← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 178

Sashe 45

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ta miq'e hnyar gida heenduh kuma ta shiga gidan nasu qirjinta rungume da handouts dinta. ta hango mama Zainab cikin madafi da sauri heenduh ta ajiye books din tareda isa wajen maman tace"mama daga samun sauqi sai kifara shiga kicen ki bari na qarasa aikin" tayi maganar tana karbar robar hannun maman tata, mama tace "barsa heendu ba wani abun ma nikeba mai wahala kinsan tun wancen satin 'yar tiyar shinkafarmu da wake ya qare hakadai muketa manage na rayuwa a gdn, kuma kinga jia babanki bai zauna sana'a ba bare, inda daman dan abunda ya cinikanta ne a ranar yake siyo yar taliya ko gwangwanin shinkafa uku a samu na girkawa, to kinga yanzun haka bai jima da lallabawa ya fita wajen sana'arsan ba baici komi ba sai dan kingin nmn nan najiya, gashi kuma yanzun lokacin sanwa yayi babu abinda zamu dafa a ranar dole na tashi yanzun na nemo wannan tsohon garin rogon dan a kwada akaiwa baba yawale nasa abincin kamar yanda aka saba kai masan, dan haka jeki dakin babanki gefen gadonsa zakiga wani qullun baqar leda wacce aka sa masa nmnsa shima sai kixo ki miqo man langar kwanon da ake zuba masa abincun nasa saiki miqa masa" jiki a sanyaye heendu taje ta d'auko abubuwan ta dawo ta ajiye nan mama ta ida had'a kwadon ta zuba ma baba yawale a langarsa gamida d'an kullin naman nasa wanda suka kasa dashi a daren jiyan. kwanon heendu ta dauka tareda yafa gyalenta ta fita zuwa gidan baba yawale ta iskesa kwance da carbinsa yanata lazumi, zaunawa tai tareda ajiye masa kwanon a gabansa tace "gashi mai ran qarfe inji mama, baba yawale yatashi zaune yana fadin "madalla zainabu Allah shi albarka bata gajiya da hidima Allah saka da gidan aljanna" "amunn mai ran qarfe,, jiya bakai cigiya taba ko kaga banzo firan dare ba muda sa'a?, baba yawale yace "ai nazata kina gidan giggonki d'ahara ne mai quli quli kinje cinye mata zogale sai gashi khaleepa ma ya shigo dashi ne muka yini dashi anan a tare ba hayaniya kalar taki, tabe lips dinta tai tace "oho kenan ma qwamma da Allah yasa banzo ba, yace "meko sabida mi? kada dai nace har yanzun baku bar wannan halin naku ba? to Allah kawo ranar sasanta wa, zumbur heendu tai ta miqe tace"aa mairan qarfe ba Amin bafa, baba yawale ya kama ha6a yace "ikon Allah, amman kinsan ai yafiki kirki shiyasa kike kishinsa a wajena, yayi maganar cikin tsokana. "tabb aiko bai fini kirki ba saidai neman suna ni kaja ma nai tafiya na gida bazan zauna ba"ta turo kallabi gaban goshi tai ficewarta gyale a kafada guda d'aya. baba yawale cewa yake ''ki gyara mayafin jikinki danke ba kamar kowace budrwa kike ba amman ina ko jinsa batai ba tayi gaba abinta ta fice, girgiza kai kawai yayi zuciyar sa na masa rawa a dud sanda ya tuno dadadden sirrin da suka boye na auran yaran, anya kuwa zasu cigaba da zura ido ga yarinya da aurenta ammn take tareda samari? anya basu so kansu ba? sukaji tsoron abun halitta sa6anin wanda ya halicci halittar shi ba azzalumin kowa bane? shikam yarasa kwanciyar hankali tun sanda yaga heendu takai munzalin cikakkar budurwa gani yake kowane sa6o heendu ta aikata batareda sanin cewa tanada aure ba a kanta tofa tabbas tabbas la shakka sune zasu kwashi zunubin nata inda dai ita harga Allah bata sani ba shima khaleepa din haka kuma, sune dai suka sani gskia dole yasan abunyi kuwa dan bazai dawwama ba a hakan, yanajin shifa koda zai rasa ransa kanya rasu tabbas saiya fadi gskia a dud snda yaji wani ya bujirowa da iyayen heendu maganar aurenta kuwa. dan babu labarin aure kan aure ko a cikin musulinci kuwa, dan haka ya q'wammace ace sanadiyyar hakan zaibar duniya komi mukhtar zai masa saidai yasa ai masan koda kisa ne kuwa qarewar kaq'e dayace zaisa ai masa kawai shi yanzun dai abu d'aya kawai ya sani bazai taba bari heendu tai aure kan aure ba muddin yana da rai kuwa wannan alqawali ne. bude abuncin yai ganin nama a sama yasan cewa samosa sukai bayin Allah, qwarai sosai yake mamakin yanda suke basa kulawa tamfar baffa komi zasu samu a gidan nan koko kuma zasuci tabbas saisun kasa dashi komin rashin dadinsa haka