← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 178

Sashe 35

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

By
*Xexen Fasaha*
[1/17, 3:10 PM] Xainab Documen: 👁👁
🥡🥡
👁👁
*DA SAURAN KALLO !!!*

Story and writing
by
Xayyneb 💤💤

Fasaha online writers f. o.w.

*🌳imparting valuable knowledge and entartaiment is our concern*🌳.

~dedicated to my mom Sadeeq hawwas~

-https://www.facebook.com/Fasaha-Online-Writes-751775151851852/?referrer=whatsapp.

```Afuwan page d'inda ya gabata an samu type errors, mntawa nayi na turo muku shi bawanda naiwa editing bane ashe```•

👁🥡👁
🅿2⃣0⃣.
babu kalar haukan da firdauseey bataiba da taji mutuwar meron tsimbe uwarta, tanaji tana gani wasu yan tsirarun mutane da basu fi su 10 suka wa mlm zayyanu kara akaje rufo ta.
iyakar ta duniyar kenan mero aje a girbi abinda aka shuka a lahira cewar wasu daga cikin mutanen wajen.
saida firdauseey tai sati d'aya sannan aka fara samun kanta daga d'an q'aramin haukan data somayi,
tana qara dawowa hayyacinta kuwa banda kuka babu abinda take sai da sannu sannan ta dangana dan ganin cewa meron tsimbe fa tatafi bawai dawo mata da ita za'ai ba, kuma ita yanzun in zata ganta ai sai
iya wajen inda gudun ceton ranta ya tsaya dan babu wnda ya ta6a mutuwa ya dawo bare a fara ta kanta. ahaka dai har aka kwashe watanni har bakwai da rasuwar meron tsimbe ko, lokacin firdauseey ta murmure tasaki ranta gaba d'aya ta kuma d'ora daga inda ta tsaya na rura wutar qiyayyar isma'il a cikin zuciyr mukhtar kullum kuma cikin cin nasara take.
amincin su kuwa tsakaninta da hjy Hadeeza gaba kawai yake dan ynzun hjy Hadeeza ke zuwan musu wajen boka tana karb'o wasu qarin magungunan suyita bankawa mazajen su kuwa, ynxu kam duniya ta zame musu sabuwa dal a leda.
kullum mutane suna q"ofar gidan alhj mukhtar maula wanda zuiyarsu take a mace knn, wataran inya fito ya basu wani lokacin kuma yaqi fitowa harsu gaji da zmn jirnsa qofar gida su tafi suna masa Allah wadai.
wannan abun kuwa na matuqar qonawa firdauseey zuciya ita tafison taga shima isma'il yabi layin 'yan maula a wajen mukhtar yanda zatai masa dariya kuma taji dadin sake wulaqanta sa amman sam yaqi zuwa, wannan yasa a daren ranar ta samu mukhtar zaune a falonsa yana kallon labarai na legos ta zauna kusa dashi khaleepa na hannun ta, da sauri mukhtar ya karb'esa yana masa wasa amman sam yaron yaqi dariya yanda ya kamata, mukhtar ya dubeta yace ''gskia madam yaron nan naki saraki ne dan inya girma ba qaramin miskilin mutum za'ai ba, yanzun kalli fa sai dai yaimun murmushi innai masa wasa bawai dariya ba" firdauseey tace "hmm alhajina knn, kai dan yana ganinka nema kullum shiyasa kasamu ma murmushin amman in baki suka shigo bakaga yanda yake komar musu ba, kadan daga halayan khaleepa na knn tun tuni nima na fahimci hkn, shiyasa nike masa laqani da mai tsada na, hmm amman dahar wani za'a cutar man wannan kyakkyawan yaron nawa a had'a sa aure da 'yar gidan matsiyacin nan wanda kansa ma nazo mu tattauna yanzun hakan nan, mukhtar yace "wannan ai tsohon zance ne kada ki damu madam dina, dan angama wuce wajen tuntuni bana tunanun suma basu mance wannnan