har ka samu kyautar sadaqi(ciki),ammandanka maidani baho saiyanzun da matsala ta kawoka ka fada munko kai dan iska? Sabanin da dakaje kakejin dadunka kama manta dani wajenmun wannan bayanin ko?" tsoki khaleepa yai yace''toba gashi yanzun kaji ba? nidai kagayamun mafita kawai Kan ynda zanjewa lollipop dan wlh nasan zaiyi matuqar wuya mukwashe ta dad'i da ita" shiru yunus yai danhar a ransa shima baiso kmr khaleepa kamili zai auri ballagaza kamar zarah ba, yarinyar data gama tsiyayar da mutuncinta a titi gaba d'aya, to amman Yaya zasuyi sai haquri dan dukkan d'a nagari bazai taba jayayya da iyayensa ba dan gamawa da duniya lpia kan buqatarsu garesu muddun bata kaucewa hanya ba, wataqil ma kota sanadiyyan auran nasa ne zarah zata shiriya daga shashancin qazantacciyar rayuwar barikin cikin gida datakeyi. danhaka yunus yadafa kafadan khaleepa yace"naji kuma nafahimceka kuma kada ka damu da mgnr auran zarah kabi umarnin iyayen dan Neman rabauta dan kuwa aljannar namiji naga iyayensa sabanin ta mace dake qasan qafafun mijinta, dan haka komi Nada iyakarsa zakaga wataran kmr ba'aiba abokina"sosai khaleepa yaji dadin tunasarwan nan ta yunus madalla da aboki na Gari shiyasa akeson tarayya dasu dan baka kyakkyawan Shawara dud inka shiga cikin taskun matsala kuwa, sa6anin wasu abokan da zasu ida dulmiyaka ta hnyar baka gurbataccuyar shawara a rayuwa wanda wataqil kazo kana nadama ta hakan daga baya. katse masa tunani yunus yai dacewa"batun heenduh kuma babu matsala insha Allah, kaidai bari na shiga cikin gida na amso mana abinci inmun gama saimuje wajenta ninasan ta yanda zan bullowa headache dun tamu mai yawan bamu ciwon kai" mgnr yake yana dariya harya shige cikin gidan nasu, khaleepa saman katifa ya kishingid'a tareda sakin sanyayyen numfashi snn ya lumshe idanunsa yana murmushi kawai abinsa na mgnr yunus dayai kan heenduh ynxu dazai fitan. a kuma daidai wannan lokacin ne heenduh ta fito daga gidan baba yawale sakamakon abincinsa data miqa masa still ranta a matuqar jagule yake, tana gabda shiga gidansu ne taji yo murya daga bayanta ance''heey 'yar kyakkyawata naji dad'in ganinki kuwa, Kice yau nazo anguwar a sa'a" dasauri heenduh tajuyo tana kallon fuskar saurayin da kmr tasansa wani GU saidai ta manta. lura dayai bATA ganesa bane yasashi cewa"I'm khames hasan gwanda Wanda muka taba haduwa keda qawarki a boutique na madam