← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 178

Sashe 24

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ya zama mallakina wannan saqo ne na baka kaje ka fad'awa su baffa hakan inkuma kunyi musu kuna iya d'aukaka q'ara har kotun q'oli ina nan ina saurarenku. In kuma sunada buqatar gidan nasu to suzo muyi list na kud'ad'en da na kashe muku dukkanku na mecca ku biyani saiku karbi key d'in gidan. tuni ismail yaji kansa yafara jujjuya masa dan girman Allah wannan wace iriyar jarabta ce haka ta samesu ne? tamvayarda yakewa kansa knn. Wai yanzun yayan sane ke masa iriyan wannan cin mutuncin da iyayensu dan yayi kud'i komi ne? Kuma wai har yake iqirarin cewan yayi garkuwa da gidan su sai anbasa kud'i? Kai duniya ina zaki damu??? girgiza kai yayi bai qara gigin cewa komi ba danya lura da kallon qiyayyar da yayan nasa ke aiko masa dashi zalla ko sirki babu. a kuma dai dai lokacin ne mukhtar ya gama sallamar yaran da suka gama kwashe kayan tas dai dai da tsinken sakace basu bari ba kuwa kamar yanda shi mukhtar d'in ya umarcesu dasuyi. suna fita shima isma'il yafara qoqarin fita daga gidan daqyar yake jan qafarsa ma dan mutuwa da jikinsa yayi amman dudda haka saida mukhtar yace"dalla mlm yi sauri ka fitar mun daga gidana zan rufe, juyowa isma'il yayi ya zubawa yayan nasa jajayen idanunsa yarasa mashi amsar dazai basa dan takaici, daqyar yace ''yaya yanzun hakan kaga ya fiye maka ka mallaki gidan daba haqqinkaba kai d'aya alhalin su baffa na raye a duniya? wani banzan qazamin kallo mukhtar yayi masa sannan yace "ok in kanason kaima ka mallaki gidan saikaje ka kashesu baffan inyaso saimu raba gidan tare" zaro idanuwa isma'il yayi waje gabansa na sake bugawa anya kuwa qwalwar yayansa bata samu mix ba da jini ba a cikinta? dan abubuwan nasa kam it's over yanzun, kuma ya shallake iyaka tareda tunanin manazarci. Abunda yake tambayar ransa kenan yana cigaba da kallon yayan nasa, mukhtar ganin ismail d'in yaqi fita ya tsaya yana kallonsa kawai sai yasa hannuwansa duka buyin ya ida tunkude isma'il d'in k'ofar gida harya gicce qasa tareda d'an matumbili dan faduwar dayai qasa warwas, daqyar ya samu ya miqe da taimakon baba yawale daya iso wajen yanzun, bayan d'agasa dayai tsaye, baba yawale yana fad'in "kai kai subhanalla mukhtar ya haka kuma? Ko kallonsa mukhtar baiba ya dubi isma'il ya nunasa da keys din gidan yace daman tuni batun yauba na lura kana min baqinciki da qyashi gamida hassada a kud'ina da nayi to wannan kuma matsalar kane nidai nasan nai maka nisan da har gaba da abada baza kamo niba,banza matsiyaci kawai, a razane baba yawale har carbaharsa da carpet d'in sallarsa dake hannunsa suna zamewa daga hannunsa zuwa qasa dan daga masallaci suke shida baffa tun bayan gama isha'e suke tare a masallacin sai yanzun suka fito shi baffa ya wuce gidan isma'il shi kuma yayo nan gida, yace "haba kaikuwa d'ana mukhtar miyake damunka kake ciwa dan uwanka mutunci haka ta hanyar gaggayya masa magana?, a fusace mukhtar yace "kai tshohonnan babu ruwanka fa badakai nikeyi ba, in kuma kaima kanada buqatar in amshi haqqi nane na kudin mecca dana biya maka ta hanyar amshe maka gida to kacigaba dasamun baki da katsalanda a cikin lamurrana, isma'il daransa ya 6aci matuqa yakoci kwalar rigar mukhtar yana girgiza sa take fadin "billaheel azeem bakai arziq'in dazan maka hassada ba, waikai yaya bakada mutunci daman ashe? yanzun baba yawale wanda ke matsayin uba d'aya a garemu kobayan ran baffa shi kake neman zagi?, to wlh bari kaji in kaimun nina jure wlh bazan juri kaiwa iyayenmu ba" tuni rigima da buge buge kuwa ta kaure tsakanin masoyan 'yan uwan biyu ada maqiya kuma a yanzun. tun baba yawale na rabasu iya qarfinsa har saida suka gajiyacceshi suka yardashi qasa wajen kaiwa