← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 178

Sashe 131

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👁🥡👁 🅿5⃣6⃣. **G* anin haka da Hjy Hadeeza tayi tuni yasa ta fasa wata razananniyar qara mai cike da ihu gamida zaman 'yan bori gaban Hjy firdauseey tana girgizata amman ina lokacin Hjy firdauseey tayi hannun riga da sanin mi duniyar tamu take ciki ne saboda sumewar datai bisa bala'in data ji data gani kuma muraran. kankace mi tuni kwaratsin ihun da Hjy Hadeeza ke ci gaba dayi yajawo hankalin jama'a dasuke wajen mushen gawar marakusa wasunsu suka fara baro wajen suna nufo su.. kuka take tana qarawa ganin jama'a sun musu zobe yasata fadin "Ku taimaka mana dan Allah bayin Allah mukaita asubiti suma tayi kada ta mutu dan Allah" to dayake da dama daga jama'ar sun shaida su hjy firdausey suna yawan shigowa cikin qauyen da motar su, kunsan jama'an qauye yawancin su da bin sahu dan neman qwaf anan ne suka tabbatar da suna zuwa wajen bokan can sakamakon sahunsu da suke lalabowa suna biyowa insunzo garin kodan suka qara kallon motar tasu datake dauke musu hankali da qyalli. dan haka suna ganin sune nan suka fara janyewa suna tafiya tareda Allah wadarai da su temakesu da take fada, dan wasu masu gajen haqurin cewa suke inama harda ire irenku masu zuwa wajen nasa kuka taru kuka qonen gaba daya da an rage mugun irin masifu kala da kala da ake fama dasu a duniyar nan na marassa tsoron Allah da zuciyarsu ta qeqashe a sabawa mahaliccin su. yazamana a wajen wanda suka tsaya dud su basusan su Hjy firdauseey din ba wanda suka sansun ne dai sukai tafiyarsu suna ida temaka jama'an da suke watsa fetur saman bukkar tsafin boka marakusa kafin su qyasta a Shana, nan take wajen yakama da wuta faaaaaaaal sakamakon laso ciyayin qasan dajin datai shiyasa wutar taita gudu har qasa tana niyyar tunkaro jama'an wajen haiqan, wasunsu da suka kunna wutar kuwa har cewa suke gwamma marakusa yaqarajin zafin azabar wutar duniya kamun yaje ya iske ta lahira(Allah mana kyakkyawan qarshe). hucin zafin wutar ne na azaba harnan kuwa ya iske su Hjy firdauseey dake wajen ga kuma wani mummunan hayaqi mai mugun wari dake tashi cikin wutar, warin kuwa in kana shaqarsa Uwa zaka mutu zakaji, shiyasa mutane sukaita gudu daga wajen dan tsira da lafiyarsu ga kuma wutar da suke gani sai bunqasa take tana feshi harda wata qara take saki quuuuuuuu Uwa wacce ake qarowa daga wani wajen tana qara yawa. hatta mutanen dasuke gabnsu Hjy Hadeeza runqa gudu sukai kuwa, wani wani farin bafullatani ne yai qarfin halin dawowa shida wani qaton saurayin dansa nan suka jawo qafafuwan Hjy firdauseey qiyyyyyyyyyyy a cikin ciyayin yayinda Hjy Hadeeza ta biyosu dan zafin wutar itama ya addabeta da warinta. saida sukai d'an nisa daga zafin wutar sannan suka daina jan Hjy firdauseey din wacce jikinta dudya gurje da qayoyi harya fara jini a wasu wuraran. dattijon yace"iya temakon da zamuyi muku knn Hjy" d'an nasa gambo yace "qwarai kuwa dan ko garin nan namu da kike gani to ko chemist na magani bamu mallaka ba bare kuma Uwa uba asibiti da kuke fadan akaiku,, yaqarashe mgnr tareda ballo ruwa a robar dake daure a qugunsa ya cire murfin tareda watsawa Hjy firdauseey ruwan a jiki wanda nan take sukaji ta kawo wata ajiyar zuciya mai qarfin gaske. Hjy Hadeeza cewa "kai ngd sosai mutanen