Sashe 12
Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
👁🥡👁 🅿9⃣. *S* aida baffa ya d'an yi shirun daq'iqa biyu sannan ya sake duban kowa dake wajen da duba, sannan daga qarshe ya tsaida fuskarsa kan mukhtar yace "mukhtar kana jina kuwa? cikin mummunan fad'uwan da gaban mukhtar d'in keyi yace " eh baffa ina jinka" baffa yace jia da na shigo da dare innonka ta fad'a mun maganar da kukai da ita gameda matar da kake so zaka aura hakane? "eh baffa hakane munyi maganar da inno jian har ranta ya 6aci wanda hakan yasa ban samu barcin kirki ba sabida ban so ace nine sanadin 6acin ran nata akan yarinyar dan haka na yanke hukunci na fad'a muku cewa na haqura na janye daga batun nawa, ya dubi inno yace cikin rawar murya "inno kiyi haquri ki yafemun 6acin ranki dana yayi dan girman Allah, kuma nai miki alqawalin ki za6a mun ko wace mace dake duniyar wacce ranki ya kwanta da ita wlh inno komin tsufanta zan aureta domin farincikin ku shine nawa" yana maganar ne wasu hawaye na zuraro masa ta idanunsa. har cikin ran inno ta qarajin tausayin mukhtar d'in sosai har tayi dana sanin fushin ta data nuna masan ga jiyan dan itama tasan yaranta masu tarbiyya ne koda bata nuna fushinta akan abuba muddin ta nuna qyamarta kan abun tofa sun barsa knn komin sonsu da abun kuwa, muddin ba itace tace si dawo ga abun ba tofa sun basa baya knn badawa ta har abada, jiyayi baffa yace "a'a mukhtar ay bama akaiga hakan ba, tun jia mun gama mgnr da ita kuma Alhamdulilla ta fahimci zancen nawa sosai, na nuna mata shi aure hadin Ubangiji Allah ne tun fil'azal abinda Allah ta qaddaro babu mahani garesa, dan haka inma kace zaka hana yuwuwar abin rabo mai tsanani sai yazo ya kaudaka daga rayuwar ma gaba day'a kuma azo ayi abun bayan ranka, anan ta nuna mun cewar daman ita bawai ta hana bane dan son ranta a'a taguji ne ko ace ita yarinyar ta biyo halin maman tane, to nikuma sai nike nuna mata duda munsan halin ita babar yarinyar batada da kirki kowa ya sani a anguwar nan, to saidai kuma ita yarinyar babu wanda ya ta6a cewa ga wani abun assha datai masa a anguwar nan dan haka wannan nikega ba hujja bane dazata sa ace ba za'a aureta ba, dan muna kyautata zaton cewa bata d'auko halayen maman tata ba, dan haka komi mutane zasu ke fad'a to akan ita maman tane bawai kan yarinyar ba, dan haka itama maman tata muke mata adduar Allah ya shuryeta ya ganar da ita hanya madaidaiciya (niko nace ayya baffa firdausey kam ta rigaya da ta tsotso mugun nono dan haka Allah dai shi kyauta kam, dan abinda Allah yayi kam Annabi kuma sai dai ceto). mlm Abdullah yaci gaba da cewa ''dan haka nike mai shaida maka kaje kaci gaba da neman yarinyar Allah ya sanya albarka a lamarin, kuma insha Allah zanma su yawale magana cikin wannan watan dan muje wajen mariqinta mlm zayyanu din atsaida ranar bikin naku" farinciki kamar kamar me mukhtar yake jinsa a ransa kannewa kawai dai yayi yace "Allah shi qara girma baffa da inno" ismail dayake cikin farinciki shima na ganin komi yayi normal tsakanin iyayen nasu yace "aminnn yaya baffa mun gode inno kema mungode" yayi maganar baki gar kunne. inno tace "ba godiyarka muke so ba amsarka muke sauraro