juna bugu da naushi uwa 'yan dambe kowa naji da qwanjinsa kuwa, kankace miye wannan tuni jama'ar anguwar sunyi musu zobe daqyar aka rabasu dud sunjiwa juna ciwuka a jiki inda mukhtar ya farfasawa ismail gefen wuyansa da kunnensa, shikuma isma'il ya kwantarwa da mukhtar jini a idanunsa guda daya da kuma bayan wuyansa g har d'an kumburi yayi,, mutane saicewa suke "haba kaikuwa alhaji mukhtar yada girmanka da darajarka zaka fito rariya kake haka da qanenka? qanen kane fa miya faru da zafi ne haka? a fusace mukhtar yace"niba jinina bane shi din danma na tsanesa kuma daina had'a ni dashi,haqqina nazo karba kuma na karba dan haka kowa yasan inda dare yai masa kona kwaso muku bataliyar sojoji billaheel azeem kowa kuwa sai ya kwana gidan army barrak dinsu tareda azaba mai tsanani banzayen mutane kawai daku magulmata" aiko da wanda suka zo rabo dan Allah da 'yan ganin qwam d'in kuwa tuni suka yaye suka bar wajen sumi sumi jin maganar sojoji. mukhtar har kusada isma'il ya matso sunata huci kuwa kamar zakuna, yace "blllahil azemu kuwa isma'il yanzun qazamar gaba ta qullu tsakaninmu bani bakai ba ahalina babu naku, ko saman hnya ka ganni inma kallo nakai Allah ya isa bare harka tanka mun" a fusace shima isma'il yace ''saimi? yo aje a hakan saimi? koka dauka kaika d"aine dan zafin kai" banza mukhtar yai masa ya duqa qasa ya dauki keys dinsa ya wuce wanda daga haka bai qarabin ta kansu ba, kamo hannun isma'il baba yawale yayi suka nufi gidan isma'il din, koda su baffa sukaga halinda isma'il take tuni suka rude suna cewa kai isma'il "miya samu jikinka haka jini gefen bakinka da hancinka? sai lokacin ma isma'il ya tuna dako babu shakka jinin dazun ne ya dawo wanda mukhtar yayi masa habo tun cikin gidan nasu ma, zubewa qasa yayi yana kuka yake shaidawa su baffa dud abinda mukhtar yace a gaya musu, yaci gaba da kuka yana cewa baffa "wannan ba yaya na bane mai sona kodai an canza mana shi ne?!, ya cigaba da maimaitawan cewar "baffa ya qwace muku gida yace saikun biyasa kudin makkansa fa? sannan yace kuma babu ahalunmu babu nasa haihata haihata ko magana karna qarayi masa bare na nuna nasanshi to dan Allah baffa ku gayamun wannan halin yaya nane?"! salati su baffa sukeyi harda baba yawale dasai yanzun yasan makamar zancen shima. gani sukayi baffa ya miqe tsaye inno da jikinta gaba daya ya saki kamar zatai kuka tai saurin cewa "mlm ina kuma zaka?" "ina xuwa" abunda yace knn ya fit. kai tsaye gidan mukhtar ya nufa ya qwanqwasa kofa saiga mai gadi ya leq'o ganin baffa ne yasashi zuqunawa har zuwa qasa ya gaidashi,baffa ya amsa sannan yace "mlm sani yimin mgn da mukhtar inyana ciki" tuni mlm sani mai gadi yahau sosa kai dan kunyar abinda zai cewa baffan kmr yanda mukhtar yabasa sallahu yanzun daya shiga gidan. daurewar Mlm sani mai gadin yayi yace "sai dai kayi haquri baffa dan alhaji yace kowa yasake zuwa gidansa indai daga bangarenku ne kada aqara bari ya qara shigar masa gida ciki kuwa hardaku yace" Allah sarki jin hakan da maigadi yace tuni sansanyar zuciyar baffata qara karewa babu zato baffan yaji hawaye suna sulalowa daga kuncinsa,da saurin sa ya gogesu da hannunsa sanin dayai cewar masifar dake faruwa inhar iyaye na zubdawa yayansu hawaye, haka yajuya ya tafi. daman shi bawai maganar kwace gidan da mukhtar din yaiba yazo yai masa ba, a'a zuwa kawai yayi dan yaji dalilin dukan isma'il d'in da ayi da kuma tambayarsa miyasa yake son canza halayensa na gari zuwa akasin hakan?? haka baffa ya karya kwanar gida yana tunanin wannan wane *rubutaccen al'amari* ne ya samesu wannan lokaci?. haka yaci gabada tafiya yana goge hawayen fuskarsa da suka kasa daina zubo masa har lokacin, dudda qoqarin hanasun fitowa dayakeyi kuwa amman abun ya faskara!! ,,,
Chapter 24 · 0% Book details