Sashe 151
Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tana tareda momy na, zomuje narakaka inyaso sainaje gidan su grandpa damn momy ceta aikin can" sosai yaji dadin hkn kuwa dan haka har falon gidan suka shiga nan suke iske momeyn amnat din zaune yayinda heendub ke gefenta tana kwance saman doguwar kujera idanunta lumshe kamar mai barci amman tsabar damuwa ne cunkushe kawai cikin zuciyarta, dan kuwa qiri qiri taqi gayyato abokanta wani biki danko sa'a ma bata fada Mata ba balle. jitake tomimane abin gayya a wannan aure da'a ka kuntata mata a cikinsa, dan ita Batama ganin laifin kowa daya wuce doctor din dan Inda bai amine da auran zarah d'inba bazasuyi masa dole ba iyayen nasa. dan haka kuwa tanajin muryarsa falon tareda qamshinsa haka baqaramin fadar Mata da gaba yaiba sakeyin lamo tai tanajin yana gaida momyn amnat ta amsa cikin took arsa dacewa "ango na amarya sannunku da hidima fa, allah sanya alheri yabaka ikon riqesu lpia kuma" tanajin sanda yake amsawa cikin muryarsa da '' aminn aunty." wani kulukulun sabon jin haushi yataso mata tareda tokare mata zuciyarta, wato zarginta nasan zarah da yake yazama gaskiya knn Inda gashi yana amsawa da aminn da'aka musu addu'a. jitai momyn amnat nad'an ta6ata tana cewa "heenduh..?heenduh tashi ga doctor nn yaxow"tana gama fadin haka tamiqe tabar falon danufin hadowa khaleepan koda kayan motsa baki ne. shiko ganin tabar falon yasa shi qarasowa har kusada heenduh ya zauna , yazuba Mata fararen idanunsa yana kallon yanda atamfar jikinta lemon green riga da Zane suka masifar karba ta, fuskarta simple make up ne amman baqaramin kyau taiba, sosai yashagala da kallon to saiko gashi caraff ta Bude idanunta sukai four eyes, ganin shigarsa shine ya tabbatar mata da aure yashiga tsakanin sa da zarah knn ?babu zato taji ko mararta tayi wani mummunan murdawa gamida katsawa amman dudda abin datakeji saida tayi qoqarin matsawa daga garesa tamiqe tsaye tana aiko mass da wani kalar mummunan kallo, shiko kokarin ruqota yake kodan yararrasheta danya hangi kishin nata kuwa qarara a cikin idanunta ya motsa, saura kadan yariqota kuwa tayi saurin ture hannuwansa hawaye suka fara zubo Mata murya narawa cikin tsawa tsawa tace "macuci mayaudari kawai ni kafutar mun daga nan mizai kawoka wajena alhalin kadai na sona nima kuma nadaina sonka kawai ka futa kakoma wajen zarah nabar mata kai duka.... taqarashe mgnr tareda ida fashewa dawani kakkarfan kuka, har cikin ransa yakejin zafin kukan nata kuwa matuqa, danhaka murya a sanyaye yace"wai dan Allah lollipop wanne kalar kishi ne haka ne dake sai kace kank...katsesa tai ta hanyar d'aga masa hannu datai zatai mgn knn taji lokaci daya cikin ta yasake wani mugun juyawa sbd tsananin azaban zafi wata qara tasaki tareda dafe cikinta da hannuwa biyu ta zube awajen tana murqususun azaba danko kukan ma tagazayi nai, ta runtse idanunta tana sakin salati domin azatonta mako mutuwa zatayi yanda takejin wannan azaban a cikin nata, ba su Ankara ba dukkansu kuwa sai ganin jini sukai yana malalowa a qasa daga jikin qasan ta. aida gudu yaqaraso wajen yazube hankali tashe idanunsa 'sukai jawur nan take, cikin tashin hankali yake cewa "shikenan?! ,,, shikenan! hankalinki ya kwanta kin zubda zubda min cikin neylar" yy mgnr jikinsa na rawa. damqo hannuwanta yai idanunsa jujjuye da tashin hankali yake cigaba da cewa " me yasa???!!! miyasa ??miyasa akan wannan banzan kishin naki heenduh zaki zubar min da gudan janina minai miki haka kikai hateing dina haka why! why minai miki kifadamun nace!!!! yayi mgnr cikin wata matsanciyar gigitacciyar tsawa gamida girgiza kafadunta, yayinda itakuwa batasan Inda kanta yaiba tun sanda taji yafurta zubewar cikin nata kuwa tune ta shid'e a wajen tareda sumewa gaba daya, lura dayai bata numfashi ne yasa shi qara gigicewa tuni yazame babban rigar jikinsa da hularsa cikin jinin ya sunkuyo ya sungumeta a jikinsa zaifita saiga momyn amnat sunshugo falon hannunta daukeda plate na snack sai baby amnat nariq'e da jug na lemo a plate itama. dukkansu rudewa sukai ganin yanda jini ya bata musu kaya musamman heenduh ma dasuka lura bata numfashi sakamakon ko'ina na jikinta daya saki ,, momyn amnat cewa take "wayyo allah Mike faruwa khaleepan miyasame ta,, kasa mgn yai yawuce kawai dawani mugun sauri ya fito ya bud'e motarsa yasakata abaya dasauri momyn amnat ma ta'iso ta shige motor yaja dagudu suka bar gidan yayinda cikin kuka baby amnat ta nufi gidan su heenduh. Suna isa asubitin dakansa ya dauko ta a saman kafad'a ya shigar da ita emergency room na masu miscrage yafara dubata,, yadau tsawon lokaci a kanta Amman dud yanda yaso ya tsaida zubewar cikin amman ina Allah bai yarda ba saida ya zube tsab ,,, daqyar yana share hawaye