Sashe 159
Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
kuma ynxun ma na qara maimaita maka, Inda ban sonka sai kaje wajen wacce kakeso itama kuma take sonka amaryar taka, sai kaje wajen ta tabaka dukkan jin dadi" taqarashe mgnr tareda yamutsa fuska. tabe lips yayi ya dubeta cikin son ya qara quleta danya fuskanci kishin ne nata ya kuma bujirowa, nan ko ya kanne mata ido daya tareda dage gira ya tabe baki yace "kinyi gskia dan amarya kam akwai nuna qwazo abin cwai cwai dad'i muah" wani qululun takaici ne yasake taso mata a fusace kuwa ta Bude motor ta fice zuwa cikin gidan nasu gabanta na cigaba da bugawa kuwa sosai, shima Bude motor yayi ya fito tareda rufeta ya biyo bayan heenduh zuwa cikin gidan yana mata dariyar kishin nan nata a ransa. tana shiga ta samu mama zainab ita da baba isma'il zaune saman carpet nan tsakar gida tana yanka masa kankana sallamar datai ne cikin d'ari d'ari tareda bin bango hakan ne yasa daga mama zainab har baba isma'il suka dago fuskokinsu da sauri suna kallon to cikin mamaki wanda lokaci daya suka miqe cikin tsakanin farin ciki kuwa, dasauri mama zainab ta'iso gabanta tana fadin"henduh kece kuwa? inn....... ii.... ina kika shiga ne Allah yabaki ikon futowa yau...? kai alhamdillah mun gode Allah, Allah qarawa annabinsa daraja aminn, tana mgnr ne cikin zubar hawaye farin ciki dasauri suka rungume juna suna hawaye daidai nan khaleepa ya qara so wajen cikin murmushi ya isa kusada baba isma'il daketa faman godiya ga Allah hannuwansa na'a sama,shima banda fara'a baya komi,, baba isma'il ya dubi khaleepa cikin mamaki yace"ah khaleepa yana ganku tare? badai kai ka nemo mana ita ba?, khaleepa yace "eh taje gidan sa'a ne qawar ta a bauci dan ta samu sauqin zuciyarta kamar yanda nasamu labarin hakan daga ita sa'a d'in, to shine sa'a d'in taban address d'in naje na daukota,,, jin hakan da mama zainab tayi taji ranta yabaci nan take ta ture heenduh daga jikinta da sauri, nan ta matsa daga gabanta sosai tana mata kallon mamaki,,, da gudu kuwa heenduh ta qara so gaban mama zainab ta duqa qasa tareda rirriqe qafafun mama zainab d'in cikin kukan nadama na abinda ta aikata musu take cewa "dan Allah mama kuyi haquri, baba ku yafeman wlh bada sona na tafi batareda sanun ku ba,, tunkudeta mama zainab tai bayan ta watsa mata marurruka qarawa biyu saiga heenduh a qasa, da sauri khaleepa ya'iso wajen ya tayar da ita ya dubi mama zainab ransa babu dadi shima yace "dan Allah mama kuyi haquri ku yafe mata damuwar data saku wlh nina yafe mata har a raina,, cikin wani sabon bacin ran mama zainab tace" rabu dani khaleepa na fuskanci taurin kan heenduh ya shallake tunanin mu, yanzu fisabilllahe bacin tana 'yar banzar yarinya dud tausarta da mukayi kan batun auran nan tai mana lub lub uwa ta dauki maganar mu da muhimmanci amman ashe ba haka bane ita a ranta ba? harta iya daukan satan hanya ta tafi gari ya garara har bauci ba tareda sanin muba tana halin ciwo kuma amman ko kanta bata tausayawa bare mu da mukayi tunanin sace ta akayi ta tada mana hankula a banza a wofi!?amman shine yanzu da Allah yasa ita sa'a d'in ta fada Inda take har aka ganota dafa knn Bama tayi niyyar dawowa gidan ba dan yanzun dan ubanta, kuma shine dan batada kunya tazo tana mana kukan qarya Alan? " taqarashe mgnr tareda qoqarin wani marin heenduh wanda dasauri khaleepa ya shiga tsakani saiga saukar marin tasss saman fuskarsa amman bai damu ba saima mama zainab d'in data dinga basa haquri dan bashi tazo mari ba, amman shi fadi ma kawai yake "kuyi dai haquri mama ku yafe mata bazata qara ba insha Allah... shiru mama zainab tai amman badan tawai haqura da hukunta heenduhn ba. heenduh daketa a cigaba da rusgar kuka ganin datai babu sa'a ta samun sauqi a wajen mama zainab hakan yasata rarrafawa gaban baba isma'il dake tsaya yana kallon ta kawai tun dazun yana mamakin abinda tayi shima wanda ko kwata kwata bai tsaye hakan daga gare taba. dasauri mama zainab tabar wajen tareda shigewa daki, heenduh kuwa tana isa wajen baba isma'il d'in shima ta dafa qafafunsa cikin hawaye tace "babana nasan kai bazaka iya taba yin fushi da heenduhn kaba, dan girman Allah ka yafe mun kuma kasa mama ta yafemun itama wlh bazan taba samun nutsuwa ba in kuna fushi dani a rayuwa ta gwaramun kuyita mun huro mai tsanani wanda koda hakanne zaiyi sanadiyyar rayuwa ta na amunce da hak... kanta ida mgnr baba isma'il ya qwace qafarsa daga gareta yana kallon ta cikin tsananin d'acin zuciya ta bacin rai yana cewa "wlh kinban mamaki heenduh matuqa gaya kuwa, da hankalinki da tunanin ki kikai wannan abin? girgiza kai yace lallaikam kin mana d'an baka zata ba, kin batamun rai sosai heenduhn wanda baki taba 6atan rai ba kamar wannan lokacin, kiyi haquri heenduh bazan iya fara kallonki da fuskar afuwa ba kamar yanda kike buqatan hakan daga gareni... kuka heenduh ta qara fasawa tadaura hannuwanta aka ta zube qasa tana burgima da mad'od'owa tana fadin "wayyoni Allah ni heenduh rayuwa kinmin zafi iyayena sun tsananta fushi dani, ubangiji Allah na roqeka ka dauki raina na hutu...adaidai nan mama zainab ta fito daga daki hannunta boye a bayanta tana isowa kuwa wajen da heenduh take, heenduh nata billayin kuka a qasa kuwa, bata ankara ba saijin zazzafan saukar wayar wuta tadunga ji a jikinta, ai wani uban ihun ta kurma tareda miqewa tsaye a guje ta fada jikin khaleepa tana ihun tsalle tsalle tareda sakin wani kukan tareda sake qamqamesa a jiknta dake rawa kota'ina. wanda shima khaleepa tsakanin tausayin hukuncin dayaga tana kar6a daga iyayenta ne yasashi fitar hankalinsa a jikinsa sbd zugin zafin da zuciyarsa ke masa, sosai yaqara qanqameta jikinsa yana sakin ajiyar zuciya mai zafi, dasauri baba isma'il yajuya yabar gidan yayinda mama zainab tai shigewarta daki bayan ta jefar da bulalan qasa..suna qanqame da juna a haka saiga baba isma'il ya dawo shida baba dahara tareda dady mukhtar da dady salis sun biyo baya suma sun shigo gidan.......