jinjirin auran ba da baffa na ya daura kan ya rasu dan matuqa sunji tsoron abunda nace zan aiwatas garesu muddin suka sake *gskiyar magana guda d'aya* ta fito daga bakinsu, dan haka in sun gaji da ajiye tar tasu sayi gaggawar aurar da ita a cikin adalcina na cewa zan 6atata ga maza a tambarin dud wnda yazo nmn aurenta danace zan sa a 6atar dashi un bai jiba amman yanzun taci albarcin auren d'ana dake kanta dan haka yanzun sunada right din aurar yarsu ga kowa ma amman badai gold boy dina ba" cikin jin dadi firdauseey tace "wlh kuwa suje can su qarata matsiyatan" mukhtar yasake cewa "mman wane batu zamu tattauna game dashi din kmr ynda kika ce yanzu kuma?
harda gyara zama firdauseey tai tace
"naga wannan dan aikin teaching din nan da matsiyacin isma'il dinn keyi yana kar6ar wasu 'yan kud'i can nasa runtse ga hannu to shine na lura sai faman tadawa mutane kai yake knsa, yana alfahari dashi to inada buqatar kasa a koresa daga school din kwata kwata alhajina sai muga ta tsiya da feleqe iriyar nasa muga dami zaiyi taqamar ne? dan wlh so nike inga abinda zaici saima ya gagaresa ya zamanto mana a qarqashin mu zaizo nema mukuma musa q'afa mu hauresa in munso mu watsa masa tsaba ya tsattsaga in munqi kuma mu watsa masa garwashi ya fuce da gudu kamar karenmu lega na bakin gate din can"
wata 'yar q'aramin dariya mukhtar yasaki yace "indai dan wannan ne an gama madam din"
hakan kuwa ta kasance mukhtar yaiwa makarantar da isma'il ke teaching tsinke tun kan ya wuce office nasa ma, yaje ya sakarwa shugaban makarantar kudi akan maganar korar ismail, dayake an samu marar tsoron Allah frincipal din dudda yasan isma'il na sahun farko daga cikin mnyan malmai da suka bada babbn gudummuwa ta wadataccen ilimi ga yara a makarantar dan har award aka basa last year na nuna haziqancinsa da jajircewarsa amman bai duba wnn ba ya nuna qarfin ikonsa na matsayinsa nan take kuwa principal din yasa aka nemo takardun Ismail akai masa kaca kaca dasu dajan biro kora ta wulaqanci akai masa babu fansho babu garatuti gashi an bata rakardun nemn aikin da mummunan sheda a kai ta yanda indai anan Nigeria ne babu ynda za'ayi government ta sake daukarsa wani aikin kuma.
Haka mukhtar yabar wajen ko a jikinsa, ismail kuwa yana zuwa aka basa takardar kora batareda wani daliliba ya kuma tanbayi ba'asin hkn nan take frincipal din yace
"d'an uwanka ne ya biya akai masa wannan aikin kuma yace in kazo in gaya maka in kanada buqatar wani aikin to yana neman mai kula da karensa lega a gidnsa zaka iya zuwa ka fara ma aikin kula da karen daga yau ma in kaso, wannan saqo ne ya bani zuwa gareka kuma gashi na isar cikin ikon Allah dan haka zaka ita ficemun daga office na"👉🏽 yayi maganr yana mai nunawa Ismail din qofar fita a wajn da hannunsa.
Allah sarki Ismail rayuwa tai masa halin nata na rashin tabbas dan haka ko yana hawayen baqinciki yabar makaranta tareda mata kallon qarshe.
koda yaje gida ya fadawa zainab tausar sa taitayi tareda nuna masa amfanin haquri ga dan adam, inda take cewa indai yaya firdauseey ce tasa mukhtar kewa qanensa haka to da sannu zataita ganen qarshensu inda gashi ta fara ganin alamun hkn daga mamarta marigayya meron tsimbe.