kaima " cikin mamakin rashin fahimta ismail yace "amsa kuma inno tami? duban mukhtar inno tai tace "au mukhtar badai baka fad'a masa maganar da mukai ba jian nan? cikin kama baki mukhtar yace "ya subhanalla,,,! wlh inno na mance ne,, cikin zuciyar ismail ya kalli yayan nasa yace "ba dole ka mance komi ga jiyan nan ba yaya kaji zancen za'a rabaka da masoyiyanka, nima nan da nike farin shiga har mafarkinta tawa na dingiyi kan gari ya waye bare ku da kuke tsofaffun hannu a harkan. maganar da mukhtar keyi masa ne yasashi dawowa tunanunsa, mukhtar yace "inno tace in fad'a maka.... nan ya kwashe komi na maganar da sukai jiya da inno akan shima ya kawo tasa matar ahada ayi bikin tare. Ismail baisan sanda wani Murmushin farinciki ya baibayesa ba, Lallaikm Zainab haske ce a rayuwar sa, daga haduwarsu jia sai batun aure kuma dudda bai ajiye ko sisi ba? lallaikam na maganar mutane da suke cewa hidimar biki temakon Allah ne ga marassa shi zai buda musu ta inda basu tsammani dan albarkacin raya sunnar manzon tsira dan samun zuri'a ta gari wacce zai alfahari dasu ranan gobe. gurgiza kafadansa mukhtar yayi cikin murmushi yace "kaifa muke sauraro mlm" tuni ismail ya fara sosa q'eya yace "na.... nam ya.. yaya ehmm..." sai kuma yayi shiru yakasa mgn kansa na qasa cike da kunya,, zaro idanuwa mukhtar yayi yace "laaaaaa qanena kaddai maganar inno ta zamo gskia kanada budurwa ka boyen"? da sauri ismail ya dubi yayan nasa yace"wayyo yaya mukhtar wlh jia kawai muka fara ganin juna da ita fa ka yarda dani ban boye maka ita ba" dariya mukhtar dasu baffa sukai masa ganin yanda ya duburce lokaci day'a. tsaida murmushin fiskarsa mukhtar ya dan rage ya qara duban ismail din yace "naji to amman ka bawasu inna bayani akai to dan su fahimta a ina ne ita ahalin yarinyar yake ko? cikin kunya gamida saddar da kai qasa ismail yace "eh to ku nimadai ku bani kwana biyun kamar yanda nima tace mun in bata kwana biyu sannan na dawo naji amsar amincewar ta gareni, sannan kuma 'yar nan anguwar ce kuma zainab qanwar firdausey ta gidan mlm zayyanu mai almajirai d'iyarsan" ay yana gama fad'in hakan ya tashi ya gudu d'akinsu cikin kunya shi dariya ma kunyar tasa taci gaba da basu a haka mukhtar ya biyosa dakin ya iskesa zaune sai murmushi yake, bayan mukhtar ya zauna gefensa ne yace "amman dai qanena indai haka ne kaima to kayi dacen tsarkakakkar mata ta q'warai, dan ni ganau ne ba juyau ba akan tarbiyya ta zainab, kuma nasan koda tace makan ka bari nn da kwana biyu ka dawo nasan kunya ce ta hanata baka amsa nan take, amman ai qanena yanda ya had'un nan babu wata yarinya wacce zai nuna yana so taqi amunce masa ko?" murmushi ismail yayi yace "kaima indai batun haduwa ne da gayu ai ban kai yakai ba yayana" Murmushi mukhtar yayi yace ''mu tashi mu tafi dai kada time ya qure mana danni yau inada aiki sosai ma" kwanciya yaga ismail yayi harda jawo malullubi yace "nikam yaya sanyin safiyan nan bada niba yau, dan yau banda exam sai 2:pm." "ayya qanena kace yau sanyin nan zai qara mun yawa inna fita, dan koba komi indai muna tare dakai sai na kanji sanyin nan ya ragemun yanda kasan ana lullu6eni haka nikeji kuma nasan hakan