← Book details Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 165 OF 178

Sashe 165

Da Sauran Kallo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

👁🥡👁 🅿6⃣9⃣. *J* a khaleepa yayi ya tsaya adai dai bakin qofar shiga falon gidan sakamon tunowa dayai ya manto da gift d'in da yunus ya siyo ya basa yace yabawa madam heenduh kyautar bikinsu, kuma gashi ya barosa a cikin motorsa, jiyai yunus yace ''yadai mlm naga kaja ka tsaya mana a hanya uwa an d'aureka a wajen? in bazaka wuce ba ni kaban hanyar na wuce, dan wannan qamshin girkin yamun kama dana headac...... dafe baki yai ganin khaleepa ya juyo yana watsa masa harara, cikin dariya yunus yace "au sorry na manta ne oga, ina son nace queen heenduh neh fa wai, wannan qamshin girkin nasan kalar nata ne dan kuwa na san qamshin girkinta tun tana gida,,, wlh kuwa friend miyau na harya fara tsinkewa ma in gaya maka mafa, please let's go man" hararsa khaleepa yayi sannan ya d'an saki murmushi tareda fadin "kaidai ka sani da tarin kayan kwad'anka, ni kaida lollipop d'in ma ta fannin kwad'ai da maqulashe bansan gwani ba" yayi mgnr yana mai niyyar komawa da baya. dariya yunus yayi yace "eh munji dai bakomai mlm, bin khaleepa yayi da kallo ganin ya juya yana tafiya hakan yasa shi cewa "a'a yaya zaka fita ne ka barni kuma anan?" cikin nisa daga wajen da khaleepa ya farayi dan kuwa har yayi kusa ma da isa bakin motor, to jin abinda yunus yacen ne yasashi d'an waiwayowa yace "shiga ciki ka jirani a falo, gift d'in nan naka zan dauko danna baiwa maishi abinsa" yunus yace "OK shikenan to" kai tsaye kuwa yunus ya d'aga qafarsa ta dama ya kutsa kansa @ cikin falon gidan tareda sallamarsa da fadin cewa"Assalamu alaikum masu gida gamu mun qara so cikin yardar Allah" yana gama fadan hakan yasa qafarsa ya ida tsallakowa ya shigo falon gidan.........!!!!! (faqat) wanda adaidai wannan lokacin ne hjy hadeeza dake zaune kusada hjy furdauseey anan gidan alhj mukhtar d'in, dan daman tana gidan tunda suka dawo, dan cewa tayi bazata bar gidan ba har sai sunji waya daga zarah in khaleepa ya dawo ya tsallako domin shigowa gidan snn hankalinsu zai kwantan. aiko dai dai sanda yunus ya shigo falon ai anan take daga hjy furdauseey har hjy hadeeza suka kwarwatsa wani uba uban ihun suka mimmiqe tsaye suna billayi tareda qanqame jikunnansu wanda sukeji uwa ana galgala musu zazzafan garwashin wuta a kota 'ina a cikin jikinsu kuwa, gwara kawunansu suka dinga yi a bango suna ihu gamida cizgar gashi kansu suna kuka dan hankalinsu kuwa qoqarin gushewa yakeyi kwata kwata daga cikin jikinsu,,, da gudu dady mukhtar yasauko qasa jin wannan ihun, da yake yana cikin bedroom dinsa gama wankansa knn da shiryawarsa yana qoqarin futowa zuwa gidan qanen nasa cin girkin dare kmr yanda suka saba kuwa dayin hkn tun shiryawarsu,,,yana saukowa qasa kuwa abinda yagani ne na faruwa dasu hjy hadeeza ba qaramin tayar masa da hankali yayiba, musamman dayaga yanda suka cumamiyi junansu suna dukan fusakokinsu jini na futowa ta baki ta hanci gamida turawa junansu mummunan zagi na batsa na wulaqanci gamida aibata juna,,, a rud'e yake cewa "kai subhanillah hjy Mike damunku haka da girmanku kuna abu na qananun yara marassa hankali?? babu wanda ya kulasa a cikin su dan basu sanma yanayi ba, kasa rabasu yayi