dole tasa isma'il fara sana'ar gwari can bakin hnya tun lokacin, hkn kuwa ba qaramim faranta ran mukhtar da firdauseey yayi ba ganin qasqantar isma'il din hartakai haka, shiko isma'il baiji komi ba dan dayaje yana maula ana tozartasa qwamna ya yi sana'arsa komun qanqantarta indai zata dauki nauyin sa da kuma na iyalensa haka yaita sana'arsa kuma Allah ya sanya masa albarka ga abun dan shi kadai ke kalar sanaar wajen shiyasa dud kusan jamaar anguwar wajensa suke siyan kayan miya ga kuma sauqi da sauqaqawa dan sanin dayai tsada bata kawo riba, kuma kad'an mai amfani tafi mai yawa albarka.
a haka a haka dai kuma rayuwa nata tafiya babu abunda ya sauya daga muguwar qiyayyar da mukhtar kewa isma'il.
zuwa yanzun ma kuma mukhtar ya qara samun girma a office dinsu shiyasa arziq'insa kullum qaruwa yake, babu wnda ya kamo qafarsa a kudin dud doguwar santar anguwar sun nan dudda akwai masu halin kuwa a cikinta da kuma marassa shi remix ward knn.
wasa wasa kwanaki na tafiya har yau gashi shekara 23 da haihuwar yaran nasu..
haka khaleepa ya taso dason d'an uwan mahaifinsa tunda ya mallaki hankalin kansa kuwa, kullum sai yaje gidan tun mukhtar na masa fad'an daina zuwa har ya gaji ya barsa danba qaramin so suke ma khaleepa ba.
saidai kwata kwata khaleepa kokadan basushiri da heenduh ko shiga gidan yy iyakar mgnrsa da mama Zainab ne, dan ya fahinci heenduh akwaita da tsiwa, fad'a kuwa koda uban waye yinsa take inya 6ata mata, saidai tana shakkun khaleepa da kuma haushinsa na ganin girman kansa it's t much ga jama'a musamman mata, kodan yaga yanada kyau ne da kowace budurwa a anguwar take bada knta a kansa shi kuma yake yarfata da rashin ko'in kula kalar nasa ne oho. kuma dud intaso tana shiga godan babanta mukhtar tadauko kalar abin sha data keso ta fito tun firddausy na zaginta tana korarta harta haqura takoma cemata mayya yanda taga koda fakar ido ne sai heenduh tazo gidan ta dauki abinda takeso itada qawarta snn su fice inta ga dama kuma saita kwashe wata daya ko qofar gidn bata kalla ba bare taje, kuma in taje komi takeso bata roqon zata dauka saidi lawai ta dauka tasha ta wullar musu da robarsu nn tai fitowarta dan mmnta tai mata kaahedin kada ta qara daukar abunsu ta kawo mata shi nn ckn gida inda ita batajin mgn, heenduh kan turo red lips dinta jawir wur dasu tace ' to mama na daina' hkn kuwa bazai hanata gobe ta koma gidan ba inta kado mata, dan hatta yan aikin gidan sunsan da zaman heenduh headache kamar yanda sukaji yalla6ai khaleepa na fad'a mata dud in sun had'e ckn gidan nasu, ita kuma takan yatsuna masa kumatu tai gaba dud intaji yace mata ciwon kai din nan kuwa.