ba komi bane yajazasa face jinina dake gudana tareda matuqar qaunar qanena shiyasa". Zumbur kuwa ismail ya yakice mayafin tareda miqewa tsaye yace "muje na rakaka yaya, bai jira komi ba ya fice mukhtar yabiyo bayansa har suka fito tsakar gida mukhtar ya leqa dakin inno yayi musu sallaman saiya dawo su kuwa suka bisa da adduar Allah temaka adawo lpia. sun fara tafia a hanya mukhtar ya lura da yanda tsigar jikin qanen nasa ke tashi sabida sanyi sakamakon wata riga marar hannu da ya ke a jikinsa, yarasa yanda zai masa yasan koda yace ya koma gida bazai koma ba inda yace har wajen aikin nasu zai kaisa ma, gashi kuma yasan qanen nasa da tsananin jin sanyi dole ya gaqura har saida suka isa wajen aikin nasu suka tarar da oga daniel da wasu sauran ma'aikata rsirarru dan yanzun ake ta zuwa ko salis ma kansa bai iso ba. shima ismail gaisheda ogan yayi cikin ladabi kamar yanda yaga yayan nasa yayi har zasu wuce oga daniel daketa kallon ismail cikin mamaki ganin tsabar kamarsa da mukhtar sun koma masa ma tamka 'yan tagwaye dan bada wani abi sosai mukhtar din ya d'ara ismail ga tsawo ba, oga yace "ahh mukhtaru wannan brother naki ne ko? cikin murmushi mukhtar yace "yes oga" oga daniel yace ''bamta6a gani nasa ba kuma to, mukhtar yace ''hakane oga dayake yana zuwa school ne amman yanzun haka dhis month ne suke yin final year nasu a school din" dubn ismail oga daniel yayi yace "ok no problem amman mi dai hana qane nakan nan shima yajo nan muna aiki tale dashi muna bashi albashi nasa in ya gama jalabawan nasa? cikin tsananin farinciki mukhtar yace "ok thankyu sir thankyu,, shima ismail yai ma oga godia sannan suka jiya suka bar oga din yana cigaba da aikin sa na seta body na wata mota da yake gyara. har inda su mukhtar suke aikinsu sukaje sannan cikin fara'a mukhtar yace "kaga amfanin adduar iyayenmu akan mu ko q'anena? kaga zuwanka alheri ni anan inda kaima gashi ka samu aikin kamawa, cikin murmushi ismail yace "hakane yaya na shiyasa kullum muma muke masu addu'a kamar yanda suke mana, amman yaya burina a rayuwa shine inganni a class ina koyar da students lesson wato teacing to kuma gashi ban samu ba inda na samu wani aikin" yaqarashe maganar fuskarsa tadan canza,, dafasa kad'an mukhtar yayi yace " wannan dinma daka samu ka godewa Allah q'anena, dan wlh wani ma Yana cen bai samu iriyar wannan dinba, batun son aikin teacher naka ni kamanta buri na ne? kallonsa ismail yayi a ransa ya tunano tun suna qananu kowanen su yakan cewa itayensu ga abinda yakeson zama inya girma, iyayen sukan fara da tamvayar yayan nasa mukhtar akan wane buri ne dashi na aiki idan ya girma, saiyace shi burinsa inya girma tasami aikin government yagansa a babban office nasa yana aiki tareda samun albashi maqudai wanda zai dinga kai su baffa da inno mecca cikin jirginsa da ya siya domin su da qanensa. shikuma ismail saiyace " nikuma baffa so nike inna girma burina shine na zama malamin makarantar boko, nima inga ina koyarwa kamar yanda malamin mu ke koya mana yayinda yake mana rubutu da alli ga allo, insun fad'i hakan iyayen kan dinga bunsu da adduar cikan burin nasu na alheri ga rayuwa. ta6asanda mukhtar yayone