kirki.... katsewa mgnr tata tayi jin datayi Hjy firdauseey na cewa "wayyo Allah nahh marakusa kadawo garemu dan Allah in kaga mana wannan babban aikin danafi buqata a rayuwata na rabuwan kawunan 'yan uwan nan wlh na yarda ka koma dan Allah kadawo"!!!! mgnr take tana qarar kuka tana qarawa harda dalalar da yawu gamida fece majina. itako Hjy Hadeeza kunya da takaicin Hjy firdauseey dud ya isheta jin yanda take bud'e asirin ta gaban mutanen nan 2 da basusan tare suke da bokan ba su. aiko dattijon da dansa najin hakan suka zabura gamida cewan dattijon"aho daman kuna tareda wannan mugun bokan kuna aikata mummunan aiki kuma kuka sa muka taimakeku? to wlh kuwa Allah ya isa temakonku da mukai" d'an ya amshe da cewa"aida munsani ma munbarku wutar ta laqumeku kudashi arna maqiya Allah, ashe ba'a banza mutane suka dare daga wajenku ba suka ki taimaka muku dan sunsan mugun halinku?, turrr daku na jikin la'anannen bokan nan marakusa, lallai kuma kuwa annoba kalarku a duniya inda har kuke zancen raba zumuncin Allah,, d'an kuwa yaci gaba da cewa cikin hucin zuciya "ay barsu dani kawai baffa yanzun zasu amshi hukuncin wahalar damu dasukai abanza wlh..Kan su ankara sukaga ya jawo wata zungureriyar dorina murtuqeqiya kalar ta bugun hird'a hird'an dawakai babu 6ata lokaci kuwa yaita lafta musu a jiki suna ihun ceto su kuma, kan kacemi jikinsu yayi rid'u rid'u aida gudu suka miqe suka arce shima d'an dattijon nan wato gambo yabiso da gudun nasa yadinga cigaba da kafta musu bulalar kota ina su kuma suna cigaba da kwarara ihu suna gudu suna sosa d'uwawuka da baya da baya,,,ba shine ya barsu ba saida yaga sunkai kusan qarshen dajin zasu fita waje hanyar jama'a sannan fa yahaqura ya koma sukai wucewarsa shida babansa suna qara Allah wadai dasu. hajaran majaran cikin wuya da azabar uq'uba su Hjy firdauseey suka fada motarsu suna maida numfashi, a 309 da hamshin Hjy firdauseey ta murza sityaring motar suka fuce daga qauyen sukaita tsala gudu tsawon awanni basune sukai burki ba sai a bakin gate din gidan ta. nanma wani mummunan oda ta dungayi da gudu baba sani mai gadi dake alwalar sallar la'asar yataso ya bude danya sheda horn din motarta. suna parking kuwa cikin tsamun jiki suka fito suka shiga falon gidan baba sani yabisu da kallo kawai ya girgiza kai yakoma yasake sabuwan fara alwala bayan Kalmar sa ta "Allah kyauta muku" daya furta a ransa. suna shiga falon kowacce ta zube nn warwas a qasa suna huhhutai. sunkusa minti 10 sannan sukaji jikin nasu da hankalinsu yafara dawowa waje daya sakamakon ruwan sha da kowanensu yasha Sama da robar faro uku uku, rarrafawa Hjy firdauseey tai ta shige toilet din qasa dan kam bata iya hawan benen, ruwan zafi ta kunno yana sauko jikinta tana zaune tubus qasa ko kayan tagagara cirewa, saida ruwan zafin suka ratsata ta rage jin radadin ciwon, kuma jinin jikinta inda ya farfasa ya daina zuba saidai shatin fasawar na nan rad'o rad'o sun kunbura. tajima tana gashi a jikinta na ruwan zafi sannan taji dan dama dama har ta maida kayanta jikinta tareda qudurtawa a ranta da bazata bari mai tsada yasan dukan dasuka shaba dudda tana buqatar maganin da zata shafa sbd rage radadun zungar daga garesa, saidai tasan mizata CE masa su samu maganin koda na shafawa ne a jiki dan rage zafin. haka itama Hjy Hadeeza ta shiga ta gasa jikinta sosai