dayake khaleepa karatun likitanci yake shiyasa kwata kwata bai samun zama a gida inba weekend ba da zasu zauna shida abokn sa su yunus a nan barandar kofar gidnsu smn kujeru suna fira, abinda heenduh ta tsana knn kallo intazo wucewa ta wajen zuwa gidansu sa'a qawarta sukuwa abinda suka sarewa gaba knn kallon dud budurwar da taxo wucewa kuwa, musamma ma ita da suka fiye sawa ido dan cut cheif baby suke ce mata, dan heenduh kam ba qaramin kyakkyawan gaske bace, sautari itake tsokanar khaleepa fada inyazo gidnsu ammn shi ko kulata baiyi bare ya tanka ta, qwamma yai shirunsa yafiye masa in yaje gidan inya iske mama na wani aikin dadai ya biye matan harta sashi mgnr dole. danshi bb wata ma mace dake zaune rayuwarsa gaba daya bare yasa damuwar ta a ransa dan yasan karatun sa nada son nutswa addabarsa datake ne lokutta da dama shine fa harya sa mata sunan headache to dagann kuma kowa saiya dauki sunn daga cikin aboknsa yana ve mata hkn, musaman babban abokinsa yunus.
lokacin da heenduh aka zama yan mata sai rawar kai ya qaru dan tana jida kyaunta kamar ynda kowa ke fada mata cewa kalar kyanta ba kowane Allah yaiwa baiwarsa ba a 'alumma, shiyasa feleqe iyayi rangwada tsiwa fafa da nuna ita din babban yarinya ce babu wanda heenduh battayi wannan ne ke qara sawa khaleepa jin haushinta a ransa danta kula kan heenduh ya fiye rawa ba kadan ba.
ahaka har ya tafi qasan waje dan qaro karatunsa wanda hkn ba ba qaramin dadi heenduh taji ba, dan ganinta kusa dashi baqaramin laluri take daukar abun ba, kuma koba komi sun daina takurata da wannan muguwar majalissar tasu ma.
saida ya shekara d'aya cip sanna ya dawo Nigeria cikin wannan satin da kwalinsa na cikakken likitan mata ta kowane fanni wannsn kenan, doctor khaleepa ya qara girma yazama cikakken namiji qaqqarfan gaske
sabida ya biyo jikin babansa mukhtar dogo qaqqarfane sosai ko ina kuwa na jikinsa a murd'e yake cikeda yalwar gashi a faffaden qirjinsa da jikin hannuwansa gaahine kwance lu6 lu6 a kyakkyawan farar fatarsa, yanda kasan balaraben mutim iriyar na musura dun nn tofa haka doctor khaleepa ya koma sak, tsare gida kuwa da rashin bada fuska ga mata sai abunda yaci gaba, koda yadawo yaga heenduh yanda ya barta haka take dan bazata wuce iya kafad'arsa bama a tsayi, saidai yaga ta qara masa hske da kyau sosai komi nata yaqara cika dm dam dasu alamun maqerin budurci nata kera mata siffofinta kowane kwana, samari kuwa kamar su kashe heenduh dnma bawai kulasu take ba saidai saurayinta musaddiq daya nace mata kamar qarfen qafa dudda rashin kulawa da take nuna masa kuwa, kudi yake kashe mata bana wasa ba, wai nanma dan bata karba sai taga dama, dan harso yk ta dunga tambayar sa abu kai tsaye, amman taqi dan batada halin roqon maza ita dud rawar knta kuwa wannan kenan.
dawowar khaleepa wannan satin ne iyayensa ba qaramin had'a masa fatittitika na murnar kammala karatunsa sukai ba, khaleepa har aransa yaso kawunsa isma'il yazo wajen amman sanin halin dadynsa yasa yai shiru tukun.
kwana d'aya daya wuce ne wato jia mukhtar yaiwa ismail dirar mikiya a gidansa karo na farko tun rasuwan iyayensu kuwa, yai rashin mutunci akan sunbawa yaronsa abinda ba cimarsa ba yasha wuya harya ce saiya ramawa dansa,
ran heenduh ya qara 6aci ganin ynda ake cin mutuncin datake iyayen ta kan wancen dan qa'idar, dudda haqurin da baba ismail ke basa kuwa amman saida ya raunatasa a yau din sakamakon turesa da yayi da
motarsa har ya kaisu suka tafi cemist shida heenduh dan ayi masa dreesing.
in baku manta ba masu karatu a nan aka tsaida labarin.
Chapter 35 · 0% Book details