Sashe 13
Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ya maidosa daga d'an balaguron tafiyar tunanin da yayi, ya sake maimaita masa da cewar " kamance ne q'anena? girgiza kai ismail yayi yace "ban mance burinka ba kaima yaya" mukhtar yace "to danmi zamu zauna babu abinyi alhalin Allah ya bamu wani? kawai kazo ka fara koyon aikin da zaman da zakai tayi in yaso kana aikin kana kai takardunka neman aikin teacing din a haka saikaga Allah yasa an dace wataran kamar yanda nima ban fidda tsammani ba, kaga daga zarar mun samu offer ta samun aikin aikaga sai mi saki wannan mu tafi can koya ka gani q'anena?" miqa masa dunqulallen hannun sa ismail yayi shima mukhtar ya miqa masa nasa sukai 🤜🏻🤛🏻ta'adar su sannan daga bisani suka cafke hannun juna🤝🏻sukai musabaha, cikin dariyar farinciki ismail yake cewa "hmm✔idear yaya na,, dariya mukhtar yayi shima baice komi ba ya cire jibgegiyar rigar sanyin dake jikinsa ya tsaya dagashi sai singlet kawai sai 'yar rigar aikinsu dake saman singlet din kawai. mukhtar yayi hakanne danya kare qanen nasa daga sanyin daya lura yana addabarsa sakamakon qanqame jikinsa dayaga yanata yi tun d'azun, shi ya gwammace sanyin yai masa koma miye ajiki dadai ya ta6a lafiyar qanen nasa dan haka gudun kada ismail ya zargi wani abu ya sashi cewar "q'anena ka tafimin da wannan sweater din tawa gida ka ajuyemun dan banjin dad'in aiki da ita sabida nauyi" cikin tsananin mamaki ismail yace "to yaya yakuma zakayi da sanyi? konaje gida na d'auko maka tawa qaraman wannan ne kasa? " "a'a q'anena hakanma yayi ai, yanzun dai zan yi aiki kaje gida haka, Allah sarki dudda ismail baisan ta kan aikin ba sai yace " to yaya gwadamun yanda kuke aikin nima saina tayaka ko? d'agowa daga kwance qusan da mukhtar ya zuqunna yafarayi na wata taya ya dubesa yace "hmm kabari in lokacin koyon naka yayi zaka koya kaji ko q'anena? yanzun dai katafi gida dan Allah kaga sanyi fa" badon ismail yaso ba yasashi furta kalmar ''to taya" mukhtar yace "yawwa dan qanen" muryan salis sukaji a bayansu yana cewa "ah yau baqon student mukai knn?" murmushi ismail yayi cikin girmamawa ya gaisar da salis din ya amsa,ya dan qara jimawa sannan ya wuce gida sakamakon uzzurawar mukhtar da yai akan ya tafin. bayan tafiyarsa ne mukhtar ya dubi salis dake cin waina da miya wacce yayo musu guzurinta daga gida yace "yau narigaka zuwa abokina" bai samu salis ya amsa masa ba saida yakai komar wainar cikin bakinsa ya hadiye sannan yace "bismillah fa kasan ban jira nidai Indai akan ciki nane shiyasa kan na fara dumamuqan wadannan qarafan saina cika tumbina tsaf tsaf sannan na q'addamar musu a lafiye wallahi " mukhtar yace "to nidai kam yanzun bannajin yunwa ci kawai ka ajiyemun nawa sai anjima naci" salis yace "to lpia lau, nima abinda yasa na taushe hannu bari nai mama ta qarasa ida wainar sannan kuma daga nan na ajiyeta gidanku da mashin dina saida na shiga na gaisar da inno sannan kuma na yo nan". wani d'an siririn murmushi mukhtar yayi yasan maman salis taje gidan nasu ne dan maganar sa da firdausey, hankali kwance yake tafiyar da aikinsa dan yasan baida matsala ga batun inda baffa ya daidaita komi yau. hakan kuwa ya farun bayan maman salis sun gaisa da inno nan sukaita labarinsu har ismail ya dawo gida shima ya gaisheta sannan ya wuce dakin su, jiyake kamar ya jawo gobe tazo ko zai samu hankalin sa ya qara kwanciya daganin masoyiyar tasa da kuma samun amsarsa gareta zuwa garesa. sai gab da maman salis zata tafi har inno ta rakota nan tsakar gida sannan ta dubi inno tace "nace inno daman tambayar ki nike sonyi,,,,,? shin da saninki mukhtar yafara neman auren yarinyar nan kuwah firdausey d'iyar meron tsimbe matar mlm zayyanu mai almajirai ? dudda halin mamanta kuwa marar kyau? bakkwa gudun nan gaba ta haifar muku da tarwatsewar iriyar wannan kyakkyawan ahalin naku mai cike da tsantsan son junanku? to wlh basuda kirki ko kad'an mutanen dan bai dace ace kamar mukhtar mai mutunci da d'a'a yaje neman aure wajen mero ba, ni na d'auki mukhtar kamar salisu ne, dan haka dud wani abu da nasan zai kawo cikas a rayuwar sa gameda danginsa bazan so shiba, shine nace bari nazo naji ta bakinki shin da sanunki koko?" haq'iqa jikin inno ya qara yin sanyi dajin bayanan ta game da mero, tabbas kuma tasan gskia maman salis ke fad'a, dan mero kam abin gudu ce ga al'umma saboda munanan halayen ta maras kyau wanda babu wanda bai sansu ba kaf anguwar. to amman kuma yaya zatayi inda har mlm ya amince wa batun an gama mgn?. tuni zuciyarta ta shiga tunane tunane na anya bazata canza shawara ba kuwa?! daman tunda mukhtar yayi mata maganar auren firdausey tun jiyan nan gaban ta keta faman dukuwa kamar kamarmi, jitake a jikinta kamar wani babban al'amari marar dad'i yakusan kusantowa garesu a rayuwarsu haiq'an,,,,!