← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 178

Sashe 58

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"yakukai dashi?" sa'a tace "nima dai nace masa dai kuna biki be shine yace zai dawo gobe, snn yace kuma wai koya kira wayarki bakya dauka hakane? cikin ko'in kula heenduh tace"kinsan bakowace number nike accept ba barea tasa da bnsn taba" sa'a tace "haka ne, dannayi mamakin ganinsa qofar gidanku lokacin dana fito byn nmnki da naje sai kuma nai tunanin aike bawai 6oyayya bace a anguwar dan da tambaya daya ma za'a iso dashi nan, ko amsa heenduh bata bata ba saima tashi datai tana dube dube cikin dakin kamar mai neman wani abun. sa'a tace"qawata wai me kina nema be haka kiketa bincike ko'ina kuma kina yabud'amun kaya a jiki banfa son wulaqanci kin ma maisheni bola ko? tsoki heendu taja tace"yi haquri qawata wlh narasa Mina ajiye a d'akin nan yake mun wani wari wari can qasa qasa tun jia nikejin hakan mafa" "toh ko kusu ne ya mutu a dakin naki baki sani ba? cewar sa'a. heenduh tace "wama yasani tashi kitayi neman sa dan Allah ma, dan bazan qara ko wuni guda ba cikin dakin nan bare kwana batareda na ganosa bafa, dan na tsani launin d'oyi koya yake Allah kuwa". nanfa suka ma dakin d'ai d'aya did sun fidda kayan waje suna zuwa can kusurwa inda katifa ke wajen saiga wata leda baq'a da alama dakwai wani abu a cikinta ,had sauri suke wajen sunsunawa bayan sun daukota, saikuwa gashi exactly iriyar warin ne ke tashi a dakin. suna bud'ewa saiga kaza harts fara tsutsa kad'an. sa'a tace"kutmelesi ajiyar kaza kikai Ashe qawata?" mamaki heenduh tai sosai na tuno kazar da khaleepa CE yakawowa su mama wace aka bata bats Ciba harma ta lalace, Dan haka wani dogon tsoki tai tace''nina mnce da itama wlh, takusan sati, doctor be yakawo was mama ita, da akaban nikuma dayake banyi niyyar ciba saina jefata nan, kawo nan na fiddata bola ma Ashe itace dud ta hanamun sukuni ma mtss kayan banza" "amman qawata dasai kiba mai so yaci ai inda ke bazakici ba, ko almajiri kikaba sa zaki samu lada akan ki ajiyeta tayi d'oyi" cewar sa'a. a masife heenduh tace "nifa kin isheni malama, dan wanda yama kawo kazar bayya gaba na bare na iya tunawa da wata kazar da ya kawo harna bayar'' saa tace''ke kika sani dai kuma can tsakaninku ne wannan dan kun saba bawai yau kika fara masa rashin kunyarki ba bare abun ya zanemun sabo saidai kuma bansan mizai biyo baya ba dud inya juyo kanki dan kinsan ance mai kurum kurum na nauyin magana zaki ne inya miq'e haiqan, sannan kuma naga zaki iya zuwa gkdansu ki dauko komi kike so kici ko?'' heendu tace "eh idan naje na d'auki daga hannunsa ya fito abun koko? mtss niya mazo ya rabani da wannan baqar rigar kalar mai ita" sa'a tace "wacce ba'ai mata gwaninta oho dai ay riga kam dai rayi miki rana kuwa. taqarashe maganar cikin yiwa heenduh din dariya. qwace ledar kazar heenduh tai tai waje dan sawa a bola batareda ta sake tankawa sa'ar ba danta q'ulu sosai. haka ta yaddo kazar ta dawo (niko nace ayya hafsyna kaza ta tafi sai atari ta gaba wataqil an sami fuffuken nan da aketa mgn hhh). haka suka gyara dakin tareda fesa masa sanyayyar air conditioner mai dadi dan heendu kam badai gayu ba. nan bakin qofar dakinta suka shinfid'a carpet itada sa'a suka duq'ufa yin wani game a wayar heendun na wata 'yar mage Angela, dariya kawai suke abinsu. mama Zainab dake zaune can qofar dakinta tana gyara shinkafa 'yar Hausa wacce baba isma'il ya samo ya auno musu ita kwano d'aya yau da safe dan Allah yasa anyi cinikin kayan miyan nasa jia sosai kam alhamdulilla. to jin dariyar tasu ta isheta ne wajen hakan ne ya sata d'agowa tace "haba kuko? kai dan albarkar iyayenku in bazaku daina isata da wannan shirmen dararrakun naku ba to maza maza Ko kutashi Ku koma d'aki dan kuwa kun hanani jin tafseer a radio d'ina ynda ya kamata." dole kuwa sukai tsit tareda yin komi a cikin qasa qasa yanda mama Zainab din bazata ji sun ba. har cikin kanta taji sallamar tasa kafin qamshin turaren sa ya biyo baya. da sauri ta dago kanta Sam yaqi kallon inda suke itama ganin hakan yasata ta6e baki ganin