dan haka jiki na rawa ya fito ya shedawa baba musa mai gadi yaje da marmaza ya kirawo masa baba isma'il da baba yawale gamida dady sales yanzu nan, dasauri kuwa baba musa ya fita shima a rud'e dan halin dayaga dady mukhtar kuwa a ciki yasa babu lpia yau a gidan kam, ai baba musa na barin wajen saiko dady mukhtar yaga da gudu su hjy furdauseey da hjy hadeeza sun sheqo sun fito daga gidan da gudu suna niyyar fucewa,, da gudun gaske kuwa dady mukhtar yaje ya rufe qofar da sarqa, suna isowa kuwa suka yi wani mummunan Karo da qofar, tuni fuskokinsu suka qara fashewa kuwa, amman Sam basu haqura da son fita gidan ba haka suka dinga d'alewa saman jikin gate d'in gidan uwa qadangaru, saidai tsawon gate d'in da sulb'insa ya dinga fyad'eso qasa kuma basu daddara ba nan take zasu koma,, shiko dady mukhtar tagumi yayi daga tsaye yana kallon su, dan zuwa yanzu kam ya shaida dutta qare su hjy hadeeza gamdakar sukai da baqaqen aljannu marassa imani masu kasar juna........ a kuma can dakin zarah itama daidai sanda yunus ya shigo falon gidan ai nan take ta duqe qasa tana kwarara ihun, kankace mi tuni tayo qasan falon da gudu wanda heenduh dake shirin saukowa qasa tajiyo wannan ihun daga dakinta, wanda hakan yasa ta ida fitowa da sauri, hatta yunus ya furgita da ganin zarah yanda ta sauko qasa a guje,, tuni ta nufi kofa tareda bangaje khaleepa daya shigo falon a lokacin har yana watsar da gift d'in dayake riqe a hannunsa kuwa,, a rud'e suka biyota ganin yanda take ihun kankace me harta bud'e qofar gate d'in gidan ta fuce tahau titi tanata falfala gudu, da wani mugun sauri kuwa khaleepa da yunus suka shiga mota sukabita,,,yayinda suka bar heenduh nan tsaye hankalinta a matuqar tashe,,,,. daqyar suka cimmata suka kamota suka sata a motar, ganin yanda take fuzge fuzge abun sai qara tuburewa yake hakan yasa khaleepa yanufi gidansu kai tsaye,, yana shiga anguwar kuwa yaci Karo da alhj Bala, dasauri ya kashe motor daidai gate din gidansu yaje Inda alhj Bala d'in yake tsaye sun gama gaisawa da abokinsa yana qoqarin wucewa gida shima,, khaleepa yayi qarfin halin sheda WA alhj Bala abinda ke faruwa da zarah wacce ke cikin mota tana sakin qara, dud ta fashe masa glass na mota kuwa hannuwanta sai jini sukeyi,, dasauri alhj Bala suka kamota suka fiddota a motor, alhj Bala ganin dayai gidansu khaleepa d'in yafi kurkusa yasa shi umartar khaleepa da su shiga gidan kawai da'ita Inda dud gida ne kuma, ahaka sukai mata talla talla suka shiga ciki da ita, dan sauqinsu ma dare ne babu mutane sosai a wajajen, kwata kwata kasa binsu ciki yunus yayi dan gani yake wannan personal life dunsu ne, kuma komi na buqatar sirri shiyasa kawai ya musu fatan alheri yajuya motor khaleepa d'in ya wuce da'ita gida. wani tashin hankalin khaleepa da alhj Bala suka risqa sadda suka shigo harabar gate d'in gidan suka samu su hjy furdauseey zube a qasa suna billayi uwa macizzai wanda da qarfin gaske zarah ta qwace kanta daga wajen su khaleepa da alhj Bala dasuketa rirriqe da'ita , da gudu tayi sukuwa ta fada jikin iyayen nata, tuni suka kacame da fad'a suna yagin juna uwa mayunwatan zakuna giggan ma juwa, kankace MI tuni sun qara 6ata jikinsu sunyiwa junansu jina jina wanda dasauri khaleepa ya'isa gaban mahaifinsa dake tsaye har lokacin yagaza mgn, nan ya