zalika komin dadinsa kuma, yawansa ko kadan dinsa. bismillah yai tareda jawo abincin ya fara ci bakinsa dauke da adduar dayakewa su baba isma'il fatan gamawa lpia gamida maido hankalin d'an uwansa kusa dashi dan cigaban zumuncinsu. heenduh kuwa na fita wajen sa'a taje ta karb'o kud'inta d'ari biyar daga nan ta biya shagon da hjy firdauseey keda 'yan haya dayake dud anguwar nan ake siyar da provisions da kayan abinci sbd shagunan nata a jere suke sama da 20 , dan anguwar tasu makekiya ce dan kowace mota zata iya shigowa ta fita kuma lpia. to nan ta shiga shagon farko ta siyo musu shinkafa da kud'in rabin tiya saurin canjin kuma ta sai musu manja da magi inda tasan sunada sansamin tasshi a gida kuma, koda ace babu saisu haqura suci haka nn inda sun saba. Koda ta koma gida ta ba mama Zainab kayan tai mata bayanin da kudin makarantar tane ta siyo musu abincin har qwalla mama Zainab ta goge a fakaice tasan heendu dud rawar kanta tana da tausayin iyayenta wannan ke nuna mata cewa ko bayan ransu heendu zataci gaba da alherinta ga mabuqata muddn ta samu damar hakan cikin bud'in Ubangiji, shiyasa kullum cikin zuciyarta tanaiwa 'yar tata add'ua dudda wasu halayen nata datake k'i tasan nan gaba ta q'ara hankali a matsayinta na mace zata daina ne, haka suka kasance a yinun ranar itada mamarta, kuma taji dad'i q'warai da taga khaleepa bai sake waiwayosu ba har dare suka kwanta barci. khaleepa kuwa sai wajen qarfe 11 saura ya shigo anguwar daga kallon ball shida yunus ajiyesa yai gida sannan shi kuma ya karkata kan motarsa zuwa gidan small dad d'in nasa sai dai kashh!! abinda ya guda ne ya faru, wato har sun rufe gidan su, yasan maybe sunyi tunanin bazai zoba inda ana gama sallar isha'e ne lokuttan shigowar tasa. juya hancin motar yai zuwa gidan su dai dai wajen gidan su, dayake daga gidan hjy Hadeeza sai nasu to ganin mota wata ja qirar pejo ta tare hnyar yasa shi cigaba da sakin horn amman shuru ransa ya 6aci ya ganin da alamun mai motar na ciki kuma yana 6ata masa lokaci shiyasa a fusace ya fito daga motar tasa ya isa ga motar nan ya leqa knsa ta qofar drive din ciki da nufin masa mgn ya basa waje zai wuce dayake glass din motar an dan zugesa qasa kadan sbd shigowan iska da shaqansa kuma, wacce yagani ne a motar liq'e jikin saurayin nata sai faman tsotsar juna suke kota ina haka kazalika rabin rigar ta a zuge yake har ta dawo saman cikinta ma. mamaki q'warai ne yakamasa dan bai taba tunanin tsabar tantirancin yarinyar yakai ga ta saida mutuncinta ga mazan iska ba sabida tsabar fand'arewa kalar tata, tsoki yaja da qarfi tareda cewa"excuse mlm bani hnya zan wuce dauke motar nn tk" abinda saurayin knn yaji a saitin tagan motar tasa, aiko da wani sauri ya dube khaleepa ganin yanda fuskarsa take a murtuq babu wani wasa yasa tuni mutumin yasha jinin jikinsa daga rashin mutuncin dayaso kartawa dud wani shege dayazo katse masa jin dadinsa da yayi nisa a ciki, dan wani mugun qwarjini daya gani ga khaleepa har wani d'an tsoro da shakku yaji ya kamasa dan gani yai guyn yai masa kama da zubin cikakkun soldiers a tunanin sama soja ne yasa personal din kaya yake round a motarsa cikin ward din, shiyasa tsoron sa ya nunku tuni jininsa ya dawo saman akaifar sa. itako cikin rawar murya da borin kunya tai saurin zuge zip d'in rigarta sama kamar ta nutse wajen takeji dan wata kunya data kamata, daqyar tace "am yaya khaleepa ka.. sam bai bari yaji mgnr da tk shirin fad'a ba ya ya qara had'e fuskan nan tasa a qyamace yabar wajen ya shiga motarsa shi kuma saurayin dayaga alamun b soja bane harya ji dadi ya daina tuno iriyar mugun dukan da zaisha daga belt din jikin khaleepa a tunanin sa. dan haka ckn saurin gaske ya gyara masa parking yai wucewarsa ransa cike da mamakin yarinyar harya shiga harabar gidan nasu abun na tuqosa tuni yaji kowace mace ma ta qara sire masa yagodewa Allah daba koyi sanin ynda ake so ba bare yayisa har ya wahalar dashi a banza. (shifa a tunaninsa so koyansa ake sannan a yisa ma) a haka ya kashe motar ya shige cikin gida yana sakin tsoki a zuciyar sa still hoton yanayin daya gansu bai baccewa tunanin saba kuma! .
Chapter 45 · 0% Book details