sannan ta futo tana nishi dan jiki daman gashi bai saba da wahala ba shiyasa sukejin abun sosai. saida suka dan natsa ne budar bakin Hjy Hadeeza said cewa tai "Amman dai ubangiji Allah ya tsinewa mugun mutumun nan da dansa, shege Uwa basamude ya kamamu yana ta jubga Uwa an jera masa jakuna gashi yanzun yasa mun tane da gashin ruwan zafi uwa masu wankan jego" dagowa Hjy firdauseey tai ta dubeta jiki a mace tace"hmnn ni fa har yanzun mutuwar marakusa CE tafi addabar min rayuwa ta gaba daya ji na nike uwa bani ba a jikina, dan ganin komi Nike tamfar a mafarki." saida Hjy Hadeeza tad'an gantsara sakamakon wata cakar zugar zafin ciwon jikinta dataji yaja ta soketa,, runtse ido tai tace "kai wash Allah na, daqyar tasamu takoma dai dai lokacin sannan ta dube Hjy firdauseey tace"yafa kamata ki cire tunanin boka marakusa a ranki inda ya rigaya daya mutu, kuma Alhj mukhtar dai kin samesa yanda kikeso to miye yai saura ana damuwan kuma?" sauke ajiyar zuciya Hjy firdauseey tai snn tace"eh dudda hakan Amman kamar in inason aqara mun wani zazzafan aikin ina kikega zan samu kamarsa? Ai babu" taqarashe mgnr cikin dafe kanta tana cigaba da sharben kukan baqinciki ga kuma zafin bulalar jikinta dake mata zugi dan abun kam 2 ya hade mata,,wanda tanajin rabonda a bigeta tun tana qarama sai yanzun da girmanta tasha zana daga qaton qauye harma kuwa yana neman zagwanye mata fatar jiki da dukan. dafata Hjy Hadeeza tai tace wannan ai badamuwa bane inada wani tantirin malami aikinsa yankar wuqa ma yai masa kadan wajen sauri, saidai shi fa dole sai yayi amfani dake sannan zakiga aiki da cikawa, dan shine yaimun aiki kan alhajina dadyn zarah wlh ko kara Alhj bai qetarawa saida umarni na, saidai kuma shi aikinsa sa'a ne saudayawa zakije kita samyn biyan buqata, sau dayawa kuma zakije kiji shuru, amman biyan buqatar tafi shirun yawa dan haka ki kwatanta kigani" "yanzun saida kuka watse dashi knn snn buqatarki ta biya? dudda ciwon dake jikin Hjy Hadeeza saida ta kece da wata kafiran dariya tace"yo miza'a fasa? kuma wlh kijima in gaya miki yafimun Alhj dadin harka, sainaga dama ma nike bawa alhj kaina inbangani ba saidai yahaqura da jarabarsa a ranan nai kwanciya ta, dan haka nan siddan fa in naji kwad'an Mlm har zagawa nike kobadan aiki bama musha budirin mu" wata dariya suka saka dukkansu snn Hjy firdauseey tace"wani ma yayi rawa balle dan makadi da abinsu, yanda banda mahaifar nan ma bare naji tsoron ciki ai na amince Qawa indai buqata zata biya qarewar ta gaba yake neman customers dinsa wlh indai zaimyn aiki mai kyau kota baya na yanemi tsab zan basa" Hjy Hadeeza tace"mikikece na baka na zuba? ay Indai Mlm kalla ne babu ta inda bai Neman mata, sake darawa Hjy firdauseey tai tace"babu marsala zaki kaini cikin satin nan yamun aikin nan nasu salis dan bawai haqura zanyi b....shiru tai ganin khaleepa ya shigo falon gidan fuskarsa ad'an sake wanda ga alamu yana cikin farinciki Amman dayake muskilin qin qarawa ne saima fuskar tasa bata bayyana ainahin farincikin nasa ba sosai. gaisheda Hjy Hadeeza yai snn yazauna saman hannun kujerar da Hjy firdauseey take zaune cikin kalar murmushinsa yace "surprise Momy dady yace mun yanzun damukai waya yana nan sauka zuwa Nigeria gobe ko jibi" wani ihun murnar dadi Hjy firdauseey tasaki tareda kama
Chapter 131 · 0% Book details