yayi mata wankin ciki tareda wasu allurai yasaqala mata qarin jini ta hanyar jininsa daya deba da kansa nan take yasa mata danta zubar da jinin sosai,, zama yai gaban gadon yana kallon yanda take sauke numfashi jiyai idanunsa suncika da qwalla nn yad'ora kansa ajikin gadon nata wasu zafafan hawayen d'acin baqinciki na fita cikin idanun nasa. yajima haka harya samu yatsaida zubar hawayen nasa lokacin har ledar jinin daya samata taqare nanya zareta yasake mayar mata da qarin ruwa danta samu qarfin jiki,, saida yayi tsawuwan minti 10 yana kallon to saidaga bisani yabar dakin yana fitowa waje kuwa nn ya iske dady sales da dady mukhtar gamida baba ismail sai momyn menat da mama zainab dukkansu sunyi jugun jugun musamman masu mama zainab da baby amnat ta kai musu wnn labarin maitada hankali na cewa datai musu GA aunty heenduh can cikin jini. suna ganin fitowar khaleepan kuwa sukayo kansa da tambayar yaya jikin nata? "" jikin babansa yashige yana hawaye dan xuciyarsa sosai take sake raunana kan fitar cikin nn dud inya tuno kuwa.. a haka yashaida musu zubewar cikin heenduh dudda yaboye musu ainihin dalilin fitar cikin kuwa. har dakin suka shiga ganinta sunji babu dadi suma amman ya suka iya da abinda Allah yaqaddara saihaquri ay,,nan su dady sales sukai ta rarrashinsa dan kmr yaro yakoma musu kuwa, saidaqyar yayi settling xuciyarsa da kansa sannan yayi saurin barin room din dukansa. burinsa ya'isa office d'insa koya samu wata nutsuwar acan, danshi kota b'acin kayan da jikinsa sukai bai damuba daya chanza su, haka yawuce yana goge hawaye xuciyarsa na cigaba da rawa dud inya tuno cikin sa na baby neylar yafita da gske kuwa, haka ya'ida wucewa yashige office dinsa ko ganin gabnsa baiyi sosai, gefe guda GA kiran wayarsa da momynsa da yunus gamida amarya zarah dasuketa famanyi amman kwata kwata yama rasa ta'inda ake daukan wayar ma a rayuwa bare yayi qoqarin yin hakan. haka suka zauna asibitin harzuwa lokacin da'aka kira sallar la'asar su dady mukhtar suka nufi masallacin asibitin danyin salla yayinda mama zainab taje gida itada baby amnat daukewa heenduh kayan dazata sake,nan akabar maman menat wajenta, basu jimaba suka dawo akai sa'a ko minti uku su mama zainab ba suyi da dawowa ba heenduh ta farfad'o tareda bude idanunta. ahankali ta d'aga hannun ta na dama ta d'aurasa saman cikin nata jin wayam babu alamun wannan d'an tudun cikin nata data keji inta taba a wajen nan take ta fashe da wani gigitaccen kuka naqin qari harda turje turje banda baby neylar babu abinda taken tunawa . dasauri _su_mama zainab suka yo kanta suna faman rarrashi, momyn meenat kecewa "kiyi haquri heenduh insha Allah ubangiji zai canza miki wani kiyi haquri da wannan daya fuce kinji ko?, kihaqura ba'a fushi da ikon Allah kuma Inda rayuwa bata qareba bazaka yanke qauna ba ay daga samun haihuwan kudama zaku fara rayuwa yanzu,, kiyi haquri ki kwantar da hankalinki muma knmu bamuji dadin zubewarsa ba, amman babu yadda muka iya sai haquri, tashi muje toilet ki gyara jikinki kiyi wanka ga part nan dasauran kaya an dauko miki daga gida saiki cire wadannan na jikin naki dasuka baci, ganin qarin ruwa yaqare heenduh bata tsaya wata wata tasa hannu ta fusgesa harsu mama zainab namata fadan mimakon tabari akirawo khaleepan, shiru tai a haka momyn meenat takamata suka shiga toilet din tadan taimaka Mata da hada ruwan dumi sannan tabaro toilet din bayan ta'ajiye Mata kayan da zata saka, bata jimaba tafi to bayin sanye da doguwar rigar material green colour da gyalenta data yafosa aka, taqara wani haske sosai saidai kai daka ganta kasan tana cikin tashi hankali kala daban daban, dasauri momyn amnat takamota tazaunar da ita sannan tamiqe tana cewa''bari naje toilet nawanko kayan dakika cire,, da kallo kawai heenduh tabita batace komiba hartaga shigewarta toilet din kuwa, kallon ta tamaida can gefe tahango mama, zainab na salla Dan haka cikin murmushin qarfin Hali ta juyo ta dubi baby amnat data sata gaba tana kallo kamar mai tsaron lafiyanta tace "baby amnat kinsan office din yaya khaleepan ko? dasauri cikin jin dadi na ganin aunty tata na mgn tace '' eh aunty nasani dazun munje , yawwa tojeki ki kiramin shi, aiko dasauri baby amnat ta fuce, nan danan heenduh tamiqe ta zuge jikkar momyn amnat ta dauko wayarta data sakata ciki tun zuwanta gidan nasu, tareds wasu kudi data gani cikin jikkar ta dauko dubu uku dasauri tazuge jikkar tagyara mayafin kanta ta rufe fuskarta dashi tabi tawata kofar ta fuce daga asibitin tahau napep babu Inda ta sauketa sai tashar mota kuwa tabarin garin kaduna....... tarasa wanne gari zatace akaita gashi sai tambayrta Inda zata direbobin tashar keyi, batasan ko'ina ba batta zuwa ko'ina to ina zatace akaita kenan yanzu??,,,,