ynda yaketa daure dauren fuska. qasa qasa ta cewa sa'a"mtss dubeshi" sa'a tace "handsome gy. hakan yake, kazalika qarfaffan takunsa gskia yai masifar sake had'uwa yau wlh qawata, dubi yanda fararan kayan nan na aikinsu sukai masa kyau, kazalika medial glass dindake fuskars.. buge mata baki heenduh tai tace"dalla malama surutunki ya isa hk, ina ruwanmu dashi ma to?mtss kune masu zubdawa mata class wlh" kan sa'a tace wani abu sai jisukai yana gaisheda mama cikin kalar maganarsa a nutse. cikin faraa mama Zainab take ansawa sannan tace"likitoci fa koda yaushe babu hutawa khaleepa naga yauma weekend ne lahadi zaku je asibitin knn. "mama nama dawo at, dayake run qarfe 6na fita sand emergency da aka kawo wata baiwar Allah, shine naje, amman kuma dai alhamdulilla ynxun" mama Zainab tace "Allah Sarki Allah sawqqa to"! "Amunn mama, yana maganar ne yana decline na kiran da zarah ta addabesa dashi tun dazun. soyake ya cewa heendu ta dauko masa rigar ta jia amman bakinsa yai masa nauyi yaji komi yasa oho. sosai yayi farinciki lokacin da yaji mama Zainab tace"heenduh dauko masa rigar nn man saiya kaiwa masu ita tad'oro ko zasuyi amfani dashi" tsam heenduh ta miqe ta shiga daki ta dauko afterdress din a zuciyar ta take cewa"nasan wajen wannan banzar zarah din zaije, saiko gashi ile tana miqa masa rigar kiran zarah na qara shigowa wayar tasa. dauka yayi wannan karon"gani nan zuwa" amsar daya bata knn ya kashe wayar. wani qululu taji ya tasoya tsaya mata a saman qirjinta na jin amsar daya bawa zarah. komawa tai ta zauna kwata kwata taji ta kasa samun cikakkar nutsuwa, dubn sa'a tai taga hankalinta naga game dinsu yanzun, tasake dubn sa taga firarsa kawai yake da mama. tunani take shin wai tawace hanya zatabi tai masa ba daidai ba hartai sanadiyyar hanasa zuwa wajen waccen ballagazar cikin dad'in rai da kuma fanshe haushin klr wulaqancin dayai mata ne jia?! tsam kuwa ta miqe cikin qwarin gwiwa da wani murmushin ta na samun mafita datai. kai tsaye ta nufi wani qaton bokitin tsarinsu ta daukosa tsagwayam tazo wucewa ta daidai inda yake aiko ta taka wani taklmin ta mai tsini da gangan ta sheqo masa tsarin gaba d'ayansa tun daga saman kansa har zuwa fararen kayan jikinsa sannan ta duqe gefensa tareda cewa"wayyo sannu ban lura bane nazo rage ruwan ne a maguji shine ya kucce mun a han.... babu zato taji mama Zainab ta d'auketa da mari tass Tass abinda maman bata ta6a yi mata ba kuwa wato dukanta. sa'a daman tunda taga sanda heendu taiwa doctor khlpa wannan aika aikan hannuwa bibbiyu tasata rufe bakinta cikin wani tsantsar mamaki na heendu. fada kawai mama Zainab take mata tareda cewa"ashe bakida mutunci yarinyar nan?! babu abinda zai hanani zaneki gidan nan kuwa, tayi maganar tana shirin fizgo wani kebel dake jikin wata qusa a bango. aida wani masifar gudu heendu ta shige cikin daki tana qwalla, taba qofarta garamm ta rufe da qarfi bayan tasa sakata. har qofar dakin mama ta isa tana cewa"bazaki bud'e mun q'ofar bane koko? khaleepa datun sanda abun ya faru kansa na duq'e ransa sai tafarfasa yake masa, to sai yanzun ya samu ya dago ya sake duban jikinsa dan ko gaba daya ya 6aci kaca kaca kamar zaiyi amai yakeji a lokacin tsabar qyanqyamin daya shigesa. miqewa yai tsaye bayan ya zare glass dinsa dasauri yabar gidan anan qofar gida sukai kusan karo yunus daya biyosa gidan dan yaga shigarsa gidan baba Ismail din tun lokcn.. kama baki yunus yai sannan kuma ya fashe da dariya ganin khaleepa dayai dagaje dagaje da tsari mai manja. daqyar yasamu ya tsaida dariyar tasa yace "huhhhhhh kaiii!! cancad'i wannan daga gani aikin tijararriyar yarnyar nan headache ne wlh, fadamun man abokina taya hakan ya farune to waima tukun?" wani takaici ya qara kama doctor khlpan na dariyar qeta da yaga yunus din na masa jiyai kamar ya masa wani kalar mummunan kutafo gamida shaqosa koya sauke hushin sa a kansa, amman ganin yanda mutane keta kallon jikinsa ne yasashi daure zuciyarsa yabar wajen kamar ya fashe da kuka yakeji tsabar baqin cikin da heenduh ta qunsa masa a safiyar yau d'in nan......
Chapter 58 · 0% Book details