← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 178

Sashe 75

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

masu yawa bane dudda qibar tata kuwa, snn dud sunma fara russunawa sakamakon sakarwa kowane saurayinta su da takeyi dud sun fara saccewa. gyara gashin dokin dake kanta tai ta dauresa da wani qaton band ta zura wasu plate shoes ta fito falon nanta iske uwar zaune tana shafe fuskarta da fante fante kamar wata magajiyar karuwai wai nan kuma futa zatayi.. "morning momy" dubanta Hjy Hadeeza tai kokacin da ta tsaida laining dinda takewa labbanta kalar na zarah din. "morning din ubanki shegiya 'yar iska tsinanniya tambad'addiya da bakida burin daya wuce kisa adunga zagina a anguwa? to dadin abunma babu d'anta matar da ya isa ya kafamun na qurya masu datti gahukka dan naci dubu sai ceto wlh, dayake kuma yanzun garin Allah ya waye da zakice min morning alhalin marece na shurin saqqowa". turawa uwar baki tai tace''haba Momy ki gane rayuwa man, yanzun fa iriyar Shaye shayen nan ake yayi dud wacce batayi raina mata class ake, kuma birthday party din abokina mukai jia shiyasa kika ganni hakan, amman bagashi na dawo normal ba yanzun? hararata uwar tai tace"ato kowa dai lpia taiwa dadi babu kamar mai ita sarai kinsan ciwonki qodar nan naki bison wannan shaye shayen Inda hasali ma shine ya jaza miki hakan amman kinqi ki daina kiji in gaya miki babu namijin dazai auri mai shaye shaye indai yasan ciwon kansa to bare ma khaleepa kankatak shida kika nacewa" "Momy aibazan bari yasan ina sha ba har muyi aure ko". maganar take ta na kurban totalin dinta na mayensu gaban uwar kuma. "saikije kici abuncin ki gaya can"cewar hjy hadeezan tana mai tashi tsaye rataye da jikkarta tana qara haska kwalliyan fuskarta da madubi dan taga Inda tai badaidaiba ta gyara. "nizan fita inkin gama shaye shayen naki ki dauki saqo gashi nan a Leda lace ne kikaiwa hjy safiya matar chairman kice injini" "to momu in zaki? "Inda kika Aiken" Hararar uwar tai a kaikaice taci gaba da surbar abinta. bayan fitar Hjy Hadeeza kuwa lokacin biyar saura kota kan abincin zarah bata biba dan daman shaye shaye inya kama maka jiki abincin ma bakkada garanti din cinsa yanda ya dace. danhaka wani dan gyalen rariya ne ta yafa akai ta dauki wayarta da saqon ta fice ta kaiwa matar saqon ta fito Kai tsaye gidan hjy Firdausi ta shige ta sameta nan tana cin abinci a plate dan ba kan daning take ba. nan suka fara fira bada jimawa ba saiga khaleepa ya sauko saman sa da kayan ball a jikinsa dan bai jima ba da dawowa daga aiki. yana shirin fita ne zarah tai Saurin cewa "pleass Yaya khaleepa ka ragemun hanya zanje gidan su mama rayya ne(qanwar mamarta) mama ta aikeni" cikin ko in kula yace"Sry zarah ba hanyar filin ball namu bane" dasauri tace "dan Allah Yaya khaleepa, hanyar ce wlh ba cikin gari suke ba daman ay. zai sake musawa momyn sa tace"mai tsadana ka taimaka ka sauketa man inda ta nemi ragin" hadr zece to Momy Ina motarta ita daba zataje ba? sai kuma yai shuru kawai abinsa yayi gaba ya fice, murmushi Hjy Hadeeza tace "hmm muskilin d'ana knn yama amsa mana dudda yanayinsa ya nuna amincewa ammn abun yaqi fitowa a bakinsa maza jeki zarah kinsan baison jira danna tabbatar zai tafiyar sane" aiko dasauri zarah ta mike ta bisa cikin motar ta iskesa tai saurin bude gidan gaba ta zauna tana sakin murmushi. dubnsa tai cikin wata kwarkwasa da banqaro wasu qirji tace"sannu da office Yaya na" keyy kawai yaiwa motar batareda ya amsa taba suka fita waje ya tsaya saiga yunus shima cikin shirin kwallon harda ball a hannunsa ya iso tareda shiga motar suka wuce ta qofar gidansu heenduh sukabi adaidai lokacin motocin Yan daukar amarya sa'a zuwa garin baucin harsun fara daukar wasu daga cikin iyaye sun tafi kamar yanda aka tsara babu yawan gayya zuwa can. shiyasa iyayen amarya hudu aka dauka sai kuma Yan matan amarya suma saisa saisa. Waii!! kamar ance heenduh takai kallon ta lokacin da take qoqarin shigarda qafarta a motar amarya dansu tafi aiko idonta ya hango mata doctor din shida zarah sun wuce cikin mota dan sune a gaba taga sai wani kallo take jefa masa kuma sam bata kula da yunus dake zaune a baya ba yana dan wasa da ball yayinda suke mgn jefa jefa shida khaleepn. suna wucewa taji wani abu mai ciwo da zafi ya taso mata a wuyanta kamar zata fashe da kuka taji batareda ta Ankara ba. Goggo dahara ta janyo hanunta ta ida zama cikin motar Wanda zaman nata yayi dai dai da saukowar wasu zafafan hawaye saman kumatunta na zafin kishin da taji ya d'arsu a zuciyarta babu shiri kuwa. baba d'ahara ta dubeta tace"au kukan ne yadawo kuma? waiku bazaku haqura ba keda sa'ar ne? dole fa daman aure ya rabaku dun Allah kubar koke koken nan haka. heenduh ko batasan tana cewa "miyasa zata bisa ne baba d'ahara???!! kice ya dawo da ita dan Allah kada zuciyana ya fashe dan zafi takemun" akan khaleepa take sambatun kukan mgnr tata amman kuma baba d'ahara tazata akan mijin sa'a take mgnr dan haka sakin baki baba d'aharar tai tace"haba heenduh ke kuwa? tayaya za'akai yarinya gidan mijinta kice miyasa mijin zai dauki halalin sa? shinwai sabo hauka ne ne?,kifa nutsu heenduh kisan maganar da zakiyi" sake fashewa da kuka sukai a tare wannan lokacin heenduh da sa'a, kowa na kukansa maban banta dan ayanzun kam heenduh ba kukan tafiyar sa'a takeba face na ganin zarah datayi a kurkusa da khaleepa sosai taji maqaqin ciwon abun nasake hautsina mata zuciyarta har kamar zata faso takeji, ita kanta saiyau ta tabbatar da cewan tana matsancin kishin mijin nata Ashe ma???!!!.... tana tsaka da wannan tunanun ne har motarsu ta daga zuwa babban garin bauchi......
Chapter 75 · 0% Book details