Sashe 143
Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read
tana kuka wiwi banda radadin zafi babu abinda zuciyarta ke mata. cikin muryan kuka ta tashi zaune a fili tace"wlh narantse da Allah bazan taba zama a cuceni ba tafiyata zanyi sai abasa itan da hujja" da sauri ta miqe tasaka hijab da takalmanta zata fuce daga d'akin knn taji cikinta yayi mata wani mugun juyawa babu shiri tadafe cikin tareda durqushewa qasa tana cije lebe tareda faman sakin nishi kan kukan azaban zafin ciwon murd'awan cikin nata dayake yakece mata...