riqesa hankali tashe yace "dady miya faru ne dasu momy suke wann... shugowar baba isma'il ne da baba yawale gamida dady salis harda ma mama zainab, dan da baba musa yaje gidan cewa yai kowa yazo inji alhj sbd gigita dayayi shima, to ganin su yasa khaleepa yin shiru yakasa ci gaba da mgnr, banda ma bugawa babu abinda zuciyarsa ke masa... su kansu su baba isma'il dasukaga halin da su hjy furdauseyy suke ciki saida suka d'umauta,, daqyar dady mukhtar yaja su baba isma'il da nufin kamo hjy furdauseyy datayi nasarar d'alewa takai qarshe gate d'in tana niyyar durewa qasa dudda mummunan tsawon gate d'in kuwa amman bata kula ba, dan ita dai burinta kawai ta haura, banda bugawa fattt!! fattt!! babu abinda zuciyar khaleepa take sakeyi,, dasauri ya matsa ya kama gate din yana hawa ganin dayayi takusan sulalawa gasu dady sun kasa cimmata,, yana gab da'isa Inda take kuwa cikin ikon Allah sukaga kamar anyi sama sama da'ita an fyad'ota qasa jikake timmmmmm nan take qafafunta suka karairaye da hannuwanta sai gulu gulu suke suna yawo gamida zubar jini,, dasauri sukazo kanta dan har ta sume sbd tsananin azaba,, kuka khaleepa yake sanda ya durqushe gaban uwar yakasa furta komi sai faman girgiza uwar yake,,,,, daqyar su ka samu sukai musu talla talla suka shigar dasu cikin gidan anan falo wanda hjy hadiza da 'yarta zarah suketa sakin ihun kuka har lokacin suna fuzgar gashin kansu tareda dukan jikinsu suna yagansa da haqora wanda nan take suka sake yiwa jikinsu kaca kaca da jini,,, yayinda hjy furdauseyy ke a sume har lokacin. dasauri baba yawale ya umarci khaleepa dayaje ya kawo masa ruwa cikin kwano, nan da nan da gudu kuwa khaleepa yaje ya kawo masa ruwan, baba yawale ya kar6a yadunga adduo'e a cikin kwanon ruwan yana tofawa yana gamawa kuwa ya miqe tsaye yawatsa masu hjy haddeza ruwan a jiki su dukknsu harda hjy furdauseyy da ta farfad'o lokacin, jin saukar ruwan adduo'e in nan a jikinsu kamar Ana babbaka su sukaji, nan take suka qara qwalla wani uban ihun suka zube wajen babu wacce ke motsi a cikinsu sama da daqiqa goma sha kuwa, banda sauke numfashin azaba babu abinda sukeyi,, zuwa can suka miqe zaune suka dinga bin jama'ar wajen da kallo (daya daga qa'idar sihirin nan da mlm lamma ya basu shine muddin akayi ba daidai ba tofa bala'oen nau'in azabobi ne gamida tonon asiri zasuyi tasiri ga wanda sukai abin ba daidai ba) mafarin knn hjy haddeza na d'aura idanunta kan alhj Bala mijinta nan take ta fashe da kuka tana fadin "alhj Bala ka yafemun bisa kalar mummunan cutarwar danai maka a rayuwa, ta hanyar bin malamai da na dungayi da 'yan tsubbu dud a kanka, wanda hakan harta kaini ga rabaka da' yan uwanka, kuma nai maka asirin da kaji kaqi jinunsu, snn kuma nice nayi asiri dahar na mallakeka, wanda komi nace kamin baka musu da rawar jiki kake mun shi, wanda ahaka wajen bin malamai na harna samu wani malamin tsubbu waishi mlm lamma yanaciga ba damun aiki a kanka kuma muna harkar alfasha dashi wanda ahaka ne har na samu cikin zarah dashi, sanin danai cewa kana son haihuwa ido rufe a lokacin shiyasa na fad'a maka ina dauke da cikin zarah a lokacin, wanda kai kuma kayi tunanin cikin Kane, shine a lokacin kuma mlm lamma yaqara mun wani aiki wanda saida aka yanka saniya goma, jar akuya goma,
Chapter 165 · 0% Book details