← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 178

Sashe 20

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

nasu zai kasance. tun bayan tafiyar su mukhtar da sati daya nan masu gyaran gidan sukazo fara aikinsu. yayinda firdauseey tasa aka kwashe kayan gidan duka ta kai d'akin mero ta ajiye mata su dan tace ta bayar dasu dan itama sabbi zata siya mata, masu gyara kuwa basu jirkinta ba akasa mota ta rushe gidan babu wasa aka fara aiki, abinka da angama biyan kudi na komi nan suka hau aiki babuji babu gani wanda ya d'aukesu har tsawon satittika sannan suka kammalasa duka. gidan babu abinda ba'a saba irinsu esi kuwa ko ina kabi ta gidan saika sameta uwa uba kayan dake falon da kuma saman dakunan zaka rantse da allah cewar inka kalli fuskar gidan zuwa gate dinsa isuwa harabar farfajiyar makekiyar barandar su ta wajen gidan harya zuwa dakuna tofa zakace gidajen qasashen waje ne aka d'auko aka ajiye musu shi sak. wannan kam shi ake kira da a ljannar duniya cewar meron tsimbe da tazo ganin gidan dud tabi ta rud'e ta gigice da santin gidan,bama ita kad'ai ba har 'yan unguwa maganar qanqararren gidan mukhtar sukeyi. firdauseey tuni ta tare a gidan ko tadan jira alhajin gidan ma ya dawo ta gagara. kullum mero tana gidan har kwana takeyi tun mlm zayyanu na mata maganar rashin dacewar kwanan nata harya gaji yai shiru sakamakon harshe datake finsa. kullum kuwa sai firdauseey tayi waya da mukhtar amman koda wasa bata ta6a cewa ya bata su baffa ba su gaisa, kuma shima baima kawo komi a ransa ba inda gani yake insun gaisa dashi kmr sun gaisa dasu baffa din ne. yauda gobe inji yan magana asarar mai kwana har gashi an fara d'auko alhazawa 'yan makka. dan yau kam tun safe firdauseey ake rawar jikin yin girki dan jirginsu mukhtar gab yake da sauka qasar Nigeria. bata jimaba ta kammala masa hadaddeyar fridrice dinsa mai hadin coslow na barma a cikinsa, sannan tai masa tuwon shinkafa miyar ganye da kuma lemummuka har kala uku wanda tayi da kanta kuma dud cikin girkin babu wanda batasa masa ganyen maganin nan ba kuwa a ciki, yayin da ta girka wasu baffa suma abuncinsu na daban dudda ya kasance kuwa iri d'aya ne dana mukhtar d'in dandai su banbancin kawai bata sa ganyen maganin nn ba a cikin nasun, abinda kuwa yasa ta girka musu iri d'aya kuwa tasan mukhtar na iya cewan kalar abincinsa shi su baffa zasuci suma. dan kokadan bai yarda yaci abu mai dadi ba batareda ya kawowa iyayen nasa nasu kason ba qa'idarsa kenan kuwa kullum leda uku yakeyi yakawo daya gidansa daya gidansu daya gidan Ismail cike da kaji yhugurt ice-cream dss. hakama abincin karin safe da rana da akeyi da nama zu6u zu6u a ciki dole saiyasa an dibar musu yakai musu, hakan kuwa ba qaramin k'onawa firdauseey rai yake qara yiba da kuma tsanarsu baffan da ismail. biyar dai dai su alhaji mukhtar suka dura airport, bada jimawa ba motar kamfaninsu tazo ta kwashesu da manyan jikkunansu na tsaravar mecca, gidan su mukhtar din suka sauka gaba d'ayansu. dudda mukhtar nason xuwa yaga firdauseeyn tasa dajin dumin babynsa amman kasa tashi yayi sabida jama'ar dake shigo musu barka da dawowa ciki kuwa harda surukansa maman Zainab da mlm zayyanu. baba yawale bai jimaba yatafi gida dan hutun gajiyar hnya, baifi minti biyar ba da fita saiga firdauseey ta shigo gidan cikin shigarta mai kyau wacce ta karb'eta, cikinta kuwa ya fito sosai dan wata matsayi ne take haihuwa, jar atanfa tasa riga da zani sai farin gyale mai ratsin jaja a cikinsa, nan taiwa su baffa barka da dawowa a zuciyarta cewa take "hmmmmm samun farincikinku ya kusan qarewa indai kuwa daga mukhtar ne tsoffin kawai" ko kallon zainab bataiba bare ta tnka mata babu wanda lura da hakan kuwa wajen face Zainab din da ismail. haka firdauseey ta ajiye musu abincin tadan jima a gidan sannan ta tashi ta fita ta koma gida. shi kansa mukhtar yayi mamakin jimawarta gidan nasu dan zai iya q'ilgawa da aurensu zuwan firdauseey gidan basu kwata kwara baufi sau uku ba shima a tsattsaye, itakuwa yana lura da zainab matar ismail kusan dud ran juma'a da alhamus nan take wuni wajen inno, shiyasa ko shaquwa sunfi yi sosai tsakanin zainab da inno akan ita din firdauseey . yaso ya cusa mata ra'ayinsa na zuwa kaida kai a gidan nasu dan su saba da inno itama sai iai daya lura bataso saiya barta dan babu takurawa a lamarin kowa yagyara dan kansa ay a cewarsa. ganin baffa ya dubi abinci yakaiwa baba yawale yadawo nan inno da zainab sukai 1 plate baffa da ismail suma suka zuba nasu nan, har mukhtar yayi nufin sanya hannunsa cikin nasu baffa yaci aiko baffa ya dakatar dashi yace dole sai dai yaje can gidnsa yaci nasa wajen matarsa, ganin baffan bada wasa yake masa ba shiyasa ya tashi ya wuce zuwa gidan nasa, shi knsa gidan ba qaramin burgesa yayi ba matiqa gaya daya shiga cikinsa. saida yaji dumun matarsa da babynsa sosai sosai sannan ya rabu da ita ya miqe tsaye tareda d'aura towel Wanka kawai yayi tareda salla yana gamawa ya kuma nufi dining table dunsu inda firdauseey ke zaman jiransa yaci abinci , yana zama cikin murmushi ta matso da kujerata kusa da tashi tace. "hm mikakeson fara ci ne alhajina?" murmushin shima ya mayar mata yace "ni wannan qamshin abuncin yayi dad'i fa hajiyata, fara samun fridrice ma dai to dan yau abincinnan naki mai dad'i yanda nai missing din nan nasa dud yau saina cinyesa rass" fari tayi masa da ido tareda sakin 'yar dariya sannan ta fara zuba masa lemo ta ajiye masa agabnsa taresa tura masa plate din Friedrich din kamar yanda yace, babu wata wata ya d'auko spond da nufun fara ci tace "waitt alhajina aiki nane ay ciyar dakai" murmushi yayi ya sakar mata cokalin datake qoqarin kar6a garesa, nan ta d'ebo abuncin tasa masa abaki ya karb'a tareda taunawa a hankalin harda lumshe idanuwa alamun dad'in girkin yayi masa sosai, cup din lemon data hada da ganyen sihirin nan ta d'ora masa abaki nan shima yafara shan lemun, sannan daga bisani ya karb'i cokalin daga hannunta yana mai cigaba da cin abincinsa da kansa ita kuwa sai faman kallonsa take tana sakin murmushi na cin nasarar tasu ga alama...
Chapter 20 · 0% Book details